Rufewa
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe Litinin idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 15/12/2024
Abdullahi Bello Diginza da Ahmad Bawage
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe Litinin idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.
Gwamnatin Isra'ila ta amince da shirin faɗaɗa matsugunan da aka mamaye a Tuddan Golan.
Firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya ce matakin ya zama dole ta la'aƙari da samun abin da ya kira ''sabon fagen daga a Syria''.
Mista Nethanyahu ya ce Isra'ila za ta ci gaba da riƙo da yankin da kuma tabbatar da ganin ya bunƙasa.
Tun bayan kawar da gwamnatin Assad, dakarun Isra'ila suka ƙara dannawa cikin Syria, inda suka kai hare-hare da dama a kan cibiyoyin soji.
Ƙungiyar Ecowas ta goyi bayan ƙirƙirar wata kotu ta musamman da za ta saurari ƙara a game da manyan laifukan kama-karya da aka aikata a ƙarƙashin gwamnatin tsohon shugaban Gambia, Yahya Jammeh.
ECOWAS ta ce kotun za ta yi hukunci, a kan laifukan keta ƴancin ɗan Adam da aka aikata a tsakanin shekarar 1994 zuwa 2017.
Ana zargin Jammeh da aikata laifuka da suka haɗa da ɓatar da mutane, da kisan gilla, da kuma tsare mutane babu shari'a, a lokacin mulkinsa.
A shekarar 2017 ya samu mafakar siyasa a Equatorial Guinea, bayan shugaban Gambia na yanzu, Adama Barrow ya kayar da shi a zaɓe.
Manchester City ta yi rashin nasara 2-1 a hannun Manchester United a wasan mako na 16 a Premier League ranar Lahadi a Emirates.
City ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Josko Gvardiol tun kan hutu, kuma haka suka je hutu suka koma zagaye na biyu ƙungiyar Etihad tana cin 1-0.
Sauran minti biyu a tashi daga wasan na hamayya ne, United ta farke ta hannun Bruno Fernandes, sannan Ahmad Diallo ya kara na biyu daf da za a tashi daga karawar.
Kenan City ta yi nasara ɗaya daga karawa 11 a dukkan fafatawa, wadda aka doke karo na takwas da canjaras biyu daga ciki.
Haka kuma ƙungiyar da Pep Guardiola ke jan ragama, an zura mata ƙwallo biyu a raga a karawa ta takwas daga wasa 12 a lik, fiye da yawan da suka shiga ragarta a wasa 62.
Jakadan Majalisar Ɗinkin Duniya a Syria, Geir Pedersen ya ce yana goyon baya janye takunkumin da aka ƙaƙaba wa Syria, yayin da ake neman tallafawa ƙasar domin kafa sabuwar gwamnati bayan hamɓarar da shugaba Assad.
Mayaƙan HTS suna daga cikin ƙungiyoyin da aka ƙaƙaba wa takunkumin, amma Mr Pedersen ya ce akwai buƙatar canza salo.
Ya ce suna fatan ganin an janye takunkumin da aka sanya cikin gaggawa, saboda a samu damar tashi tsaye wajen sake mayar da zaman lafiya a Syria.
A ziyarar da ya kai Damascus mako guda bayan shugaba Assad ya tsere, Mr Pedersen ya yi kiran a warware matsalar ƙasar ba tare da yin ramuwar gayya ba.
Shugaba Bola Tinubu ya buƙaci shugabannin ƙungiyar ƙasashen Afirka ta Yamma Ecowas, da su yi koyi tsarin dimokraɗiyyar Ghana, bayan gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da kuma na ƴan majalisar dokoki a ƙasar cikin lafiya da kwanciyar hankali.
An sake zaɓar John Mahama, tsohon shugaban ƙasar a zaɓen ranar 7 ga watan Disamba, inda ya kayar da mataimakin shugaban ƙasar Mahamudu Bawumia. Bawumia ya kira shi tare da yi masa murna tun kafin a sanar da sakamakon zaɓen a hukumance.
Da yake jawabi a wajen taron shugabannin ƙungiyar Ecowas karo na 66 da aka yi a Abuja yau Lahadi, Tinubu ya ce abin da ya faru a Ghana abin koyi ne ga wasu ƙasashe da ke yankin.
Shugaban ƙungiyar ta Ecowas ya kuma yaba wa shugaban ƙasar Ghana mai ci, Nana Akufo-Addo, wanda ya halarci taron a karo na karshe a matsayinsa na shugaba, da irin namijin ƙoƙari wajen shirya sahihin zaɓe.
Tinubu ya kuma yaba wa Senegal ka gudanar da zaɓen ƴan majalisa cikin gaskiya da lumana.
Ya yi kiran haɗin kai tsakanin ƙasashe mambobin Ecowas, musamman wajen kare hakkin ƴan ƙasashensu da kuma samar musu da ababen more rayuwa.
An sallami shugaban Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva, daga asibiti bayan aikin da aka yi masa a ƙwaƙwalwa.
Zai fara zuwa mahaifarsa, Sao Paulo inda ake sa ran ƙara yi masa gwaji kafin ya koma Brasilia.
Jami'an gwamnati sun ce shugaba Lula mai shekara 79 yana ƙara murmurewa, anna akwai buƙatar ya guji yin tafiya mai nisa a jirgin sama.
Ana kyautata zaton mutum 20 sun rasa ransu bayan kifewar kwale-kwalensu a karamar hukumar Agatu na jihar Benue ranar Asabar.
An ruwaito cewa waɗanda lamarin ya rutsa da su na komawa Doma ne a jihar Nasarawa bayan cin kasuwar kauyen Ocholonya, lokacin da kwale-kwalen ya kife.
"Kwale-kwalen na ɗauke da mata da yara waɗanda suka je cin kasuwar Ocholonya saboda ranar Asabar take ci. Kan hanyar su ta komawa Doma ne jirgin ya kife da dukansu," a cewar wani jagora a yankin Adanyi Adanu.
Shugaban karamar hukumar ta Agatu Melvin James, ya tabbatar da faruwra lamarin a yau Lahadi, kamar yadda gidan talbijin na Channels ya ruwaito.
Ya ce yawancin mutanen sun kasance ƴan kasuwa daga Doma na jihar Nasarawa.
"Na samu labarin afkuwar lamarin, kuma rahotanni sun bayyana cewa kusan mutum 20 ake kyautata zaton sun mutu. Masu aikin ceto sun ce sun gano gawawwaki amma babu alkaluma kawo yanzu," in ji James.
Shugaban karamar hukumar ya ƙara da cewa ana ci gaba da aikin ceto, kuma rundunar sojin ruwa ta Najeriya na taimakawa a aikin ceton.
Dakarun bataliya ta shida na sojojin Najeriya, sun ce sun kuɓutar da wasu mutum uku da aka yi garkuwa da su a kauyen Manzala da ke karamar hukumar Yorro na jihar Taraba.
Wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na bataliyar, Olubodunde Oni, ya fitar, ya ce sun samu nasarar ceto mutanen ne bayan samun bayanan sirri kan wajen da masu garkuwa da mutanen suke, inda daga nan suka afka musu.
Ya ce tuni aka miƙa mutanen hannun ƴan uwansu.
"Bayan nan kuma, mun kai samame kan tsaunuka da kuma wurare masu haɗari a ƙananan hukumomin Ardo-Kola da Yorro, inda muka daƙile barazanar masu garkuwa da mutane da mayar da doka da oda," in ji sanarwar.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya naɗa fitaccen tauraron fina-finan Hausa na Kannywood, Sani Musa Danja a matsayin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin matasa da wasanni.
Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwaman jihar Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ranar Lahadi, ya ce gwamnan ya amince da naɗin Sani Danja tare da wasu mutane da shugabannin hukumomin da aka sauya wa ma'aikatu da masu bai wa gwamna shawara.
A mako mai ƙarewa ne dai gwamnan na jihar Kanon ya yi wa majalisar zartarwarsa garambawul, inda ya sauke wasu ƙusoshin gwamnatinsa, cik har da sauke sakataren gwamnatin jihar da shugaban ma'aikatar fadar gwamnatinsa.
A wannan makon mun kawo muku labarain Tsalle Daya na, Zainab Mohammed Chubaɗo, wanda ya zo na uku a gasar Hikiyata ta 2024 da BBc ta shirya.
Zainab Mohammed Chubaɗo ƴar asalin jihar Kaduna da ke zaune a unguwar Rijiyar Zaki a birnin Kano ta, ta gina jigon labarinta ''Labarin Tsalle Ɗaya'' kan wata mai juna biyu da ta tsinci kanta a hannun masu garkuwa da mutane.
Kwanaki kaɗan bayan hamɓarar da gwamnatin shugaban Syria Bashar al-Assad, ƙasar Rasha ta ce ya tsallaka zuwa Moscow.
Hakan na zuwa ne bayarn da 'yantawaye suka kifar da gwamnatin shugaban.
Sai dai ba shugaba Assad ba ne kawai wani babban mutum da ya taɓa guduwa zuwa Rasha ba.
Akwai wasu fitattun mutum huɗu da suka taɓa guduwa zuwa ƙasar a baya.
Babban kamfanin man fetur na ƙasar Libya ya dakatar da ayyukansa a matatar man fetur ta ƙasar, bayan da aka samu arangamar masu dauke da makamai, lamarin da ya tayar da gobara da ta lalata wasu ɓangarorin matatar.
Hotunan da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna wasu tankunan mai na ƙonewa a matatar ta Zawiya, da ke yammacin birnin Tripoli.
Rahotonni daga wurin sun ce an samu nasarar kashe gobarar tare da dakatar da gas ɗin da ke zuba.
Zawiya ce matatar man fetur ta biyu mafi girma a Libya, kuma ita ce kaɗai ke samar da man fetur ga kasuwannin ƙasar.
Ƙasar Libya na daga cikin manyan ƙasashe masu arzikin man fetur, to sai dai rikicin masu ɗauke da makamai na ci gaba da kawo wa fannin tarnaƙi, tun bayan hamɓarar da gwamnatin Muammer Gaddafi a 2011.
Shugabannin ƙungiyar ƙasashen Afirka ta Yamma Ecowas za su gana yau Lahadi a Abuja, domin tattauna batutuwan da suka shafi haɗin kai da tsaro da kuma tattalin arzikin yankin.
Ana sa ran batun ficewar ƙasashen yankin Sahel daga ƙungiyar ne zai zama babban ajandar taron na yau.
Ƙa'idar da Ecowas ta gindaya ta sanarwar shekara guda kafin ficewar ƙasa daga ƙungiyar - wanda ƙasashen Mali da Burkina Faso da Nijar suka yi - zai cika a watan Janairu mai zuwa.
A makon da ya gabata ne, shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya shaida wa shugaban Jamus da ya ziyarci ƙasar, Frank-Walter Steinmeier, cewa muradun walwalar 'yan ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar ne babban abin da ke ran shugabannin Ecowas.
Inda ya alƙawarta yi amfani da diplomasiyya da hikima wajen maido da ƙasashen cikin ƙungiyar.
Shugaba Tinubu - wanda shi ne shugaban Ecowas - ya sha amfani da hanyoyin diflomasiyya don ganin ya janyo hankalin ƙasashen na yankin Sahel domin su koma cikin ƙungiyar.
Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo a birnin Abeokuta na jihar Ogun.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar na jam'iyyar NNPP tare da tsohon gwamnan jihar Cross River, Donald Duke, sun gana da Obasanjo a gidansa da ke birnin Abeokuta.
Cikin wani saƙo da tsohon gwamnan na jihar Kano, ya wallafa a shafinsa na X, ya ce a lokacin ganawar sun tattauna abubuwan da suka shafi ƙasa, ciki har da makomar siyasar ƙasar.
“Mun yaba da yadda Baba ya nuna mana karimci da cikakken goyon baya,” kamar yadda ya wallafa.
Masu shigar da ƙara a Koriya ta Kudu sun ce shugaban ƙasar da aka tsige, Yoon Suk Yeol, bai amsa gayyatar da aka yi masa ba domin masa tambayoyi.
An dai tsige Mista Yoon daga shugabancin ƙasar a ranar Asabar, bayan kalaman da na ya furta a farkon watan da muke ciki na cewa zai ayyana dokar soji a ƙasar.
Yanzu dai masu shigar da karar sun ce za su sake aike masa da wata gayyatar.
Mista Yoon ka iya fuskantar tuhume-tuhume da suka shafi tozarta muƙami da sauran manyan laifuka.
Shugaban ƙasar na riƙo, Han Duck-soo, ya tabbatar wa shugaba Biden na Amurka ta waya cewa Seoul za ta ci gaba da aiki da manufofinta na ƙasasashen waje da tsaro ba tare da wata tangarɗa ba.
Shugabannin mulkin soji na ƙasashen yankin Sashel sun sanar da ɓuɗe ƙofofin ƙasashensu ga mambobin ƙasashen ƙungiyar Ecowas a wani mataki na ƙara dankon alaƙa tsakanin ƙasashen da ƙungiyar Ecowas.
A yanzu mutanen ƙasashen Ecowas za su iya shiga ƙasashen Mali da Burkina Faso ta Nijar su yi yawo ko su zauna a ciki ba tare da biza ba.
Cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da ƙasashen suka fitar, kuma shugaban mulkin sojin Mali, Kanal Asimi Goita - wanda shi ne shugaban ƙungiyar ƙasashen yankin Sahel - ya sanya wa hannu, ya ce a yanzu mutanen ƙasashen Ecowas na da damar shiga ƙasashen uku ba tare da wata tangarɗa ba.
“A yanzu mutanen ƙasashen Ecowas na da damar shiga da fita, ko zama da yawo da gudanar da harkokinsu a cikin ƙasashen ƙungiyar yankin Sahel kamar yadda dokokin ƙungiyar suka tanadar,'' in ji sanarwar.
Shugabannin mulin sojin sun ce sun ɗauki matakin ne domin inganta zamantakewa da 'yan'uwantaka da abota da kuma muradin haɗin kan al'ummar Afirka.
Shugaban 'yantawayen Syria, Ahmed al-Sharaa - da aka fi sani da Abu Muhammed al-Jolani - ya yi alla-wadai da hare-haren da Isra'ila ke cigaba da kai wa Syria.
Al-Jolani ya ce hakan barazana ce da ka iya sake haddasa rikici a ƙasar.
A nata ɓangare Isra'ila na cewa tana ƙoƙarin daƙile faɗawar makamai a hannun maƙiyanta a Syria.
Amma Jolani ya faɗa wa kofofin yaɗa labarai cewa wannan ba gaskiya ba ne, tare da jadadda cewa a yanzu ba yaƙi ba ne a gabansu ba.
Kungiyoyin da ke sa ido a Syria sun ce Isra'ila ta kai hare-hare ta sama, fiye da 60 a ranar Asabar a ƙasar.
Amurka ta ce ana tuntuɓar juna tsakaninta da ƙungiyar al-Sharaa da ta kifar da gwanatin Assad
Kafar yaɗa labarai ta ABC News da ke Amurka ta amince ta biya dala miliyan 15 ga sabon shugaban Amurka mai jiran-gado, Donald Trump bayan da ya kai kafar ƙara a kan zargin ɓata masa suna.
Ya kai ƙarar ne saboda wata hira da mai gabatar da shiri a tashar, George Stephanopoulos, yake cewa an samu shugaban mai jiran-gado da laifin fyade a wata shari'a.
A lokacin wata hira a shirin na talabijin, a watan Maris, hirar da ta yi zafi, inda, George Stephanopoulos da ke tattaunawa da ‘yar majalisar wakilai ta jamiyyar Republican, mai gabatarwar ya rika cewa kotu ta samu Mista Trump da laifin fyaɗe.
Mista Trump ya kai karar tashar talabijin ɗin ta ABC da kuma Mista Stephanopoulos.
Yanzu dai bayanai na nuna cewa ɓangarorin biyu sun sasanta, kuma a ƙarƙashin yarjejeniyar da suka cimma, ABC za ta biya dala miliyan 15, ga wata gidauniyar Trump da kuma wani gidan adana kayan tarihi.
Haka kuma kafar yaɗa labaran za ta biya dala miliyan ɗaya da Mista Trump ɗin ya kashe a sharia’r.
Bugu da ƙari a ƙarƙashin yarjejeniyar sasanton za a sanya wata sanarwa a jikin wata Maƙala da ake rubutawa a shafin intanet na ABC News da ke nuna kafar da George Stephanopoulos na nadamar kalaman da ya yi.
Wata mahaukaciyar guguwa da ke tafiya da ruwan sama mai ƙarfi da ba a taɓa ganin mai muninta ba a kusan tsawon ƙarni ɗaya, ta afka wa tsibiran Mayotte, wanda yanki ne a tekun Indiya da ke ƙarƙashin Faransa.
Guguwar mai laƙabin Chido, wadda ta yi wa yankin kaca-kaca ta hallaka aƙalla mutum biyu, kuma ana ganin yawan zai iya haura hakan.
Shugaban Faransa Eammanuel Macron ya ce al'ummar Faransa na tare da wannan yanki domin taya su alhinin, yayin da jami’an Faransar suka ce tuni aka tura 'yan kwana-kwana 250 sannan kuma za a tura jami’an tsaro zuwa tsiburan, inda tuni ma wasu sun rigaya sun hallara a can.
Bayan wani taron gaggawa da sabon firaministan Faransa ya yi da ministoci a kan lamarin.
Ministan cikin gida Bruno Retailleau, ya yi wani taron manema labarai inda ya ce guguwar ta yi wa yankin kaca-kaca.
Ya kara da cewa yanayi ne na daban da ba a taɓa ganin irinsa ba a Mayotte tun 1934.
Ministan sufuri na Faransa ya bayyana lamarin a matsayin babban, abin damuwa. Ya ce filin jirgin sama na Mayotte ya lalace sosai, kuma ana tura jiragen ruwa domin su kai kayayyaki.