Iran na neman tattaunawa da mu bayan barazanar kai mata hari - Trump
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce hukumomin Iran sun tuntubi Amurka domin neman tattaunawa, bayan barazanar da ya yi na ɗaukar matakin soji kan yadda ake kashe masu zanga-zanga a kasar.
Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da manema labarai, inda ya ce an riga an shirya wata ganawa tsakanin ɓangarorin biyu, amma kuma ƙila Amurka ta ɗauki wani mataki kafin a kai ga ganawar.
A halin da ake ciki, wata kungiyar kare hakkin dan Adam a Iran ta ce ta tabbatar da mutuwar kusan mutum 500 tun bayan ɓarkewar zanga-zangar.
Hakazalika, wasu faifan bidiyo da ke yawo sun nuna wani fili da ake ajiye gawawwaki a wajen Iran, inda jama’a ke zuwa domin neman gawarwakin ‘yan uwansu da suka ɓace.