Hamas na ganawa da Qatar da Turkiyya kan yarjejeniyar Trump
PENGASSAN ta janye yajin aikinta
An samu jagoran adawar Afirka da Kudu da laifin harba bindiga a bainar jama'a
Rahoto kai-tsaye
Abdullahi Bello Diginza
Dakarun Faransa sun kama jirgin ruwan Rasha bisa zargin safarar mai
Dakarun ƙasar Faransa sun shiga wani jirgin ruwan dakon mai a yammacin gaɓar tekun Faransa da ake zargin na cikin jiragen ruwan da Rasha ke amfani da su ta bayan fage wajen fitar da man fetur domin bijirewar takunkuman da ƙasashen yamma suka sanya. An kama ma'aikatan jirgin ruwa biyu.
Wakilin BBC ya ce Ofishin Mai gabatar da ƙara a garin Brez ya ce sun fara gudanar da bincike kuma shugaba Macron ya ce ma'aikatan jirgin sun aikata laifi.
Jami'an hukumar kula da jiragen ruwa sun ce jirgin ya bar Rasha kwanaki goma da suka gabata kuma ya kasance a gaɓar tekun Denmark a lokacin da jirage marasa matuƙa suka keta sararin samaniyar ƙasar
Mun ba wa Falasɗinawa damar ƙarshe na su koma kudancin Gaza - Kartz
Asalin hoton, EPA
Sojojin Israila sun sake kai hare hare ta sama a birnin Gaza inda rundunar sojin kasar ta ce sun kusa yi masa kawanya.
Rahotanni sun ce an kashe Falasdinawa fiye da arabain kuma kungiyar agaji ta Redcross ta ce ta dakatar da ayyuikanta saboda hare haren da sojojin Israila ke kaiwa yankin sun tsanananta.
Ministan tsaron Israila, Isreal Katz ya ce mazauna yankin nada da dama ta karshe na tserewa zuwa kudancin zirin Gaza.
Kawo yanzu Hamas ba ta ce komai ba kan shirin zaman lafiya na baya-baya nan da Amurka ta fito da shi.
Ma'aikatan gwamnati sun soma zaman kashe wando a Amurka bayan dakatar da ayyuka
Asalin hoton, Getty Images
An tilastawa dubban ma'aikatan gwamnatin Amurka zaman kashe wando sakamakon takadamar siyasa da ta sa aka rufe cibiyoyin gwamnati.
An rufe dukannin ma'aikatun gwamnati tare da dakatar da akasarin ma'aikatan gandun daji daga aiki inda ƴan jamiyyar Republicans da Democrateke ci gaba da ɗora wa juna alhakin gazawa wajan amincewa da sabon tsari kashe kudi na gwamnati.
Kawo yanzu akwai rashin daidaito tsakanin yan Republicans da Democarts kuma bambance-bambancen da ke tsakaninsu na ci gaba da ƙaruwa.
Ma'aikata masu muhimman ayyuka kamar masu kula da zirga -zirgar jiragen sama na ci gaba da aiki ba tare da an biyasu albashi ba
Majalisar Dattawan Amurka sun yi watsi da shawarar sake buɗe cibiyoyin gwamnati
Majalisar dattawan Amurka ta sake yin watsi da shawarar da yan jamiyyar Republicans suka bayar na bada tallafin wucin gadi domin a sake bude cibiyoyin gwamnati.
Mataimakin shugaban ƙasa JD Vance ya ɗora alhaki kan yan jam'iyyar Democrats kan abin da ya kira rufe cibiyoyin gwamnati na babu gaira babu dalili wanda ya sa dubban ma'aikata tsayawa gida ba tare da an biya su albashi ba.
Ya ce ɓangaren senata Chuck Schummer na jam'iyyar Democrats sun sa a rufe cibiyoyin gwamnati saboda sun faɗa mana cewa za su bude cibiyoyin gwamnati kawai ne idan muka tallafi biliyoyin dala ga tsarin kiwon lafiya domin kula da bakin haure
Shugaban marasa rinjaye a Majasalisar wakilan Amurka wanda dan jamiyyar Democarsta ne Hakeem Jeffries ya ce yana bada tabbacin saka Amurkawa masu ƙaramin karfi cikin tsarin kiwon lafiya na ƙasar.
Majalisar Shura za ta watsa zama da Sheikh Lawal Triumph kai tsaye
Asalin hoton, Lawal Triumph/Facebook
Sakataren Majalisar Shura ta Kano, Shehu Wada Sagagi ya ce da farko za a fara da aike masa takardar gayyata tukunna wadda kuma za ta ƙunshi rana da lokacin da zai bayyana a gaban kwamitin.
Ya kuma ƙara da cewa domin cire shakku daga zukatan al'umma an shirya yin zaman kai tsaye.
"Wannan zama an shirya yin sa ne "Live" wato kai tsaye domin kowa ya ga irin tambayoyin da za a yi masa da kuma irin amsoshin da zai bayar," in ji Shehu Sagagi.
Dangane kuma da labaran da ke yawo a kafafen watsa labarai kan cewa Majalisar ta dakatar da Malam Lawal Triumph daga yin wa'azi, sai Shehu Sagagi ya ce a'a ba wai an hana shi yin wa'azi ba ne kwata-kwata.
"E an kawo shawara ne cewa wasu mutane suna ta fitintunu ana ta maganganu marasa daɗi har daga wajen jihar da ake ganin wannan abun zai iya hargitsa gari saboda haka aka kawo shawarar cewa a dakatar da shi daga dukkan waɗannan maganganu da suka shafi wannan mas'ala." In ji Sagagi.
Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta ce ta dakatar da ayyukanta a Zirin Gaza saboda ƙaruwar hare-haren sojojin Isra'ila a ƙwayar birnin.
Ta ce dubban Falasɗinawa na cikin wani mawuyacin hali, yayin ake ci gaba da yi musu ruwan bama-bamai.
Rahotonni daga birnin sun ce a aƙalla Falasɗinawa 41 aka kashe a yau Laraba a yankin, mafi yawansu a birnin Gaza.
Rundunar sojin Isra'ila ta fitar da sabon umurnin da ya buƙaci mazauna birnin su fice zuwa kudancin Gaza.
Ministan tsaron Isra'ila, Isrea Katz ya ce manufar farmakin ita ce ƙarfafa ƙawanyar da suka yi wa mayaƙan Hamas a Gaza.
Kawo yanzu shugabanin Hamas ba su mayar da martani ga shirin shugaba Trump na kawo ƙarshen yaƙin ba.
Majalisar Shura ya gayyaci Sheikh Lawal Triumph ya kare kansa
Asalin hoton, Lawal Triumph/Facebook
Majalisar Shura ta Kano ta gayyaci malamin nan da ake zargi da furta kalaman "ɓatanci" ga janibin annabi Muhammad SAW a birnin Kano, Sheikh Lawal Triumph da ya je gabanta domin kare kansa.
Sakataren Majalisar Shehu Wada Sagagi ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya yi da yamamcin ranar Larabar nan a birnin na Kano.
Shehu Wada Sagagi ya kuma ƙara da cewa Majalisar ta dakatar da malamin daga tattauna batun da ake zarginsa da shi wanda ya janyo cece-kuce har zuwa lokacin kammala bincike bayan karɓar bahasinsa.
"Ba wai shi kaɗai Majalisar ta dakatar daga tattauna batun da ya janyo ruɗani har ma da dukkannin sauran malamai da al'ummar gari. Muna kira da a kame daga tattauna batun a jira har sai sakamakon binciken ya fito." In ji Sagagi.
Sojojin Sudan sun ce sun yi wa RSF lahani a El-Fasher
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar Sojin Sudan ta ce ta haifar da babbar illa da mayaƙan RSF suka yi wa birnin El-Fasher a Arewacin Darfur ƙawanya, inda aka kashe da yawansu, ciki har da sojojin hayar Ukraine da na Colombia.
To sai dai mayaƙan RSF sun ci gaba da iko da birnin mai muhimmanci, inda kusan fararen hula kusan 300,000 suke maƙale.
BBC ta zanta wasu daga cikin mazauna birnin da suka bayayna mummunan halin da birnin ke ciki na mace-mace da ɓarna da yunwa da kuma rashin lalacewar asibitoci.
An fara maido da sabis ɗin intanet a Afghanistan
An maido da sabis din intanet a wasu wayoyin hannu a Afghanistan, kwana uku bayan da ƙungiyar Taliban mai mulkin ƙasar ta katse sabis ɗin.
Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce an fara ganin sabindin intanet a wayoyi a biranen Kandahar da Herat.
Ƙungiyar Taliban ba ta bayar da dalilinsu na ɗaukar matakin katse sabis ɗin ba.
Katse sabis ɗin ya janyo cikas a bankuna da filayen jiragen sama a ƙasar.
Mutum 25 sun mutu bayan ruftawar coci a Ethiopia
Hukumomin Ethiopia sun ce aƙalla mutum 25 ne suka mutu, yayin da fiye da 50 suka jikkata a lokacin da wata coci da ake kan ginawa ta rufta a ƙasar.
Lamarin ya faru ne yau Laraba a garin Arerti mai nisan kilomita 70 arewa da Addis Ababa, babban birnin ƙasar.
Mutanen sun taru a cocin ne domin wani bikin ibada na shekara-shekara.
Ana tunanin cewa akwai wasu da suka maƙale a cikin ɓaraguzan ginin, yayin da hukumomin ke fargabar adadin waɗanda suka mutu zai iya ƙaruwa.
Wani ma'aikacin asibitin da aka kai waɗanda suka jikkata, ya ce lamarin ya rutsa da ƙananan yara da tsofaffi.
Asibitin ya buƙaci tallafin ƙungiyar agaji ta Red Cross domin kula da waɗanda suka jikkatan.
Gwamnan Kano ya buƙaci Tinubu ya cire kwamishinan ƴansandan jihar
Asalin hoton, Abba Kabir Yusuf
Gwamnan jihar Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya cire kwamishinan ƴansandan jihar CP Adamu Bakori daga mukaminsa.
Yayin da yake jawabi a bikin ranar cikar Najeriya shekara 65 da samun ƴancin, da aka gudanar a filin wasa na Kofar Mata, gwamnan ya nuna ɓacin ransa kan abin da ya kira ''halin rashin kishin ƙasa da kwamishinan ke nunawa a jihar''.
Gwamnan ya zargi kwamishinan da janye jami'an ƴansanda daga filin taron a daidai lokacin da ake dab da fara taron.
''A yau kowane ɗan Najeriya na murna da zagayowar ranar samun ƴancin kan ƙasarmu,... amma a matsayinsa na kwamishinan ƴansanda ya yi abin da ya kunyata mutanen Kano'', in ji Gwamnan.
''Sai da aka kusa fara wannan biki, kawai ya janye duka jami'an ƴansandan da ke wannan wuri, inda ba don sauran jami'an tsaro da muke da su ba da wannan taron ba zai samu armashi ba'', in ji shi.
"A matsayina na jagoran gwamnatin Kano da mutanen Kano suka zaɓa, mun yi Allah wadai da wannan hali na rashin nuna kishin ƙasa da wannan kwamishinan ke nuna mana, wannan ya saɓa ƙa'idar aiki, sannan cin aiki ne''.
''Don haka ina kira da babbar murya ga shugaban ƙasa Bola Tinubu tare da girmamawa ya cire mana wannan kwamishinan daga jiharmu'', in ji gwamnan na jihar Kano.
Haka kuma gwamnan ya ƙara da cewa zai rubuta ƙorafi a madadin gwamnati da al'ummar Kano zuwa ga shugaban ƙasa ta hanyar ofishin bai ba shi shawara kan harkokin tsaro.
Kawo yanzu dai rundunar ƴansandan jihar ba ta ce komai ba game da zargin gwamnan jihar.
Girgizar ƙasa ta halaka kusan mutum 70 a Philippines
Asalin hoton, Anadolu via Getty Images
Aƙalla mutum 69 ne suka mutu, gommai suka jikkata bayan wata girgizar ƙasa mai ƙarfi ta auka wa ƙasar Philippines.
Girgizar ƙasar mai ƙarfin maki 6.9 ta auka tsakiyar ƙasar a ranar Talata da daddare.
A ranar Laraba hukumomin lardin Cebu - inda lamarin ya fi ƙamari - suka ayyana iftila'in a matsayin mummunan bala'i, bayan da dubban mutane suka kwana a kan tituna saboda fargaba.
Ɗaya daga ciin mazauna lardin na Cebu ya shaida wa BBC cewa babu abin da ake ji a yankin sai kukan ƙananan yara da suka ''ɗimauce'' sakamakon iftila'in..
Ya ci gaba da cewa yanyoyin samar da ruwa da na wuta duka sun katse a yankin.
Girgizar ƙasar na zuwa ne kusan mako ɗaya bayan da ƙasar ta fuskanci mummunar guguwar da ta kashe fiye da mutum 10.
An samu ƙari a yawan ɗanyen mai da Najeriya ke haƙowa - Tinubu
Asalin hoton, FADAR SHUGABAN NAJERIYA
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ce ƙasar ta samun gagarumin ƙari a yawan ɗanyen man da take haƙowa daga ganga miliyan ɗaya a shekarar 2023 zuwa miliyan 1.68 a kowace rana a yanzu.
Yayin jawabin da ya gabatar wa yanƙasar, kan bikin cikar Najeriya shekara 65 da samun yancin kai, shugaba Tinubu ya ce an samu ƙarin ne sakamakon inganta tsaro da samun sabbin masu zuba jari.
Haka kuma ya alaƙanta ci gaban da kyakkyawan shugabancin masu ruwa da tsaki a harkar mai a yankin Neja Delta.
Shugaba Tinubu ya ƙara da cewa Najeriya ta samu gagarumin cigaba wajen tace mai a cikin gida karon farko a cikin shekara 40.
''Kuma yanzu haka ƙasarmu ce kan gaba wajen fitar da man jirgin sama a nahiyar Afirka'', in ji shi.
Shugaban Najeriya ya ce darajar kuɗin ƙasar ta farfaɗo sakamakon sauye-sauyen da gwamnatinsa ta ɓullo da su a fannin tattalin arziki.
An samu jagoran adawar Afirka da Kudu da laifin harba bindiga a bainar jama'a
Asalin hoton, Getty Images/ Per-Anders-Petterson
An samu madugun hamayyar Afirka ta Kudu, Julius Malema da laifin harba bindiga a wurin da jama'a ke taruwa da kuma gangancin jefa jama'a cikin haɗari.
Jagoran masu tattsauran ra'ayin mai janyo ce-ce-ku-ce ya ce bindigar da ake zarginsa da ita ta wasan yara ce.
Ya yi harbin ne a wani gangami a 2018.
Mista Malema zai iya fuuskantar ɗaurin shekara 15 a gidan yari, idan aka yanke masa hukunci a watan Janairun shekara mai zuwa.
PENGASSAN ta janye yajin aikinta
Asalin hoton, Dangote Refinary
Ƙungiyar manyan ma'aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya, PENGASSAN ta amince da jingine yajin aikin da shiga bayan samun saɓani da matatar mai ta Dangote
Yajin aikin ne zuwa ne bayan PENGASSAN ta zargi mattaar da korar fiye da ma'aikata 800 saboda sun nuna sha'awar shiga ƙungiyar.
Gwamnatin Najeriya ce ta shiga tsakani a sasancin ɓangarorin biyu da ake yi tun ranar Litinin, to amma sai a yau Laraba ne aka cimma matsaya.
Cikin wata sanarwa da ma'aikatar kwadagon ƙasar ta fitar ta ce matatar ta amince da mayar da ma'aikatan da ta kora domin su ci gaba da aiki da ita.
"Babu ma'aikacin da zai cutu sakamakon saɓanin matatar Dangote da PENGASSAN," a cewar sanarwar.
A nata ɓangare, ƙungiyar ta PENGASSAN ta ''amince ta fara shirye-shiryen janye yajin aikin''.
Tun bayan fara aikin matatar Dangote a 2024 ta riƙa cin karo da rassan ƙungiyoyin ƙwadago a fannin man fetur na ƙasar, wadanda ke zarginta da ƙoƙarin mamaye harkokin kasuwancin man fetur a ƙasar.
To sai dai matatar ta zargi wasu kamfanonin mai na duniya ne da ke aiki a Najeriya, da ingiza ƙungiyoyin ƙwadagon domin cimma muradunsu.
Tattalin arzikin Najeriya ya fara bunƙasa bayan sauye-sauyenmu - Tinubu
Asalin hoton, Fadar shugaban Najeriya
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce a lokacin da ya hau karagar mulkin ƙasar, tattalin arzikinta na dab ta durƙushewa saboda abin da ya kira tsare-tsare tattalin arziki marasa ɗorewa.
Cikin jawabin da ya yi wa ƙasar albaracin cikarta shekara 65 da smaun ƴancin kai, Shugaba Tinubu ya ce matakan da gwamnatinsa ta ɗauka ne suka taimaka wajen ceto ƙasar daga durƙushewar;
''A ƙarƙashin gwamnatinmu tattalin arzikin ya fara farfaɗowa sakamakon sauye-sauyen da muka ɓullo da su shekaru biyu da suka gabata'', in ji shi.
Shugaban na Najeriya ya ce a rubu'i na biyu na shekarar 2025 arzikin da ƙasar ke samu a cikin gida ya haɓaka da kashi 4.23, mafi yawa cikin shekara huɗu, inda ma ya zarta hasashen da IMF ta yi.
''Hauhawar farashin kayayyaki ta ragu zuwa kashi 20.12 cikin 100 a watan Agustan da ya gabata, raguwa mafi yawa cikin shekara uku'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Ya ci gaba da cewa gwamnatinsa na aiki tuƙuru domin bunƙasa fannin noma don wadata Najeriya da abinci da kuma sauko da farashin kayan abinci a faɗin ƙasar.
Haka ma shugaban na Najeriya ya ce ƙasar ta samu bunƙasar da ba a taɓa gani ba wajen tara kuɗin shiga a fannin da na mai ba.
''Zuwa watan Agustan 2025 mun samu kuɗin shiga a fannin da ba na mai ba, da ya kai naira tiriliyan 20. A watan Satumba kaɗai mun samu naira tiriliyan 3.65, ƙarin kashi 411 kan abin da aka samu a watan Mayun 2023'', in ji Shugaba Tinubu.
Hamas na ganawa da Qatar da Turkiyya kan yarjejeniyar Trump
Asalin hoton, Reuters
Bayanai na cewa jami'an Hamas da Qatar da Turkiya na tattaunawa a Doha bayan shugaba Trump ya ba ƙungiyar Hamas wa'adin kwana huɗu ta mayar da martani ga yarjejeniyarsa ta kawo karshen yakin Gaza.
Shugaban na Amurka ya gargaɗi Hamas cewa za ta ɗanɗanta kuɗarta idan ta yi watsi da yarjejeniyar.
Qatar - wadda ke bai wa shugabannin Hamas mafaka - ta ce ƙungiyar na nazari kan yarjejeniayr.
Rahotonni na cewa da wahala Hamas ta amince da tsarin ba tare da neman sauyi ba ga wasu buƙatun.
Yarjejeniyar ta ƙunshi kawo ƙarshen yaƙin Gaza da sakin dukkanin mutanen da ake tsare da su cikin kwana uku da kuma ajiye makaman Hamas
Najeriya ta samu gagarumin ci gaba tun bayan samun ƴanci - Tinubu
Asalin hoton, Fadar shugaban Najeriya
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ce ƙasar ta samu gagarumin ci gaba tun bayan samun yancin kai a 1960.
Yayin wani jawabi da ya gabatar wa ƙasar albarkacin cikar Najeriya shekara 65 da samun yancin kai, Shugaba Tinubu ya ce ƙasar ta samun ɓunkasa a fannin tattalin arziki da ci gaban zamantakewa da fannin ilimi.
''...dole ne a yaba wa ci gaban da ƙasarmu da samu. A yau Najeriya ta samu wadatuwar fannonin ilimi da kiwon lafiya fiye da lokacin da muka samu yancin kai'', in ji shi.
Shugaban na Najeriya ya ce a lokacin da ƙasar ta samu yancin kai a 1960, makarantun sakandire 120 ne a faɗin ƙasar, da ɗaliban da ba su wuce 130,000 ba.
'"Amma bisa alƙaluman da muke da su a 2024, akwai makarantun sakandire fiye da 23,000 a ƙasarmu'', in ji.
Haka ma ya ce a lokacin da ƙasar ta samu ƴancin kai Jami'ar Ibadan da Kwalejin Fasaha da ke Yaba ne kawai manyan makarantu a ƙasar, amma bisa alƙaluman 2024 akwai jami'o'i 274 da kwalejojin fasaha 183 da kwalejojin ilimi 236 a faɗin ƙasar, yana mai cewa wannan adadi ya ƙunshi na gwamnatin tarayya da na jihohi da ma masu zaman kansu.
An dakatar da ayyukan gwamnati a Amurka
Asalin hoton, Reuters
An dakatar da ayyukan gwamnatin tarayya a Amurka bayan kasa samun jituwa tsakanin ƴanmajalisar Democrats da Republican game da kasafin kuɗin ƙasar.
Matakin ya shafi ayyukan yau da kullum, kuma ma'aikata da dama ba za su samu albashi ba.
Wannan ne karon farko da aka rufe harakokin gwamnati bayan shekaru bakwai.
Gwamnatin za ta ci gaba da zama a rufe har sai ɓangarorin biyu sun cimma matsaya.
Ƴan Democrats na neman dawo da kuɗaɗen da aka zabtare na inshorar lafiya.
Donald Trump ya yi gargaɗin yin amfani da damar domin korar ma'aikata da kuma rage wasu ayyukan gwamnati
Assalamu alaikum
Masu bibiyar shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana da Talata.
Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.
Kuna iya bibiyarmu a shafukanmu da sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.