Kamfanin Orano ya sake shigar da Nijar ƙara kan haƙar Uranium
Kamfanin Orano na ƙasar Faransa ya sake shigar da sabuwar ƙara game da dambarwar da ke tsakaninsa na Jamhuriyar Nijar.
Bayan buƙatar farko da aka ƙaddamar a watan da ya gabata bayan janye izinin aiki na ma'adinan Imouraren, Orano a wannan karon ya yi ƙarar ne yana neman a tabbatar da abin da ya kira haƙƙinsa.
Kamfanin na Faransa wanda ya ƙwararre a fannin uranium, ya yi tir da yadda hukumomin mulkin sojan Nijar suka daƙile masa duk hanyoyin fitar da uranium daga wurin aikinsa na SOMAIR da ke ƙasar domin sayar da shi a kasuwanin duniya. Yanzu haka a wurin da ake ajiyar ma’adinan akwai sama da tan dubu ɗaya na ƙarfen uranium da darajar kuɗin shi ya haura Yuro miliyan 200.