Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 17/08/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 17 ga watan Agustan 2026.

Rahoto kai-tsaye

Aisha Babangida, Abdullahi Bello, Haruna Kakangi

  1. El-Rufai ya shigar da ICPC ƙara kan hana shi ganin iyalansa

    Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (ICPC) sabuwar ƙara ta naira biliyan 10 a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan hana shi ganin iyalansa yayin da hukumar ke tsare da shi.

    A cikin ƙarar da lauyansa Ubong Akpan ya shigar ranar 13 ga Agustan 2026, El-Rufai ya ce ICPC ta hana matarsa Aichatou Asabe da ɗansa Abba El-Rufai ziyartarsa, lamarin da ya ce ya tauye masa haƙƙinsa na samun kulawa daga iyalansa.

    Ya ce hana shi hulɗa da iyalansa ya hana shi samun abinci, magunguna da sauran muhimman abubuwan da iyalansa za su kawo masa yayin da yake tsare, duk ba tare da wani sahihin dalili na doka ko umarnin kotu ba.

    El-Rufai na kuma neman kotu ta ayyana cewa an karya masa haƙƙoƙinsa na ɗanadam da ƙundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

    Haka kuma yana neman diyyar naira biliyan 10 kan abin da ya bayyana a matsayin take haƙƙinsa.

  2. Isra'ila ta kama Falasdinawa tara bayan yahudawa sun ƙulle su a gidajensu

    Kamfanin dillancin labaran Falasdinu na Wafa ya ce dakarun Isra'ila sun kama Falasdinawa tara na iyali guda bayan sun shafe sa'o'i suna maƙale a gidansu sakamakon wani hari da yahudawa kama wuri zauna suka kai.

    Rahoton ya ce maharan sun kewaye gidan Mohammad Sabet Majid Hassoun da ke wajen ƙauyen Beit Imrin, arewa maso yammacin Nablus, na fiye da sa'o'i uku a daren Lahadi.

    Daga bisani ne sojojin Isra'ila suka mamaye yankin tare da kama duka mutane tara da ke cikin gidan.

    Wannan na zuwa ne yayin da wasu iyalai Falasdinawa uku ke ci gaba da kasancewa cikin gidajensu a ƙauyen Qusra da ke kudancin Nablus, bayan da yahudawan suka yi musu ƙawanya.

  3. Ambaliya ta mamaye wasu sassan Abuja

    Mamakon ruwan sama da aka yi a Abuja ya haddasa ambaliyar ruwa a wasu sassan Babban Birnin Tarayya, Abuja lamarin da ya jefa mazauna yankunan cikin halin ƙunci tare da katse zirga-zirga.

    Daga cikin wuraren da ambaliyar ta fi shafa akwai Wuse 2, musamman titin Adetokunbo Ademola, inda ruwa ya mamaye hanyoyi da muhallai.

    Bidiyoyi da suka karaɗe kafafen sada zumunta sun nuna yadda motoci da dama suka nutse a cikin ruwa ko kuma suke yawo sakamakon kwararowar ambaliyar.

    Haka kuma an ga direbobi da fasinjoji sun makale a wasu hanyoyi yayin da ruwa ya hana ababen hawa wucewa.

    Ambaliyar ta kuma shafi yankunan Gudu, Lokogoma da hanyar da ke haɗa Gaduwa da Durumi, inda ruwa ya mamaye gada tare da hana zirga-zirga.

    Wasu 'yan kasuwa sun rufe shaguna bayan ruwa ya shiga wuraren kasuwancinsu, yayin da mazauna yankunan suka yi kira ga hukumomi da su ɗauki matakin gaggawa.

    Lamarin ya sake tayar da hankali kan matsalar magudanan ruwa a Abuja, musamman ma bayan hukumomin hasashen yanayi sun yi gargadin yiwuwar aukuwar ambaliya a birnin a bana.

  4. Hare-hare kan tankokin mai sun rage zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz

    Rahotanni sun nuna cewa zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz ta ragu sosai cikin kwanaki biyun da suka gabata bayan hare-haren da aka kai wa tankokin ɗaukar mai a yankin.

    Lamarin na faruwa ne a daidai lokacin da tattaunawar Amurka da Iran kan warware rikicin da ke tsakaninsu ta tsaya cik.

    Bayanan kamfanin Kepler sun nuna cewa jiragen ruwa biyar ne kawai suka ratsa mashigar a ranar Asabar, yayin da babu ko jirgi guda da ya ratsa a ranar Lahadi.

    Wannan ya bambanta da yadda jiragen ruwa 31 suka ratsa mashigar Hormuz a ranar Asabar da Lahadi na makon da ya gabata.

  5. Gwamnatin Yemen ta ce ta kai hare-hare kan wuraren 'yan Houthi a sassa daban-daban

    Gwamnatin Yemen ta sanar da kai hare-haren bindigogi da na jiragen yaƙi marasa matuƙa kan wuraren mayakan Houthi a lardunan Al-Jawf da Marib.

    Dakarun gwamnatin, masu samun goyon bayan Saudiyya, sun ce sun kai hare-hare 181 a sassa daban-daban cikin kwanaki biyu, lamarin da suka ce ya yi sanadiyyar mutuwa da jikkatar mayaƙar da dama.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargadin cewa Yemen na fuskantar barazanar komawa cikakken yaƙi duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kafa tun 2022.

  6. Matakanmu na kare kai ne zuwa yanzu, amma za su iya komawa hare-hare - Iran

    Mataimakin shugaban harkokin siyasa na dakarun juyin juya halin Iran, Yadollah Javani, ya ce matakan da Iran ke ɗauka a yaƙin da ake yi a halin yanzu na kare kai ne, amma za su iya komawa na kai hare-hare a gaba.

    Da yake magana a wata hira da gidan talabijin da rediyon ƙasar Iran, Javani ya ce maƙiyan Iran ne suka fara yaƙin, kuma martanin Iran ya kasance na kare kanta.

    Iran ta kuma ce za ta ɗauki duk matakin da ya dace domin kare ƙasar da kuma daƙile barazanar maƙiya, tare da yiwuwar sauya salon martaninta idan lamarin ya buƙaci hakan.

    Ya ce rundunonin sojin Iran za su ɗauki sabbin matakai bisa umarnin da aka bayar, tare da ɗaukar duk wani mataki da ya dace don kare ƙasar, tabbatar da tsaro da kuma dakile barazanar maƙiya a lokacin da ya dace.

    Kalaman Javani na zuwa ne bayan mai bai wa babban kwamandan IRGC shawara, Mohammad Reza Naqdi, ya bayyana cewa Iran ta yanke shawarar sauya aƙidar soja daga ta kare kai zuwa wadda ta haɗa da kai hare-hare idan an ga hakan ya zama dole.

  7. Iran ta saka sharaɗin buɗe mashigar Hormuz

    Mataimakin shugaban harkokin siyasa na dakarun juyin juya halin Iran (IRGC), Yadollah Javani, ya ce Iran ba za ta buɗe mashigar Hormuz ba sai idan Amurka ta cika nauyin da ke kanta ƙarƙashin yarjejeniyar Islamabad.

    A wata hira da ya yi da Ƙungiyar Matasan 'Yan Jarida ta Iran, Javani ya ce dole ne yaƙin ya ƙare bisa tanadin yarjejeniyar Islamabad, yana mai ƙara da cewa buɗe mashigar Hormuz zai biyo bayan cika alƙawurran Amurka da ke cikin yarjejeniyar.

    Ya kuma ce mashigar Hormuz da tsarin da za a tafiyar da ita ba za su sake komawa yadda suke kafin ɓarkewar yaƙin ba.

    Javani ya zargi Amurka da Isra'ila tare da ƙawayensu da ƙoƙarin ƙwace ikon mashigar Hormuz daga hannun Iran tsawon watanni, amma ya ce duk da haka ba su yi nasara ba.

    Haka kuma ya ce tattaunawar da ake yi yanzu game da wata hanyar ruwa tsakanin Iran da Oman za ta kasance ne bayan ƙarshen yaƙin, yana mai jaddada cewa babu shakka yaƙin zai zo ƙarshe"

  8. Ana atisayen soji tsakanin Amurka da Koriya ta Kudu

    Ana ci gaba da gudanar da atisayen soji na shekara-shekara tsakanin Koriya ta Kudu da Amurka, duk da umarnin Shugaba Donald Trump na rage girman atisayen sosai.

    A wani saƙo da ya wallafa a kafafen sada zumunta, Mista Trump ya ce atisayen, wanda aka tsara domin tunkarar barazana irin su hare-haren intanet da kuma jiragen sama marasa matuƙa, yana da tsada kuma yana ɗauke da saƙon ƙiyayya ga Koriya ta Arewa.

    Atisayen yana da muhimmanci sosai ga alakar sojin Amurka da Koriya ta Kudu.

    Mista Trump ya ce kyakkyawar alaƙar da ke tsakaninsa da shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, na daga cikin dalilan da suka sa ya yanke wannan shawara.

    Matakin da Mista Trump ya ɗauka na iya zama wani babban sauyi a daɗaɗɗiyar dangantakar tsaro ta tsakanin Amurka da Koriya ta Kudu.

    A halin yanzu, Koriya ta Arewa ba ta fitar da wata sanarwa ko martani kan lamarin ba.

  9. Barka da warhaka!

    Masu bibiyar shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa,Barkanmu da Safiyar ranar Lahadi.

    Kamar kodayaushe, za mu kawo maku labarai game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida ce ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokacin.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.