Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 15/01/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Ibrahim Muhammad da Isiyaku Muhammed

  1. Al'ummar Birnin Gwari sun kira da a faɗaɗa sulhu da ƴanbindiga zuwa sauran jihohi

    Al'ummar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta faɗaɗa shirin sasanci da ƴanbindiga da aka yi a yankin zuwa sauran jihohin da ke fama da matsalolin rashin tsaro.

    Wannan kiran na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ƙungiyar ci gaban yankin masarautar Birnin Gwari wato Birnin Gwari Birnin Gwari Emirate Progressives Union (BEPU), wadda shugabanta Isah Muhammad ya sanya wa hannu.

    Sanarwar ta ce al'ummar yankin suna godiya da zaman lafiya da suka fara samu a sanadiyar sasancin, "amma muna kira da a faɗaɗa shirin zuwa sauran jihohin da suke fama da matsalar ƴanbindiga irin su Neja da Zamfara da Katsina da Sokoto domin hakan ne zai wanzar da zaman lafiya a faɗin ƙasar."

    Sanarwar ta kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jiha da su samar da ababen more rayuwa a yankin na Birnin Gwari, "akwai buƙatar a gyara titin Birnin Gwari zuwa Kaduna da na zuwa Funtua da zuwa Neja da na zuwa Tegina, wanda ya sada yankin da kudancin Najeriya."

    BEPU ta kuma kira ga kamfanonin sadarwa irin su MTN da Airtel da su dawo da hanyoyin sadarwarsu da suka katse a baya a yankin, sannan ƙungiyar ta yi kira a kafa jami'ar nazarin ayyukan noma saboda yadda ake noma a yankin.

    Yankin Birnin Gwari ya daɗe yana fama da matsalar tsaro, amma cikin ƴan kwanakin nan an fara samun zaman lafiya, inda harkokin kasuwanci da noma suka fara komawa yadda ya kamata bayan wani shirin sasanci da ƴanbindiga da gwamnatin ta jagoranta.

  2. An kama shugaban ƙasar Koriya ta Kudu da aka tsige

    Masu bincike kan zargi a Koriya ta Kudu sun kama shugaban ƙasar da aka dakatar, Yoon Suk Yeol.

    An tafi da shi domin amsa tambayoyi a kan tuhume-tuhumen da ake masa na tayar da zaune tsaye da cin zarafin mulki, sakamakon yunƙurin da ya yi na ayyana dokar mulkin soji a ranar 3 ga Disamban bara.

    Sai da ƴansanda suka kutsa ta cikin shingen da aka sanya don kare shi kana suka shiga har gida suka kamo shi.

    Sai dai ana buƙatar kotun kundin tsarin mulkin ƙasar ta tabbatar da tsige shi, kafin tsigewar ta tabbata.

  3. Kamfanin Orano ya dakatar da ayyukan kyautata muhalli a Nijar

    A ci gaba da takun-saƙa da gwamnatin Jamhuriyar Nijar ke yi da kamfanin ORANO na Faransa da ke aikin haƙar uranium a ƙasar, kamfanin ya sanar da dakatar da aikin cike ramuka don kyautata muhalli a wuraren da ya yi aiki.

    Aikin ya taso ne sanadiyar haƙar ma'adanan da tsohon kamfanin uranium na COMINAK wanda ya kawo ƙarshen aiki bayan shekara 50 a yankin Arlit.

    Haka kuma, kamfanin na ORANO ya sanar da dakatar da biyan albashin ma'aikatan tsohon kamfanin na COMINAK su 500 da ke aikin cike ramukan.

  4. Ƴansanda sun ƙi amsar cin hancin naira miliyan 1 kan binciken ƴan Lakurawa a Kebbi

    Jami'an ƴansandan jihar Kebbi sun ƙi karɓar cin hancin naira miliyan ɗaya daga wasu waɗanda ake zargi suna da alaƙa da ƴan Lakurawa.

    A wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansandan jihar Kebbi, Nafiu Abubakar, ya fitar, ya ce mutum uku: Umaru Garba daga ƙauyen Ɗangandu da Abubakar Mamman daga Maimaichi da Usman Muhammadu daga ƙauyen Bakaramba ne aka kama da laifin.

    Kakakin ya ce sun ba babban jami'in binciken wani ta'addanci da ake zargin ƴan Lakurawa da aikatawa a arewacin jihar Kebbi, inda suka kai kuɗin domin a rufe binciken.

    Ya ce ana cigaba da gudanar da binciken, sannan da zarar an kammala za a tura su kotu.

    Lakurawa wata sabuwar ƙungiyar ƴanbinda ne da ta ɓulla a yankin arewa maso yammacin Najeriya, da ma sassan Nijar.

  5. Ana fargabar gobarar Amurka za ta faɗaɗa

    Mummunar guguwa haɗe da iska mai ƙarfin gaske, na bazanar haifar da ƙarin gobara a sabbin wurare da dama na birnin Los Angeles, bayan shafe mako guda ƴan kwana-kwana na ta ƙoƙarin kashe wadda yanzu haka ake fama da ita a ƙasar.

    Masu hasashen suna yin gargaɗin wani yanayi mai hatsarin gaske da sanyin safiyar Laraba.

    Wakilin BBC ya ce hukumar hasashen yanayi ta ƙasa ta ce guguwar na iya maida hannun agogo bayan kan nasarar da aka samu ta cin ƙarfin wutar a wasu wurare.

    An yi ƙiyasin ta janyo asarar da ta kai ta dala biliyan ɗari biyu da saba'in da biyar. Gobarar ta shafe sama da mako guda tana ci ba tare da an iya kashe ta ba, inda ta lalata dubban gidaje da kashe aƙalla mutum 25.

  6. Dukkan ɓangarori sun nuna shirin amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

    Ana ci gaba da tattaunawa kan yarjejeniyar tsagaita wuta da sakin mutanen da aka kama a Gaza a ƙasar Qatar, inda dukkanin ɓangarorin ke nuni da cewa an kusa cimma yarjejeniya fiye da kowane lokaci.

    Sharuɗɗan da ake tattaunawa a kansu, sun haɗa da sakin ƴan Isra'ilar sannu a hankali da kuma musayarsu da na Falasɗinawa, da ma janye sojojin Isra'ila daga wasu yankuna.

    Isra'ila da Hamas dai sun bayyana fatan ganin an cimma matsaya a ƙarshe.

    Ita ma ƙungiyar Islamic Jihad da Falasɗinawa ta ce za ta aike da tawaga zuwa Qatar don shiga cikin tattaunawar.

  7. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Laraba, inda za mu kawo muku labaran abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sadarwa irin du X da Facebook da Instagram domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo.

    Ku kasance tare da mu.