Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 28/06/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed da Umar Mikail

  1. Abin fashewa ya kashe mutum huɗu a jihar Yobe

    Wani abin fashewa ya kashe mutum uku sannan wasu 21 suka ji raunika a titin Katarko-Goniri da ke ƙaramar hukumar Gujba ta jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya.

    Akasarin waɗanda suka rasu ƴan garin Gotata ne, kuma motarsu ce ta taka abin fashewar da ake zargi nakiya ce da aka binne, kamar yadda tashar talabijin ta Channels TV ta ruwaito.

    A cewar rahoton, garin Gotata na kusa da dajin Sambisa inda mayaƙan Boko Haram suka fake suna kai hare-hare.

    A ranar Laraba ma wani bam ya yi ajalin matafiya huɗu a jihar Borno mai maƙwabtaka da Yobe.

    Mayaƙan Boko Haram, waɗanda aka fatattaka a baya, sun ci gaba da zafafa kai hare-hare a baya-bayan nan a yankin, lamarin da ya sa ake fargabar ko hanun agogo ya fara komawa baya a yaƙin da ake yi da masu iƙirarin jihadi.

  2. Hotunan sallar jana'izar Aminu Ɗantata a Kano

    Da safiyar yau Asabar ne aka yi wa marigayi Aminu Ɗantata sallar jana'iza daga nesa bayan ya rasu a ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

    Shugaban majalisar malamai ta jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, shi ne ya jagoranci sallar da aka yi a Msallacin Umar bn Kattab da ke birnin.

    Ɗaruruwan mutane ne suka halarci jana'izar, ciki har da 'yansiyasa kamar mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Barau Jibrin.

    Iyalansa sun shaida wa BBC cewa suna neman izinin ƙasar Saudiyya domin binne gawarsa a can kamar yadda yake ta buri tun kafin rasuwarsa.

  3. Ɗan ƙunar baƙin wake ya kashe mutum 8 a Pakistan

    Hukumomi a ƙasar Pakistan sun ce aƙalla mutum takwas ne wani harin ƙunar baƙin wake ya kashe a arewa maso yammacin ƙasar.

    Ƴansandan ƙasar sun ce maharin ya kai hari ne a cikin wata mota, inda ya faɗa cikin ayarin motocin sojoji a lardin Khyber Pakhtunkhwa da ke kusa da bakin iyakar Afghanistan.

    Wannan harin na cikin hare-haren da ƙasar ke fuskanta a ƴan shekarun nan, waɗanda ake alaƙantawa da tsagin ƙungiyar Taliban na Pakistan da ake kira Tehreek-e-Taliban Pakistan.

  4. Tinubu ya ce Alhaji Aminu Ɗantata dattijon arziki ne mai kishin ƙasa

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya aike da saƙon ta'aziyarsa ta rasuwar Alhaji Aminu Ɗantata, attajirin ɗankasuwa da ya rasu a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, wanda ya rasu yana da shekara 94 a duniya.

    Tinubu ya bayyana rasuwar hamshaƙin ɗankasuwar, wanda aka binne a ƙasar Saudiyya a matsayin "rashi ga ƙasar baki ɗaya'.

    Tinubu ya yaba da gudunmuwar da marigayin ya bayar wajen ciyar da Najeriya gaba, "musamman a ɓangaren ilimi da kiwon lafiya," kamar yadda sanarwar da mai magana da yawun shugaban, Bayo Onanuga ya fitar.

    Tinubu ya ce, "mun yi rashi na babban ɗankasuwa, mai kishin ƙasa, kuma dattijon arziki wanda ya ya taimaka wajen gina ƙasarmu Najeriya."

    Tinubu ya ce za a riƙa tuna Ɗantata a matsayin ɗankasuwa mai sanin ya kamata wanda ya bayar da gudunmuwa wajen haɗin kan ƙasa ta hanyar kasuwancinsa da ayyukan jinƙai, "wanda ya amfanar da ƴan Najeriya da ba za su ƙirgu ba."

    A ƙarshe Tinubu ya jajanta wa iyalan marigayin tare gwamnati da al'ummar Kano baki ɗaya bisa.

  5. Talauci da rashin tsaro na iya barazana ga zaɓen 2027 - Rahoto

    Ƙungiyar fafutikar kare haƙƙin ɗan'adam da tabbatar da dimokuraɗiyya ta YIAGA Africa ta ce babban zaɓen Najeriya na shekarar 2027 na fuskantar barazana saboda ƙaruwar talauci da rashin tsaro a ƙasar.

    YIAGA ta bayyana haka ne a Abuja a lokacin da take gabatar da rahoton bincikenta, inda daraktan ƙungiyar, Samson Itodo ya ce talaucin da ya wa ƴanƙasar katutu zai iya jawo ƙaruwar sayen ƙuri'a a zaɓen, musamman ta hanyar amfani da abinci domin sayen ƙuri'a.

    Ya ce, "wannan zaɓen akwai alamar a yi amfani da kuɗi sama da zaɓukan baya. Yanayin talauci da yunwar da ƴanƙasar ke ciki zai sa a samu sauƙin sauya tunanin masu zaɓe," in ji shi, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

    Rahoton ya ƙara da cewa maimakon matsin tattalin arzikin da ƙasar ke ciki ya sa mutane su fusata su fito zaɓe, "akasin hakan za a iya samu, domin ƴansiyasa za su yi amfani da hakan domin sauya musu tunani da kuɗi."

    Rahoton ya kuma bayyana cewa ana samun ƙaruwar ƴanƙasar da suke dawowa rakiyar Hukumar INEC, wanda ƙungiyar ta ce ya ƙaru bayan zaɓukan gwamnonin jihohin Kogi da Edo.

  6. Ƴansanda sun kama tan 2.4 na hodar iblis a London

    Ƴansandan bakin iyaka a Birtaniya sun sanar da nasarar da suka samu ta kama tan 2.4 na hodar iblis.

    Jami'an tsaro sun ce wannan ne kamen hodar iblis mafi girma, wanda rundunar ta ce ya shigo ƙasar ne daga Panama ta tashar jirgin ruwa na London Gateway.

    Ƴansandan sun ce sun samu nasara ne bayan samun bayanan sirri kan harƙallar miyagun ƙwayoyin, wanda wasu gungun mutane ke yi.

    Hodar iblis ɗin an ƙiyasta za ta kai dala miliyan 120.

  7. An naɗa Damagun a matsayin Madakin Fune

    Masarautar Fune da ke jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya ta amince da naɗa shugaban riƙo na jam'iyyar PDP, Ambasada Umar Iliya Damagun a matsayin Madakin Fune.

    Mai Fune, maimartaba Alhaji Saleh Idriss Ibn Usman ne tabbatar da naɗin bayan amincewar ƴan majalisarsa, inda masarautar ta ce ta yi haka ne bisa la'akari da jajircewarsa wajen ciyar da masarautar gaba.,

    A wata sanarwa da hadimin Damagun, Nuru Shehu Jos ya fitar, ya ce shugaban riƙon na PDP ya yi godiya bisa naɗin, inda sanartar ta ƙara da cewa yanzu Damagun ya zama daga cikin masu naɗa sarki a masarautar.

    Ambasada Damagun ya yi godiya bisa naɗa shi da aka yi a masarautar, sannan ya yi alƙawarin cigaba da ba masarautar da ma al'ummarta gudunmuwa domin da ciyar da ƙasa gaba.

  8. 'An kashe mutum 19 a zanga-zangar Kenya'

    Hukumar kare haƙƙin bil'adama a Kenya ta ce adadin mutanen da aka kashe a lokacin zanga-zanga a ranar Laraba ya ƙaru zuwa 19, wasu 15 kuma sun yi ɓatan dabo.

    Dubban masu zanga-zanga ne suka bayyana fushinsu da gwamnatin Shugaba William Ruto tare da neman gwamnati ta ƙwato ƙarshen matsalar da ke ci masu tuwo a ƙwarya ta yadda ƴansanda ke cin zalin jama'a.

    Galibin masu zanga-zangar sun yi ta ihu suna furta cewa "Dole Ruto ya sauka" inda kuma suka riƙa ɗaga ganyaye a matsayin adawa ga mulkinsa cikin lumana.

    Gwamnati ta yi tur da yadda aka yi sata a wata ma'ajiyar taki yayin zanga-zangar inda ta yi gargaɗi cewa hakan na iya jefa ƙasar cikin matsalar abinci.

  9. Dalori ya maye gurbin Ganduje a matsayin shugaban APC na riƙo

    Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na yankin arewa, Ali Bukar Dalori ya maye gurbin Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar na riƙo.

    Wannan na zuwa ne bayan tsohon gwamnan na jihar Kano ya ajiye muƙamin a ranar Juma'a, sannan aka naɗa Dokta Ali Bukar Dalori a matsayin wanda zai riƙe muƙamin, kafin a kai ga zaɓen wanda zai maye gurbinsa.

    Mutane dai sun yi zargin ruwa ba ya tsami banza, ko kuma dai da walakin goro a miya amma uwar jam'iyyar ta yi watsi da wannan hasashe.

    Bala Ibrahim shi ne daraktan yaɗa labarai na jam'iyyar ta APC, ya ce "Game da batun wanda zai maye gurbin shugaban jam'iyyar da sauka, dama jam'iyya na da kundin tsarin mulki wanda ya yi tanadi irin wannan wanda idan shugaban jam'iyya ya sauka daga muƙaminsa to za a zaɓi ɗaya daga cikin mataimakansa biyu wanda ɗaya daga arewa ɗaya kuma daga kudu to sai a ba wanda ya fito daga yankin da shugaban da ya yi murabus ya fito a bashi riƙon ƙwarya kafin a gudanar da zaɓen wanda zai gaji kujerar."

    Ya ce," A wannan hali muƙaddashi na arewa tun da Ganduje daga shiyyar ya fito wanda shi ne Bukar Dalori, shi ne zai rike kujerar na wucin gadi har lokacin da aka zabi sabon shugaban jam'iyyar."

  10. A daina taɓa ƙimar Khamenei idan ana so a cimma yarjejeniyar nukiliya - Iran

    Ministan harkokin wajen Iran ya yi tur da abin da ya kira kalaman rashin girmamawa da Shugaba Donald Trump ya yi bayan da shugaban ya yi iƙirari cewa ya tseratar da Jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei daga rasa ransa.

    Abbas Araghchi ya ce idan Mista Trump da gaske yana son a cimma yarjejeniyar nukiliya da Iran, ya kamata ya daina ci wa Mista Khamenei da miliyoyin mabiyansa fuska.

    A manhajarsa ta Truth Social, Mista Trump ya yi iƙirarin cewa ya hana yi wa jagoran na Iran mummunan kisan wulaƙanci a hare-haren Isra'ila inda kuma ya zarge shi da rashin nuna godiya.

  11. Abin da ya sa Ganduje ya yi murabus daga mukaminsa — APC

    Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta yi ƙarin haske kan dalilan da suka sa Abdullahi Umar Ganduje, ya sauka daga muƙamin shugabancin jam'iyyar a wani yanayi na ba-zata.

    Mutane dai sun yi zargin ruwa ba ya tsami banza, ko kuma dai da walakin goro a miya amma uwar jam'iyyar ta yi watsi da wannan hasashe.

    Daraktan yaɗa labarai na jam'iyyar ta APC, Bala Ibrahim, ya shaida wa BBC cewa babban dalilin da Ganduje ya bayar a game da murabus din na sa shi ne batun kiwon lafiya.

    Ya ce," Ganduje ya nemi a amince ya sauka daga mukamin shugaban jam'iyya saboda ya mayar da hankali wajen kula da lafiyarsa."

  12. MDD ta yi maraba da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Congo da Rwanda

    Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi maraba da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma tsakanin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo da Rwanda, matakin da ya bayyana a matsayin hanyar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin gabashin Congo.

    Ana kallon yarjejeniyar wadda Amurka da Qatar suka shiga tsakani a matsayin matakin farko na kawo ƙarshen yaƙin da aka shafe shekara shekaru ana gwabzawa wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane.

    Wakiliyar BBC ta ce Congo da Rwanda da ma Shugaba Trump sun yaba da yarjejeniyar da suka ce ta yi nasara kuma za ta tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa ga jama'ar da ke gabashin Congon. Bayanai na cewa zuwa yanzu babu tabbas kan yadda ƙasashen za su tabbatar da cewa ƴantawayen da ke gabashin Congo za su mutunta yarjejeniyar ko kuma sojojin Rwanda za su janye daga garin.

  13. Iran ta yi jana'izar kwamandojin sojinta da masana nukiliya waɗanda Isra'ila ta kashe

    Iran ta gudanar da jana'izar mutum 60, ciki har da kwamandojin sojinta da masana nukiliya da Isra'ila ta kashe a kwana 12 da suka yi suka gwabza yaƙi.

    An gudanar da jana'izar ce ta karramawa, inda aka lulluɓe gawarwakinsu da tutar Iran, sannan dandazon mutane suka halarta sanye da baƙaƙen kaya domin jimami da kuma karrama waɗanda suka rasun.

    A farkon makon ne aka kawo ƙarshen yaƙin ta hanyar shiga yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin ƙasashen biyu bayan Amurka ta shiga tsakani.

    Amurka ta kai hare-hare ne a cibiyoyin nukiliyar Iran, inda ta sanar da cewa ta samu nasarar tarwatsa cibiyoyin, waɗanda dama a kansu ake yaƙin.

    Daga cikin waɗanda aka binne akwai Mohammed Bagheri, wanda babban hafsan soji ne a ƙasar ta Iran, kuma shugaban ma'aikata a rundunar sojin ƙasar.

    Akwai kuma Hossein Salami, wanda kwamandan dakarun juyin juya-hali ne na Iran, da masanin nukiliyar ƙasar Mohammad Mehdi Tehranchi.

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi mamatan sun sadaukar da kansu domin ƙasar.

    Jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei bai samu halartar jana'izar, lamarin da ake dangantawa da barazanar tsaro.

  14. Trump ya ce zai yanke alaƙar kasuwanci da Canada

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai yanke dukkan alaƙar kasuwanci da ƙasar Canada, inda ya ce ya ɗauki wannan matakin domin ƙasar ta fara lafta haraji kan kamfanonin fasahar zamani.

    Trump ya bayyana haka ne a kafofin sadarwa na zamani, lamarin da ke zuwa bayan ƙasashen maƙwabta sun fara tattaunawa kan shiga yarjejeniyar kasuwanci a watan Yulin da ya gabata.

    Ƙasashen biyu dai sun lafta wa juna harajin kasuwanci, tun bayan da Trump ya yi barazanar mamaye ƙasar ta hanyar amfani da ikon tattalin arziki.

    A ranar Juma'a ce Trump ya ce zai yanke duk wata tattaunawa da ke tsakaninsu saboda Canada tana takuwa wa kamfanonin fasahar zamani da haraje-haraje, sannan ya ƙara da cewa zai sanar da sabon haraji kan kayayyakin ƙasashen a mako mai zuwa.

  15. Allah Ya yi wa Alhaji Aminu Dantata rasuwa

    Allah ya yi wa attajirin ɗan kasuwar nan na Najeriya, Alhaji Aminu Ɗantata rasuwa.

    Hamshain attajirin ya rasu ne a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa bayan fama da jinya, kamar yadda wani ɗansa ya bayyana wa BBC.

    Ɗantata ya rasu ne yana da shekara 94 kuma ya rasu ya bar ƴaƴa da jikoki.

    Aminu Ɗantata ɗa ne wajen marigayi Alhaji Alhassan Ɗantata, fitaccen attajirin da ya tashe a ƙarni na 20, inda shi ma ya taso cikin harkokin kasuwanci ta hanyar ɗaurawa daga inda mahaifinsa ya tsaya.

  16. Buɗewa

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Asabar daga nan sashen Hausa na BBC.

    Da fata za ku kasance tare da mu domin kawo muhimman labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.