Ɗan Bobi Wine ya ce jami'an tsaro sun 'ɗauke' iyayensa
Ɗangidan jagoran adawar Uganda ya ce sojoji da wasu jami'an tsaro na musamman sun sace iyayensa daga gidansu da ke Kampala.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin sa na X, Solomon Kampala ya ce an ''ɗauke Bobi Wine da Barbara Kyagulanyi tare da kai su wani ɓoyayyen wuri.
Wani makusancin Wine ya shaida wa BBC cewa jami'an tsaron sun shiga gidansa da ƙarfin tsiya sannan suka ɗauke a wani jirgi mai saukar ungulu.
Tun farko Bobi Wine ya soki ingancin sakamkon farko na zaɓen shugaban ƙasar da ya gudana ranar Alhamis, wanda ya nuna Shugaba Yoweri Museveni ne ke kan gaba da gagarumar tazara, yayin da aka kusan kammala ƙirga ƙuri'u.
Sai dai rundunar ƴansandan ƙasar ta musanta iƙirarin sace Wine.
A yau Alhamis ne ake sa ran bayyana sakamkon zaɓen, wanda tuni ake hasashen Museveni ne zai lashe.