Thailand ta saki sojojin Cambodia 18 bayan amincewa da tsagaita wuta
Thailand ta saki sojojin Cambodia 18 wadanda ta kama a watan Yulin da ya wuce a yayin wata mummunar gwabzawa da ƙasashen biyu suka yi akan iyaka.
Gwamnatocin ƙasashen biyu sun tabbatar da miƙa sojojin, wanda aka yi kwanaki hudu bayan ƙasashen da ke makwabtaka da juna sun amince da tsagaita wuta.
A watan Yulin daya wuce, dangantaka tsakanin ƙasashen wato Thailand da Cambodia ta yi tsami inda ta koma fada akan iyaka.
Tun daga nan ne kuma aka kashe gwamman mutane sannan kuma mutane wadanda ke zaune a kusa da iyakar kusan dubu 500 suka bar muhallansu.