An ceto wani ɗan Rasha
bayan kwashe sama da watanni biyu a cikin ruwa a wani karamin kwale-kwale a tekun Okhotsk da ke gabashin ƙasar.
Jami’ai sun ce wani ma’aikacin jirgin ruwa ne ya gano mutumin mai suna Mikhail Pichugin mai shekaru 46 a duniya, kusan nisan kilomita 1,000 daga inda ya taso a
farkon watan Agusta.
Rahotanni sun ce an gano gawar ɗan uwansa da kaninsa mai
shekaru 15 a cikin jirgin.
Matar Mista Pichugin ta ce
mutanen uku sun je teku ne don kallon yadda kifaye ke rayuwa kuma sun tafi da kayan abinci na
tsawon makonni biyu.
Ta shaida wa kamfanin
dillancin labaran ƙasar Rasha Ria Novosti cewa nauyinsa na iya zama sanadiyyar ceto - yana da nauyin kilogiram 100 lokacin da suka yi tafiyar.
"Ba mu san komai ba zuwa yanzu. Mun dai san yana da rai... Wani irin abin al'ajabi ne!" kamar yadda matar mutumin ta bayyana.
Ta kuma ce dama ’yarsu ya kamata ta
tafi da su a balaguron, amma ta yanke shawarar komawa gida.
Wani jirgin sama mai saukar
ungulu ya gano babu wata alama ta mutanen uku bayan da aka bayar da
rahoton ɓacewarsu, a cewar Ria.
An gano jirgin ne ranar Litinin yayin da ya ke zagayawa a gaban wani jirgin kamun kifi a gaɓar tekun Kamchatka da ke gabashin Rasha.