Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da yake kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail, Ahmad Bawage, Nabeela Mukhtar, Abdullahi Bello Diginza da Isiyaku Mohammed

  1. Rufewa

    A nan muka kawo ƙarshen wannan shafi da muke kawo muku labaran abubuwan da suka faru a Najeriya da sauran sassan duniya. Da fata kun ji daɗin kasancewa tare da mu.

    A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.

  2. An tsinci gawarwaki 12 da ake tunani na ƴanbindiga ne a Abuja

    Ƙauyan Tokulo da ke ƙaramar hukumar Bwari a babban birnin tarayya Abuja sun shiga ruɗu sakamakon tsintar gawarwaki guda da aka yi a garin da ake tunanin ƴanbindiga ne.

    Kansilan mazaɓar Igu a yankin, Jerry Alkali ya shaida wa Daily Trust cewa mutane ne suka kira shi da misalin ƙarfe 2 zuwa 3 na daren Litinin, cewa suna ta jin harbe-harbe.

    Ya ce, "ranar babu wanda ya iya barci. Da safiya da mutane suka fara zuwa tafiya zuwa gona suka fara ganin gawarwaki a wata hanyar tafiya ƙaramar hukumar Kagarko da ke jihar Kaduna," in ji shi.

    Jaridar mai zaman kanta ta ruwaito cewa mutanen garin sun ce a cikin gawarwakin babu ɗan garin, wanda a cewarsu ke nufin ko dai an kashe a musayar wuta, ko kuma an kashe ne a wani wurin daban, aka kwaso gawarwakin aka kawo ƙauyensu.

    Har zuwa lokacin haɗa labarin a a samu kakakin rundunar ƴansanda Abuja Josephine Adeh a waya ba.

  3. Sojoji sun kashe ƴanbindiga da suka je karɓar kuɗin fansa a Kaduna

    Sojoji sun kashe wasu da ake zargi ƴanbindiga ne a daidai lokacin da suke niyyar karɓar kuɗin fansa a ƙauyen Mai-Iddo da ke ƙaramar hukumar Kachia a jihar Kaduna.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa sojojin bayan kashe ƴanbindigar, sun koma ceto mutanen, waɗanda uku mata ne, da wani yaro ɗaya da aka sace a makon jiya.

    "An yi tsari ne da sojojin a kan cewa wani mutum zai je kai kuɗin fansa, su kuma su bi baya. Haka kuwa aka yi, ƴanbindigar na fitowa sai sojojin suka fito, suke buɗe musu wuta, suka kashe su a nan take," kamar yadda wani jagoran al'umma ya bayyana wa Daily Trust.

    Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, kakakin ƴansandan Kaduna bai yi magana kan lamarin ba.

  4. Adadin waɗanda suka rasu a fashewar tankar mai a Jigawa ya kai 147

    Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya ta ce adadin waɗanda suka rasu a sanadiyar fashewar tankar mai a jihar Jigawa ya kai 147, sannan kusan 90 suna asibiti.

    Lamarin wanda ya auku da tsakar daren Talata, ya yi muni ne saboda mutane da dama sun zo wurin ɗibar man da ke zuba daga cikin motar bayan ta faɗi.

    An samu ƙaruwar waɗanda suka rasu ne daga cikin waɗanda suke kwance suna jinya a asibiti, bayan an yi wa wasu jana'iza.

  5. 'Babu giɓin shugabanci duk da cewa Tinubu da Shettima ba sa Najeriya'

    Fadar shugaban ƙasar Najeriya ta ce ba za a samu giɓin shugabancin ƙasar ba duk da cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima ba sa ƙasar.

    Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara a kan watsa labarai, Bayo Onanuga ya fitar.

    Ya fitar da sanarwar ce bayan mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya tafi Sweden domin ziyarar aiki, alhalin Tinubu bai dawo ƙasar daga hutun mako biyu da ya tafi ba.

    Ya ce, "Ya kamata a gane cewa shugaban ƙasa da mataimakinsa suna cigaba da gudanar da ayyukansu, ko da ba sa ƙasar. Shugaba Tinubu ya bar ƙasar nan ne a ranar 3 ga Oktoba, inda ya je hutun mako biyu, amma duk da haka bai daina gudanar da harkokin shugabanci ba, kuma ya kusa dawowa ofis.

    "Mataimakinsa kuma yau ya tafi. Amma sauran ɓangarorin gwamnati kamar shugaban majalisar dattawa da sakataren gwamnati da ma'aikatu da da manyan hafsoshin tsaro kowa na cigaba da aiki yadda ya kamata," in ji shi.

    Ya ce ko a zamanin mulkin Muhammadu Buhari an samu haka, inda shugaba da mataimakinsa suka bar ƙasar, "lokacin da Buhari ya je taron MDD 77, shi kuma mataimakinsa ya halarci birne Sarauniyar Ingila Elizabeth II.

    "Kuma ko a wannan gwamnatin an taɓa samun haka a baya, inda a tsakanin watannin Afilu da Mayu lokacin shugaba Tinubu yana Landan, shi kuma Shettima ya tafi Nairobi, amma kuma harkokin gwamnati babu abun da ya tsaya."

    A ƙarshe ya ce a wannan zamani da ake ciki na cigaban fasahar zamani, kundin tsarin mulkin ƙasar bai ayyana cewa dole sai shugaba ko mataimakinsa suna a kowane lokaci ba ne za su iya gudanar da mulki.

  6. Gidaje sun ƙone a sanadiyar faɗuwar tankar mai a Ogun

    A ranar Laraba ne wata tankar mai ta kama da wuta bayan ta faɗi a garin Ibafo da ke ƙaramar hukumar Obafemi-Owode da ke jihar Ogun, inda gidaje da motoci da dama suka ƙone, sannan mutum biyu suka jikkata.

    Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya auku ne a babbar hanyar Lagos zuwa Ibadan, inda ganau suka ce tayar motar ce ta fashe, sai ta faɗi, inda ta tankin ya fashe wanda shi ne sanadiyar wutar.

    Kakakin hukumar kula da sufuri da ababen hawa na jihar Ogun, Babatunde Akinbiyi ya tabbatar da lamarin.

    Shi ma kakakin ƴansandan jihar ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce wutar ta kai har wani gidan mai mai suna Osadole, inda ta ƙona manyan motoci biyu da aka ajiye a waje.

  7. Hotunan kayayyakin agaji daga Masar suna jiran izinin shiga Gaza

  8. Shettima ya tafi ziyarar aiki a ƙasar Sweden

    A yau Laraba ne ake sa ran mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima zai tashi domin tafiya ziyarar aiki ta kwana biyu a ƙasar Sweden.

    Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun mataimakin shugaban ƙasar, Stanley Nkwocha ya fitar.

    "Mataimakin shugaban ƙasar zai dawo gida Najeriya ne a ranar Asabar. Zai kuma zanta da wasu manyan jami'an gwamnatin ƙasar a kan wasu abubuwa da suka shafi cigaban ƙasashen biyu, ciki har da ganawa ta musamman da yariman ƙasar da firaiminista," kamar yadda sanarwar ta nuna.

    Kakakin ya ce Shettima zai yi amfani da ziyarar domin samo wa Najeriya damaraki a fannin fasahar zamani da ilimi da sufuri da noma da ma'adinai.

    Shettima zai yi tafiyar ne a yau da ake tsammanin dawowar Tinubu daga tafiya hutun da ya yi na mako biyu.

  9. TikTok ya goge bidiyo miliyan 2.1 a Najeriya

    Shafin TikTok ya ce ya goge bidiyoyi sama da miliyan 2.1 a Najeriya a cikin wata shida na farkon 2024 saboda saɓa ƙa'idojinsu.

    Kamar yadda rahoton tabbatar da bin dokokin amfani kafar da aka kamfanin ya fitar a ranar Talata ya nuna, kamfanin ya ce ya ɗauki matakin ne a cikin ƙoƙarin da yake yi na tabbatar da samar da daidaito da kuma tsabtace kafar.

    "Bincike ya nuna cewa kashi 99.1 na bidiyoyin nan an cire su ne tun kafin a kawo ƙarar su, sannan kashi 90.7 an cire su ne a cikin awa 24. Waɗannan alƙaluman suna tabbatar da ƙoƙarin kamfanin TikTok na hana yaɗa abubuwa marasa kyau, domin tabbatar da samar da kafa mai kyau ga ma'abota kafar a Najeriya," kamar yadda rahoton ya nuna.

    Sai dai waɗannan bidiyoyin da aka goge ba su ma kai kashi ɗaya cikin ɗari ba na bidiyoyin da ƴan Najeriya suka ɗora a zamanin watannin da aka yi nazari domin wannan rahoton.

    A duniya, TikTok ta ce ta cire sama da bidiyoyi miliyan 178 a watan Yunin 2024, inda ta ce bidiyoyi miliyan 144 daga ciki kwamfuta ce ta goge su.

  10. Fashewar tanka a Jigawa: Gwamnatin Najeriya na alhinin waɗanda suka rasu

    Gwamnatin Najeriya ta bayyana alhininta kan rasuwar mutum fiye da 100 sakamakon mummunar fashewar tankar mai a jihar Jigawa da ke arewacin ƙasar.

    Cikin wata sanarwar daga ofishin mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Kashim Shettima ta bayya amataimakain a madadin shugaban ƙasar na aikewa da saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan mutanen da suka rasu a iftila'in.

    ''Ina jajanta wa iyalan mutanen da suka rasa rasu sakamakon wanna mummunan iftila'i'', in ji Shettima.

    "Wannan batu ya yi matuƙar girgiza mu. Gwamnatin tarayya tana jajanta wa mutanen jigawa kan wannan al'amari''.

    Haka kuma mataimakin shugaban ƙasar ya alƙawarta cewa gwamnatin tarayya za ta binciki lamarin tare da kiran sake nazartar ƙa'idojin kariya wajen jigilar man fetur a faɗin ƙasar.

  11. Firaiministan Lebanon ya yi Alla-wadai da harin Isra'ila a Nabatieh

    Firaministan Labanon ya yi Allah-wadai da harin da Isra'ila ta kai birnin Nabatieh - wanda ofishinsa ya ce "da gangan aka kai hari kan taron majalisar ƙaramar hukumar".

    Najib Mikati ya ce wannan sabon harin ''wuce gona da iri ne kuma laifukan da Isra'ila suka aikata kan fararen hula, abin damuwa ne ganin cewa duniya ta yi shiru kan abin''.

    Ya kuma nuna shakku kan yiwuwar batun tsagaita wuta da Majalisar Ɗinkin Duniya ke jagoranta, “saboda dukkan ƙasashen duniya ba su iya daƙile hare-haren da Isra'ila ke kai wa al’ummar Lebanon ba.

    "Me zai iya hana maƙiya aikata laifukan da suka kai har kan kan dakarun wanzar da zaman lafiya a kudancin ƙasar? Wace mafita za a yi fatan samu daga wannan rikici?", in ji firaministan.

  12. Isra'ila ta ce ta kashe wani kwamandan Hamas a Gaza

    Yayin da Isra'ila ke kai hare-hare ta sama da kuma ƙasa a Lebanon, hakan bai hana ta ci gaba da yaƙi a Gaza ba.

    Sojojin Isra'ilar sun ce sun kashe wani kwamandan Hamas ta hanyar amfani da jirgi marasa matuƙi a arewacin Zirin Gaza.

    Sojojin sun ce kwamandan mai suna Mahmoud al-Mabhouh, ya kai hare-haren jirage marasa matuƙa zuwa cikin Isra'ila.

    Sai dai Hamas ba ta ce komai ba kawo yanzu.

    Isra'ilar ta kuma ce sojojinta sun kashe sama da ƴan ta'adda 50 a yankin Jabalia na Gaza.

    A ranar Talata, ma'aikatar lafiya ƙarƙashin ikon Hamas a Gaza ta ce Isra'ila ta kashe mutum 42,344 a Gaza tun fara yaƙi ranar 7 ga watan Oktoban bara.

    A jiya ne kuma Amurka ta bai wa Isra'ila wa'adin kwana 30 don bayar da damar ƙara yawan agajin da ake kai wa Gaza ko kuma ta fuskanci barazanar yanke mata tallafin agajin soji.

  13. Gwamnatin Nijar ta sauya wa titina suna masu ɗauke da sunayen Faransawa

    Gwamnatin mulkin soji a Jamhuriyar Nijar ta sauya sunayen tituna da duk wasu abubuwa da ke ɗauke da sunayen Faransa, a ƙoƙarin da ƙasar ke yi na yanke duk wata hulɗa tsakaninta da tsohuwar gijiyarta.

    Mai magana da yawun gwamnatin sojin Col Maj Abdurrahman Amadu ne ya sanar da hakan, tare da kare matakin da cewa ya zama wajibi domin maye gurbin sunayen da gwarazan jamhuriyar ta Nijar.

    Manjo Abdurrahman Amadu ya ce yawancin sunayen da aka sanya wa manyan titunan birnin Yamai, babu abin da suke tunawa ‘yanƙasar face baƙar wuyar da suka sha da uƙuba a lokacin mulkin mallaka da Faransa ta yi wa ƙasar.

    An sauya titin nan da ke ɗauke da sunan janar Charles de Gaulle na Faransa, tare da maye gurbinsa da sunan fitaccen ɗan siyasar nan na Nijar Djibo Bakary, wanda ya taka muhimmiyar rawa a lokacin kokawar karɓar ‘yancin kai.

    Sai kuma Place de la Francophonie da ya koma Place de l’Alliance des États du Sahel (AES)”, domin tunawa da haɗin kan ƙasashen yankin sahel da jamhuriyar Nijar ta ƙulla da maƙwabtanta wato Mali da Burkina Faso domin ƙarfafa tsaro da siyasar ƙasashen.

    Kungiyar ƙasashen yankin Sahel ta La Francophonie ta dakatar da su daga cikinta tun bayan juyin mulkin da sojojin ƙasashen suka yi wa gwamnatocin farar hula.

    A wani mataki na yauƙaƙa dangantaka tsakanin Nijar da makwabtanta, gwamnati ta maye gurbin mutum-mutumin kwamandan Faransa Parfait-Louis Monteil, da na fitaccen ɗan gwagwarmayar nan na Afirka kuma shugaban Burkina Faso da aka kashe Thomas Sankara.

    Kawo yanzu ba a san martanin da Faransa za ta mayar kan hakan ba, sai dai abin ba zai zo da mamaki ba ganin cewa ba wannan ne karon farko da sojojin yankin Sahel ke ɗaukar mataki irin wannan a kan tsohuwar gijiyar ta su ba.

    Tun bayan hamɓarar da mulkin shugaba Muhammad Bazoum a shekarar da ta gabata, gwamnatin mulkin sojin Nijar ta yanke duk wata hulɗa da Faransa da sauran ƙasashen yammacin duniya.

    Sun kuma haɗa kai da ƙasashen Mali da Burkina Faso wajen kafa ta su ƙungiyar, da gayyato Rasha domin taimaka mata a fannin soji, don yaƙi da masu ta da ƙayar baya da masu iƙirarin jihadi a yankin Sahel.

    Duk da taimakon da Rashar ke bai wa yankin, har yanzu ƙasashen uku na fama da matsalar masu iƙirarin jihadin.

  14. A shirye muke mu mayar da martani idan Isra'ila ta far mana - Iran

    Yayin da Isra'ila ke kai hare-hare a Lebanon da Gaza, har yanzu yankin na dakon ganin yadda - ko yaushe - za ta kai wa Iran hari.

    A ranar 1 ga Oktoba, Iran ta harba maƙamai masu linzami kusan 200 zuwa Isra'ila, sai dai an kakkaɓo mafi yawansu.

    A lokacin, Firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce Iran "za ta ɗanɗana kudarta" - amma har yanzu babu wani martani na soji.

    Ministan harkokin wajen Iran ya tattauna da babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres a daren jiya – ya kuma ce Iran a shirye take ta mayar da martani idan Isra’ila ta kai mata hari.

    "Iran, yayin da take ƙoƙarin kare zaman lafiya da tsaro a yankin, ta shirya tsaf don mayar da martani mai tsauri kan duk wata kasada ta Isra'ila," kamar yadda Abbas Araghchi ya faɗa wa Guterres, a cewar ma'aikatar harkokin wajen Iran.

  15. Motoci 50 ɗauke da kayan agaji sun nufi arewacin Gaza, in ji Isra'ila

    Bayan sanya hannu kan wata wasika da ke buƙatar Isra'ila ta bar kayan agaji ya shiga Gaza da Amurka ta yi, an sanar da ganin motoci ɗauke da kayan agaji suna shiga arewacin Gaza da lamarin ya fi shafa.

    Wannan ya biyo rashin kai agaji na tsawon makonni biyu zuwa arewacin Gaza, a cewar MDD.

    Sojojin Isra'ila sun ce motoci 50 ɗauke da kayan agaji - ciki har da abinci, da ruwa da kuma magunguna da ƙasar Jordan ta bayar - suka shiga arewacin zirin Gaza a yau ta mashigar Allenby da kuma mashigar yamma.

    Sojojin sun ce an bar kayan agaji su shiga bayan gudanar da bincike, kuma za su yi aiki da dokokin jin-kai na ƙasa da ƙasa wajen samun saukin shigar da agaji Gaza.

  16. Yadda aka yi jana'izar mutum 104 da suka mutu a fashewar tanka

    An yi jana'izar sama da mutum 100 da suka rasu sakamakon fashewar tankar mai a jihar Jigawa cikin juyayi.

    Gwamna Umar Namadi da manyan jami'an gwamnati ne suka jagoranci jana'izar a garin Majiya na ƙaramar hukumar Taura, inda hatsarin ya faru.

    An binne mutanen 104 a cikin babban ƙabari ɗaya da aka haƙa.

  17. Messi ya ci kwallo uku rigis, Argentina ta lallasa Bolivia da ci 6-0

    Lionel Messi ya ci kwallo uku a wasan neman shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a 2026, wanda Argentina ta doke Bolivia 6-0.

    Wannan ne karo na 10 da Messi ke ci wa Argentina kwallo uku a wasa guda a tarihi.

    Dan wasan gaban Inter Miami mai shekara 37, wanda ya bayar da kwallo biyu aka ci a filin wasa na Monumental da ke birnin Buenos Aires, ya kamo takwaransa na Portugal Cristiano Ronaldo a yawan cin kwallo uku a ƙasarsu.

    Argentina da ke saman teburi ta bai wa Colombia maki uku a wasannin neman gurbin gasar kofin duniya ta 2026, duk da cewa ta yi rashin nasara a watan Satumba da kuma canjaras da Venezuela a makon jiya.

  18. An kashe uku an jikkata 54 a harin Isra'ila a ƙauyen Qana na Lebanon

    Ma'aikatar lafiya a Lebanon ta ce mutanen da suka mutu a harin Isra'ila a ƙauyen Qana, kusa da birnin Tyre na Lebanon sun kai uku.

    Ta kuma ce kusan mutum 54 aka jikkata.

    jami'ai dai na ci gaba da aikin ceto a cikin ɓaraguzai.

  19. Hotuna: Yadda al'amura suke bayan harin Isra'ila a kudancin Lebanon

    Mun samu hotuna na yadda al'amura suke bayan harin da Isra'ila ta kai Qana, kusa da birnin Tyre da ke kudancin Lebanon.

    Masu aikin ceto na ci gaba da aiki cikin ɓaraguzai.

  20. An yi jana'izar mutanen da tankar mai ta kashe a Jigawa

    An gudanar da jana'izar mutanen da suka mutu sakamakon fashewar wata tankar mai a jihar Jigawa.

    Gwamna Umar Namadi da manyan jami'an gwamnati ne suka jagoranci jana'izar a garin Majiya na ƙaramar huukumar Taura, inda hatsarin ya faru.

    Zuwa yanzu dai hukumomi sun ce waɗanda suka mutu sun kai 104, yayin da sama da 100 kuma suka jikkata.

    Shaidu sun shaida wa BBC cewa tankar ta yi kusan awa biyu tana ci da wuta kafin jami'an kashe gobara su yi nasarar kashe ta.