Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Labarin wasanni daga 18 zuwa 24 ga watan Oktoban 2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 18 zuwa 24 ga watan Oktoban 2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Wasan Bayern Leverkusen da Paris St Germain, Champions League

    Wasan da Bayern Leverkusen za ta karbi bakuncin Paris St Geramin a yammacin Talata zai ja hankalin yan kallo.

    Karo na uku da za su hadu a gasar zakarun Turai tun bayan 2013/14, inda PSG ta je Jamus ta dura 4-0 a wasa na biyu a Faransa ta yi nasara 2-1.

  2. Jannick Sinner ba zai buga wa Italiya Davies Cup

    Jannick Sinner ya yanke shawarar ba zai buga gasar kwallon tennis ta Davies Cup ba, bayan da Italiya mai rike da kofin ta sanar da hakan ranar Litinin.

    Sai dai kuma wanda yake na ɗaya a ƙwallon tennis a duniya, Carlos Alcaraz zai wakilci Sifaniya a gasar da za a buga a watan gobe.

    Sinner wanda yake na biyu a ƙwallon tennis a duniya, ya ja ragamar Italiya ta lashe kofin bara, amma yanzu ba zai shiga wasannin da za a fara daga ƴan huɗun karshe ba da Bologna za ta karbi bakunci daga 18 zuwa 23 ga watan Nuwamba.

  3. Barcelona da Olympiokos a gasar zakarun Turai, Champions League

    Barcelona za ta karɓi bakuncin Olympiokos a wasa na uku a cikin rukuni a Champions League ranar Talata

    Wannan shi ne karo na uku da za su fafata a tsakaninsu a gasar tun bayan 2017/18, inda Barcelona ta ci 3-1 a wasan farko a Sifaniya da aka je girka suka tashi ba ci.

    Ƴan wasan Barcelona da za su fuskanci Olympiokos:

    Masu tsare raga: 25. Wojciech Szczesny, 31. Diego Kochen, 33. Eder Aller

    Masu tsare baya: 3. Alejandro Balde, 4. Ronald Araujo, 5. Pau Cubarsí, 18. Gerard Martín, 23. Jules Kounde, 24. Eric Garcia, 26. Jofre Torrents, 42. Xavi Espart

    Masu buga tsakiya: 8. Pedri, 16. Fermín López, 17. Marc Casadó, 21. Frenkie de Jong, 22. Marc Bernal, 27. Dro Fernández

    Masu cin ƙwallaye: 7. Ferran Torres, 10. Lamine Yamal, 14. Marcus Rashford, 28. Roony Bardghji, 29. Toni Fernández, 41. Juan Hernández.

  4. Kompany ya tsawaita yarjejeniyarsa da Bayern Munich

    Mai horar da Bayern Munich, Vincent Kompany ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da jan ragamar ƙungiyar kaka biyu da za ta karkare karshen Yunin 2029.

    Tsohon ɗan wasan Manchester City ya fara horar da Bayern a cikin watan Mayun 2024, wanda tun farko ƙwantiraginsa zai kare a karshen kakar 2027.

    Mai shekara 39 ya lashe kofin Bundesliga a bara da lashe wasa 49 daga 67 da ya ja ragama a dukkan fafatawa a kakar da ta wuce.

  5. Karawar Champions League ta ranar Talata

    Ga jerin ƙungiyoyin da za su kara a wasannin Champions League na ranar Talata 21 ga watan Oktoban 2025:

    • Barcelona v Olympiakos
    • Kairat v Pafos
    • Arsenal v Atletico Madrid
    • Bayer Leverkusen v Paris St-Germain
    • FC Copenhagen v Borussia Dortmund
    • PSV Eindhoven v Napoli
    • Newcastle v Benfica
    • Union Saint-Gilloise v Inter Milan
    • Villarreal v Man City
  6. Arsenal ta nemi afuwar Atletico kan rashin bai wa ƴanwasanta ruwan wanka

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta nemi afuwar Atletico Madrid bayan an samu matsalar rashin ruwan ɗumi da ƴanwasan Atletico za su watsa bayan yin atisaye a Emirates gabanin komawa masaukinsu na otal a birnin Landan a yammacin Litinin.

    Dokokin hukumar ƙwallon ƙafa ta Turai, Uefa sun bai wa tawagar ƙungiyar da ke baƙunta damar yin atsisaye a filin atisaye na ƙungiya mai masaukin baƙi, kwana ɗaya gabanin kowace karawa.

    Tawagar Atletico ta yi atsisaye ne a filin Arsenal gabanin karawar da za a yi ta gasar Chamiopns League a ranar Talata a Landan.

    Jami’an Atletico Madrid sun sanar da hukumomin Arsenal cewa babu ruwan ɗumi a ɗakin canza kaya da misalin ƙarfe 6:45 na yamma, inda daga baya aka gano cewa matsalar ta shafi hatta ɗakin sauya kaya na ƴanwasan Arsenal.

    Hakan ya sa tawagar Atletico ta hanzarta kammala atisaye da kimanin minti 15 domin komawa masaukinta na otal.

    Jaridar Marca ta Spain ta ruwaito cewa lamarin ya ɓata wa ƴanwasan na Atletico rai.

    Arsenal ta nemi afuwar tawagar Atletico, inda kuma aka gyara famfon ruwan ɗumin da misalin ƙarfe 7:25 na yamma.

    Arsenal ta yi nasara a dukkanin wasa biyu na gasar Champions League da ta buga a wannan kaka ba tare da an zura mata ko da ƙwallo ɗaya ba.

    Ita kuwa Atletico ta sha kashi a hannun Liverpool 3-2 a wasanta na farko, sai dai ta ɗau fansa kan Eintracht Frankfurt da ci 5-1 a wasanta na biyu.

  7. Nottingham Forest za ta bai wa Dyche aikin kociyanta

    Nottingham Forest tana tattaunawa da Sean Dyche, domin ba shi aikin kociyanta

    Dyche ne kan gaba cikin sahun masu zawarcin aikin maye gurbin Ange Postecoglou, kuma ƙungiyar da take buga Premier League na fatan kammala komai ranar Litinin.

    Ranar Asabar aka kori Postecoglou minti 17 tsakani da Chelsea ta je ta doke Forest 3-0 a City Ground a wasan Premier League.

    Yanzu haka Forest tana ta 18 a kasan teburin Premier League, bayan cin wwasa ɗaya daga takwas da ta yi.

    Haka shima Roberto Mancini ya tattauna da mahukuntan Forest kan aikin kociyan ƙungiyar, shima mai horar da Fulham, Marco Silva yana son aikin, amma ba a tuntuɓe shi ba.

  8. Kano Pillars ta dakatar da mai horas da ƴanwasanta

    Hukumar gudanarwar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta sanar da dakatar da masu horas da ƙungiyar bisa jagorancin Ogenyi Evans da mataimakinsa Ahmed Yaro Yaro.

    Hakan na zuwa ne bayan ƙungiyar ta sha kashi a hannun Barau FC a karawar da suka yi ranar Lahadi a gasar Premier ta Najeriya.

    Sanarwar da hukumar gudanarwar ƙungiyar ta fitar ta ce an dakatar da kocin da mataimakinsa ne "sanadiyyar rashin ƙoƙari a gasar Premier ta Najeriya ta 20025/26 da ke gudana."

    Ya zuwa yanzu Pillars ta yi nasara a wasanni biyu ne kacal cikin wasa takwas da ta buga a wannan kaka, inda ta yi rashin nasara a wasa huɗu sannan ta yi canjaras a biyu.

    Sanarwar da ƙungiyar ta fitar ta ce a yanzu an naɗa tsohon kyaftin ɗin ƙungiyar Gambo Muhammad da mai horas da mai tsaron gida Sulaiman Shuaibu a matsayin wadanda za su ja ragamar ƙungiyar na wucin-gadi.

  9. Liverpool ta yi rashin nasara wasa huɗu a jere

    Manchester United ta je ta doke Liverpool 2-1 a wasan mako na takwas a Premier League ranar Lahadi, karon farko da ta yi nasara a Anfield bayan Janairun 2016.

    United ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Bryan Mbeumo, Liverpool ta farke ta hannun Cody Gakpo a zagaye na biyu.

    Daf da za a tashi ne Harry Maguire ya kara na biyu da ya bai wa United maki ukun da take bukata.

    Kuma karon farko da kociya, Ruben Amorim ya ci wasa biyu a jere tun bayan da ya karɓi aikin horar da United a cikin watan Nuwambar 2024.

    Wannan shi ne karon farko da aka doke Liverpool a wasa huɗu a jere a dukkan fafatawa, tun bayan Nuwambar 2014, karkashin Brendan Rodgers.

    Wasannin da aka ci Liverpool a jere ya haɗa da 2-1 a hannun Crystal Palace a Premier League da 1-0 a gidan Galatasaray a Champions League da wanda Chelsea ta yi nasara 2-1 a Stamford Bridge a Premier da kuma na Manchester United da ta ci 2-1 a Anfield a Premier League.

    Da wannan sakamakon Liverpool ta yi kasan teburi zuwa mataki na huɗu da maki 15, ita kuwa United mai maki 13 ta yi sama zuwa mataki na tara.

    Liverpool za ta je gidan Frankfurt a makon gobe a Champions League daga nan ta wuce Brentford a Premier League.

    Ita kuwa United za ta karɓi bakuncin Brighton a wasan mako na tara a babbar gasar tamaula ta Ingila.

  10. Real Madrid ta zayyana sunayen ƴan wasan baya guda uku waɗanda za ta yi ynnƙurin ɗauka a kyauta a bazara mai zuwa, kuma sun haɗa da ɗan wasan Crystal Palace da Ingila Marc Guehi, mai shekara 25, da ɗan wasan baya na Bayern Munich da Faransa Dayot Upamecano, mai shekara 26, da kuma ɗan wasan Liverpool da Faransa Ibrahima Konate mai shekara 26. (Talksport)

    Ana yi wa Chelsea kallon ƙungiyar da ke kan gaba wajen fafutukar siyan ɗan wasan tsakiyar Ingila Morgan Rogers mai shekara 23 daga abokiyar hamayyarta Aston Villa. (CaughtOffside)

    Manchester City da Chelsea da Liverpool da Arsenal duk sun shiga jerin ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗan wasan gaban River Plate ɗan ƙasar Argentina Ian Subiabre mai shekara 18, wanda ake sa ran zai koma gasar Premier shekara mai zuwa. (TBR Football)

    Nottingham Forest ta na nazari kan kocin Fulham Marco Silva da Sean Dyche da Roberto Mancini - a matsayin waɗanda za su iya maye gurbin Ange Postecoglou. (Guardian)

    Ɗan wasan gaban Real Madrid ɗan ƙasar Brazil, Endrick, mai shekara 19, na sha'awar komawa Marseille sakamakon rashin samun gurbin buga wasa a ƙungiyar ta La Liga. (L'Equipe)

  11. Barau FC ta yi nasara a kan Kano Pillars

    Barau FC ta doke Kano Pillars 2-1 a wasan mako na tara a Premier ta Najeriya ranar Lahadi a Sani Abacha ba tare da ƴan kallo ba.

    Pillars ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Rabi'u Ali, haka suka je hutu Pillars na cin 1-0.

    Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Barau ta kara ƙwallo biyu a raga ta hannun Abdulbari Nura da kuma Stanley Oganbor karkashin jagorancin Ladan Bosso.

    Da wannan sakamakon Barau FC ta koma ta 19 da maki 18 da kwantai, ita kuwa Pillars mai kwantai itama da maki takwas tana ta 18.

  12. Ƙungiyar Fabregas, Como ta doke Juventus a Serie A

    Juventus ta yi rashin nasara 2-0 a gidan Como a gasar Serie A ranar Lahadi, kenan tana kara fuskantar kalubale, bayan da ta yi canjaras biyar a jere kafin wannan rashin nasarar.

    Da wannan sakamakon Como ta koma ta biyar a teburin Serie A da maki 12 iri ɗaya da na Juventus ta shida.

    Wannan shi ne karon farko da Como ta yi nasara a kan Juventus tun bayan 1952.

  13. ''Haaland yana da ɗokin ya ci ƙwallaye kamar Ronaldo''

    Ruben Dias ya ce Erling Haaland yana da ɗokin cin ƙwallaye kamar Cristiano Ronaldo.

    Haaalnd ne ya ci wa City ƙwallo 2-0 da ta yi nasara a kan Everton a wasan Premier League ranar Asabar.

    Kenan ɗan wasan Norway ya ci ƙwallo 23 a wasa 13 a bana a dukkan fafatawa.

    Kawo yanzu yana da 11 a raga a Premier League, shi ne kan gaba a wannan ƙwazon, wasa ɗaya ne bai ci ƙwallo ba kawo yanzu a gasar.

    Mai shekara 25 ya zura 138 a raga a wasa 155 a City jimilla, 96 a Premier League daga wasa 105.

  14. Tottenham ta shige gaban Chelsea da Manchester United a fafatukar sayen ɗan wasan gaban Serbia Dusan Vlahovic, mai shekara 25 daga Juventus. (Football Insider).

    Chelsea na iya tayar da batun sake siyan ɗan wasan tsakiyar Belgium Diego Moreira, mai shekara 21, daga Strasbourg. (TBR Football).

    Real Madrid na sa ido kan ɗan wasan tsakiyar Mexico Gilberto Mora, mai shekara 17, wanda ke taka leda a kulob din Tijuana na Mexico. (AS)

  15. Kane ya ci ƙwallo na 400 tsakanin a kaka 14 da wata tara

    Ƙyaftin ɗin tawagar Ingila, Harry Kane ya ci ƙwallo na 400 a wasan da Bayern Munich ta doke Borussia Dortmund 2 - 1 a gasar Bundesliga ranar Asabar.

    Kane ne ya fara cin ƙwallo a wasan da ya bai wa Bayern ci gaba da zama a matakin farko a teburin babbar gasar tamaula ta Jamus.

    Ya ci ƙwallo na 400 ne a shekara 14 da wata tara, bayan da ya zura na farko a ragar Sheffield Wednesday a Janairun 2011 lokacin da yake wasannin aro a Leyton Orient daga Tottenham.

    Mai shekara 32 ya ci ƙwallo 104 a karawa 107 tun bayan da ya koma Bayern Munich daga Tottenham a 2023.

    Ya zura ƙwallo 280 a Tottenham da biyar a Leyton Orient da tara a Milwall da guda biyu a Leicester City.

    Haka kuma Kane ya ci wa Ingila ƙwallo 76 shi ne kan gaba a yawan ci wa kasar ƙwallaye a tarihi.

  16. An tuntuɓi Beckham ya goyi bayan a sayar da Man United

    An tuntuɓi David Beckham, domin ya goyi bayan sayar da Manchester United, in ji wasu rahotanni.

    A raɗe raɗin da ake yi wasu attajirai masu zuba hannun jari daga Haɗadɗiyar Daulal Larabawa ne ke shirye-shiryen sayen hannun jarin da iyalan Glazer suka mallaka.

    Kamar yadda Star da Mirror ta wallafa, attajiran na son Beckham ya zama jakada a lokacin da za a yi cinikin.

    Tsohon ɗan wasan United, wanda yake da hannun jari Inter Miami da Salford, zai iya samun damar mallakar hannun jari a ƙungiyar Old Trafford.

    Beckham wanda ya daɗe yana caccakar iyalan Glazer kan yadda suke gunadar da United ya taɓa bukatar su sayar da ƙungiyar a 2023, ya kuma ce a shirye yake a dama da shi nan gaba a gudanar da ita.

    Sir Jim Ratcliffe mai kamfanin Ineos Group ne ya mallaki hakkin tafiyar da United, bayan da ya mallaki hannun jarin kaso 27.7 a Fabrairun 2024.

    A cikin watan Mayu aka sanar da niyyar mahukuntan United kan gina sabon filin wasan da zai ci ƴan kallo 100,000 kusa da Old Trafford, sai dai ƙungiyar ba ta kokari a wasannin da take bugawa.

  17. Sakamakon wasannin Premier League ranar Asabar

  18. Karo na biyu da aka bai wa Flick jan kati a Barcelona

    Ranar Asabar aka bai wa kociyan Barcelona, Hansi Flick jan kati a wasan mako na takwas a La Liga da suka doke Girona 2-1.

    Kenan kociyan ɗan kasar Jamus ba zai ja ragamar El Clasico ba tsakanin Real Madrid da Barcelona ranar 26 ga watan Oktoba ba.

    Da wannan sakamakon Barcelona ta koma kan teburin La Liga da maki 22 da tazarar ɗaya tsakani da Real Madrid, wadda za ta je Getafe ranar Lahadi.

    Wannan shi ne karo na biyu da aka bai wa Flick jan kati a Barcelona, bayan ranar 7 ga watan Disambar 2024 a karawa da Real Betis.

    Daga nan aka dakatar da shi wasa biyu.

  19. Forest ta kori kociyanta, Postecoglou bayan kwana 39 kan aikin

    Nottingham Forest ta kori kocinta, Ange Postecoglou minti 17 tsakani da ya sha kashi 3-0 a hannun Chelsea a City Ground a wasan Premier League ranar Asabar.

    An sallami ɗan kasar Australia kwana 39 da fara aikin, wanda aka naɗa ranar 9 ga watan Satumba - kenan shine mai horar wa da aka kora a cikin ƙanƙanin kwanaki a tarihin Premier League..

    Wasu rahotannin na cewa Forest ta tuntuɓi tsohon kociyan Everton, Sean Dyche, domin maye gurbin Postecoglou, watakila a bai Roberto Mancini aikin kociyan ƙungiyar.

    Postecoglou ya kasa cin wasa daga takwas da ya ja ragama a dukkan fafatawa da canjaras biyu aka doke shi wasa shida.

    Maki ɗaya Forest ta samu daga wasa biyar a Premier League da Postecoglo ya ja ragama, ya bar ƙungiyar tana mataki na 17 a kasan teburi da tazarar maki ɗaya tsakani da ƴan ukun karshe.

  20. Barcelona ta koma ta daya a teburin La Liga, an bai wa Flick jan kati

    Barcelona ta koma ta ɗaya a teburin La Liga, bayan doke Girona 2-1 ranar Asabar.

    Pedri ne ya fara ci wa Barcelona ƙwallo a karawar da suka yi Estadio Olimpic Lluis Company daga baya Girona ta farke ta hannun Alex Witsel.

    Daf da za a tashi ne Barcelona ta kara na biyu ta hannun mai tsaron baya, Ronald Araulo, hakan ya sa ta haɗa maki ukun da take bukata.

    Sai dai an bai wa Hantsi Flick jan kati, saboda nuna ɓacin rai kan karin minti huɗu da aka yi a fafatawar.

    Kenan ba zai ja ragamar Barcelona wasan hamayya na El Clasico ba da Real Madrid ranar Lahadi 26 ga watan Oktoba.

    Da wannan sakamakon Barcelona, wadda ta buga wasan mako na takwas ta koma ta ɗaya a teburin La Liga da maki 22 da tazarar ɗaya tsakani da Real Madrid mai karawa bakwai.

    Ranar Lahadi Real Madrid za ta ziyarci Getafe a wasan mako na takwasa a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.