Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Laraba 29/10/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Laraba 29/10/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello da Umar Mikail

  1. Mun samu barazanar kai wa majalisar dokokin Najeriya hari - Ɗanmajalisa

    Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilan Najeriya, kan tsaron cikin gida, Garba Muhammad ya bayyana cewa ƴanbindiga sun yi barazar kai wa ginin Majalisar Dokokin ƙasar harin bam.

    Yayin da yake jawabi a wani zaman sauraron ra'ayoyin jama'a kan ƙudurin dokar kafa hukumar tsaron majalisar dokokin ƙasar, ɗanmajalisar ya jaddada buƙatar gaggauta ƙarfafa tsaro a majalisar da ke zama cibiyar dimokuraɗiyyar ƙasar.

    Hon. Garba Muhammad ya ce idan aka kafa hukumar za ta ƙula da tsare-tsaren tsaro da kare sanatoci da ‘yan majalisa da ma’aikata da baƙi.

    Ya ƙara da cewa majalisar na fuskantar ƙalubalen tsaro masu yawa, ciki har da satar motoci da babura da lalata kayayyaki da amfani da katin shaida na ƙarya da kuma shiga harabar majalisar ba tare da izini ba.

    “Mun samu barazanar ƴanbindiga da ke shirin kai harin bam a majalisar dokokin ƙasar, da kuma barazanar wasu masu zanga-zanga da ke son ƙulle majalisar." in ji shi.

    “’Yan majalisa na fuskantar barazana daga wasu al’ummarsu da kuma wasu mutane da ke samun damar shiga ofisoshinsu ba tare da wani tsarin ganawa na hukuma ba.”

    Ya yi gargaɗin cewa idan ba a ɗauki matakan gaggawa don magance irin waɗannan barazanar tsaro ba, hakan na iya haifar da cikas ga ayyukan majalisa, wanda zai iya yin illa ga tafiyar da mulki da kuma tsarin dimokuraɗiyya.

  2. Sabbin hare-haren Isra'ila sun kashe mutum 33 a Gaza

    Jami'an tsaron civil defence a Gaza sun ce akalla mutum 33 ne suka rasa rayukansu a yayin wasu hare-hare da Isra'ila ta kai a sassan yankin inda wasu da dama kuma suka jikkata.

    Hare haren sun faɗa kan gidaje da kuma makarantu.

    Isra'ila ta fara kai hare-hare a 'yan kwanakin nan inda ta ke zargin Hamas da kai wa dakarunta hari da kuma saɓa yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma.

    Wani jami'i a rundunar sojin Isra'ila ya ce Hamas ta kai wa sojojinsu hari a wani yanki da ke ƙarƙashin ikon Isra'ila, yayin da ita ma Hamas ta yi zargi makamancin wannan inda ta ce Isra'ila na kokarin dawo da yaki.

  3. Trump ya isa Koriya ta Kudu don halartar taron ƙasashen Asiya da Pacific

    Donald Trump ya isa Koriya ta Kudu domin bin sahun sauran shugabannin ƙasashen duniya da suka halarci taron bunƙasa tattalin arziki a ƙasashen Asiya da Pacific.

    Ana gudanar da taron ne a birnin Gyeong-ju.

    A gobe Alhamis ne zai gana da takwaransa na China Xi Jinping.

    Yayin da dukkan ƙasashen wato Amurka da China ke buƙatar kauce wa duk wani rikici na kasuwanci a tsakaninsu, ganawar ta su na da muhimmanci ga makomar cinikayya a tsakaninsu.

    Mista Trump ya shaida wa manema labarai cewa ba shi da niyyar neman wa'adin mulki karo na uku yana mai cewa kundin tsarin mulkin ƙasarsa ya bayyana haka kowa ya sani.

  4. Guguwar Melissa ta nausa Cuba bayan mummunar ɓarna a Jamaica

    Guguwar Melissa na ƙara ƙarfi inda yanzu ta nufi Cuba bayan ta yi ɓarna a Jamaica.

    Yanzu guguwar ta ƙara ƙarfi sosai inda cibiyar da ke kula da annobar guguwa ta Amurka ta ce guguwar ta Melissa za ta iya zama babbar annoba musamman a cikin sa'o'i masu zuwa.

    Tuni dai aka kwashe kusan kashi ɗaya bisa uku na mutanen da ke zaune a Cuba.

    Shugaban ƙasar Cuban ya yi gargaɗin cewa ana cikin yanayi na zullumi musamman a cikin dare.

    A Jamaica kuwa har yanzu ana kyautata tsammanin afkuwar mummunar ambaliyar ruwa.

    Filin jirgin saman babban birnin ƙasar zai kasance a rufe har zuwa gobe kafin a buɗe shi jirage su ci gaba da tashi da sauka.

  5. Marabanku

    Masu bin shafin BBC Hausat kai-tsaye, barkanmu da safiyar wannan rana ta Laraba, ta bawa ranar samu kamar yadda Hausawa ke yi mata kirari.

    Abdullahi Bello Diginza da Aisha Babangida ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku halin da duniyar ke ciki.

    Kada ku manta da shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.