Sai da safe
Mun kawo ƙarshen rahotonni a wannan shafi na ranar Laraba.
Muna nan tafe da wasu sababbin rahotonnin gobe da safe.
Kafin lokacin, ku duba ƙasa domin karanta labaran da muka wallafa a yau.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Laraba 29/10/2025
Daga Abdullahi Bello da Umar Mikail
Mun kawo ƙarshen rahotonni a wannan shafi na ranar Laraba.
Muna nan tafe da wasu sababbin rahotonnin gobe da safe.
Kafin lokacin, ku duba ƙasa domin karanta labaran da muka wallafa a yau.

Asalin hoton, EPA
Lauyoyin gwamnati a Brazil sun ce fiye da mutum 130 ne aka kashe a jiya Talata a yayin wani gagrumin samame da jami'an tsaro suka kai wa wasu gungun kungiyoyin asiri.
Kimanin sojoji 2,500 ne suka fafata da kungiyar mai suna Red Command. An dinga jin karar harbe-harbe a birnin Rio de Janaero yayin fafatawar.
Ofishin mai shigar da ƙara na kasar ya ce suna ci gaba da tattaunawa da 'yan'uwa da iyalan wadanda aka kashe domin ɗaukar mataki kan abin da suka kira kisan ba-gaira-ba-dalili.
Sai dai hukumomin Brazil sun ce suna yaki ne da kungiyoyin da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi.

Asalin hoton, ICPC
Wata babbar kotun tarayya a Najeriya ta umarci mayar wa gwamnatin tarayya kuɗi dala 49,700 da aka karɓe daga hannun Nura Ali, wani tsohon kwamashinan hukumar zaɓe a jihar Sokoto.
Mai Shari'a Emeka Nwite ya bayar da umarnin ne bayan wani ƙorafi da hukumar yaƙi da cin hanci ta Independent Corrupt Practices and Other Related Offences Commission (ICPC). ta shigar.
Lauyan ICPC ya faɗa wa kotun cewa sun bi umarnin kotu ne domin karɓe kuɗin, kuma hukumar ta wallafa a shafin jarida tana neman a kawo hujjar da za ta hana a ƙwace kuɗin domin mayar wa gwamnatin tarayya, amma babu wanda ya nuna sha'awar kawo hujjar.
Nura Ali ya yi aiki a matsayin kwamashina ko kuma babban wakilin hukumar zaɓe a jihar Sokoto da ke arewacin ƙasar yayin babban zaɓen 2023.
A watan Disamban 2024 ne kotun ta bayar da umarnin karɓe kuɗin na ɗan lokaci bayan jami'an 'yansanda na DSS sun ƙwace kuɗin daga gidan mutumin.
Hukumomi a Haiti sun ce fiye da mutum uku suka rasa rayukansu sakamkon ambaliya da guguwar Hurricane Melisa ta haddasa.
Akalla yara 10 sun mutu a kudancin kasar bayan da kogin Laa Digue ya yi ambaliya a gidajen jama'a.
Magajin birnin Peti-Guwab ya ce galibin jama'a sun makale cikin buraguzan gine-ginen da suka ruguje.
Guguwar ta yi ɓarna a kasashen da ta ratsa ciki har da Jamaica inda hukumomi suka ce ambaliya da ruwan sama mai cike da isaka sun haddasa gagarumar barna ciki har da katsewar turakun lantarki.
A Cuba ma an kwashe dubban mutane daga wuraren da aka yi hasashen guguwar ta Melissa ke shirin afkawa.
Hafsoshin tsaron Najeriya na ganawa da wani kwamatin majalisar wakilai domin tantance su.
Rahotonni na cewa ana ganawar ce a asirce, ba kamar yadda 'yanmajalisar dattawa suka yi ba - kodayake su ma sun gana a sirrance bayan tattaunawar fili.
Kwamatin tsaro ƙarƙashin jagorancin Babajimi Benson ne ke jagorantar ganawar, kuma ana sa ran za su bi sawun majalisar dattawa wajen amincewa da naɗin nasu.

Asalin hoton, Nigerian Army
A yau Laraba ne Majalisar Dattawan Najeriya ta tantance tare da amincewa da sababbin hafsoshin rundunar sojan ƙasar da Shugaba Tinubu ya naɗa.
Rundunar sojan ƙasa tya wallafa hotunan shugabanta Manjo Janar Waidi Shaaibu tare da sauran shugabannin lokacin da suke gaban majalisar.
Bayan amsa tambayoyi, 'yanmajalisar sun shiga zaman sirri tare da hafsoshin tsaron ba tare da 'yanjarida ba, kafin daga baya su amince da naɗin nasu.

Asalin hoton, Nigerian Army

Asalin hoton, Nigerian Army

Asalin hoton, Nigerian Army
Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da sababbin hafsoshin tsaro da Shugaba Tinubu ya naɗa ranar Juma'a da ta gabata.
Majalisar ta amince da Laftanar Janar Olufemi Oluyede a matsayin babban hafsan tsaro, da Manjo Janar Waidi Shaibu a matsayin hafsan sojan ƙasa, da Rear Admiral Idi Abbas hafsan sojan ruwa, da kuma Air Marshall Kennedy Aneke hafsan sojan sama.
Yayin tantance su a yau Laraba, shugabannin sojan sun amsa 'yan tambayoyi daga 'yanmajalisar bayan gabatar da kan su da tarihin ayyukan da suka gudanar kafin naɗin nasu.

Asalin hoton, Getty Images
Ma’aikatar tsaro ta ƙasar Romania ta bayyana cewa Amurka na shirin rage yawan sojojinta da ke cikin ƙasashen da ke yankin gabashi na ƙungiyar tsaro ta Nato..
A cewar ma’aikatar, sojojin Amurka 900 zuwa 1,000 ne za su ci gaba da zama a Romania daga cikin sojoji 1,700 da ke kasar a halin yanzu.
Ministan Tsaron Romania Ionut Mosteanu ya ce matakin na zuwa ne sakamakon sabon tsarin gwamnatin Shugaba Trump, inda Amurka ke mayar da hankali kan yankin Indo-Pacific.
Ya ce takwaransa na Amurka Pete Hegseth ya shaida wa ƙasashen Turai cewa lokaci ya yi da za su fi mayar da hankali kan tsaron kansu, yayin da Amurka ke sauya manufarta daga Turai zuwa Indo-Pacific.
Mosteanu ya ƙara da cewa wata rundunar Amurka da ke sansanin jirgin sama na Mihai Kogalniceanu – wanda ake shirin zama sansanin Nato mafi girma a Turai – za ta bar Romania ba tare da maye gurbinta ba.

Asalin hoton, Kano state house
Majalisar dokokin jihar Kano ta yi kira ga dukkan wakilai daga arewacin Najeriya su ɗauki matakin gaggawa don ganin an soke ɗaukar aikin kwastam da aka yi a kwanan nan.
A yayin zaman majalisar ƙarƙashin jagorancin Kakakin majalisar, Rt. Hon. Jibril Ismail Falgore, ’yan majalisar sun nuna ɓacin rai kan yadda aka gudanar da aikin ɗaukar ma’aikatan, suna kiran shi da cike da son kai da rashin adalci.
Majalisar ta ce "Duk da yawan al’ummar Arewacin Najeriya, an nuna bambanci mai yawa wanda ya saɓa wa ƙa’idojin hukumar rabon muƙamai ta ƙasa."
Shugaban masu rinjaye a majalisar, Hon. Lawal Hussain Dala, wanda ya gabatar da ƙudurin, ya ce "Tsarin bai kasance mai gaskiya ba, kuma akwai rashin daidaito da rarrabuwar kawuna da nuna bambanci."
Ya ce "Lissafin da aka fitar ya nuna fifiko ga yankin kudu musamman yankin kudu maso yamma, abin da ta bayyana da abin takaici da haɗari ga haɗin kan ƙasa."
Rahotanni sun nuna cewa daga cikin sabbin jami’an kwastam 1,785 da aka ɗauka, fiye da 1,000 daga cikinsu sun fito ne daga yankin Kudu, yayin da yankin arewa bai samu fiye da mutum 540 ba.
Majalisar Kano ta zargi hukumar kwastam da nuna fifiko ga yanki ɗaya kawai da nuna rashin gaskiya da nuna wariya.
A yayin da yake jagorantar zaman, Falgore, ya buƙaci wakilan arewa a majalisar tarayya da su sa baki don dakatar da wannan ɗaukar aikin.
Ya kuma yi kira ga shugaban ƙasa da ya soke jerin sunan ma'aikatan gaba ɗaya saboda rashin daidaitonsa.

Asalin hoton, Reuters
Ƴan sanda a ƙasar Tanzania sun saka dokar hana fita a fadin ƙasar bayan zanga-zangar da ta ɓarke yayin zaɓen shugaban ƙasa da ya rikiɗe zuwa tashin hankali a wasu sassa daban-daban na ƙasar.
Rahotanni sun nuna cewa, zanga-zangar ta ɓarke ne musamman a birnin Dar es Salaam da wasu garuruwa yayin da jama’a ke nuna rashin jin daɗi kan yadda ake gudanar da zaɓen shugaban ƙasar.
Masu zanga-zangar sun yi zargin cewa akwai son kai da rashin gaskiya a tsarin zaɓen, tare da neman gwamnati ta gyara tsarin zaɓe da kuma ba kowa damar faɗar albarkacin baki.
A cewar jami’an tsaro, an sanya dokar ne domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Sai dai wasu ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam sun bayyana damuwa cewa wannan mataki na iya ƙara takura ’yancin jama’a musamman a lokacin da ake jiran sakamakon zaɓen shugaban ƙasa.

Zanga-zanga ta ɓarke a wasu sassan birnin kasuwanci na Dar es Salaam yayin da jama’a ke kaɗa ƙuri’unsu a zaɓen shugaban ƙasar Tanzaniya.
Masu zanga-zangar sun taru a kan manyan tituna suna neman a sake fasalin tsarin zaɓe tare da nuna ɓacin rai kan abin da suka kira son kai da fifita jam’iyya mai mulki.
Mutane da dama sun jikkata ta sanadiyyar zanga-zangar yayin da ƴan sanda suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar.
Masu zanga-zangar sun kuma zargi gwamnati da cin zarafi da amfani da iko fiye da kima da tsoratar da masu fafutuka da danne ’yancin faɗar albarkacin baki, da kuma tsadar rayuwa a matsayin manyan dalilan fushinsu.

Asalin hoton, Reuters
Ma’aikatar lafiyar Gaza da ke ƙarƙashin Hamas ta ce aƙalla mutum 104 ne suka mutu sakamakon hare-haren Isra’ila da aka kai a daren Talata.
Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta kai hare-haren ne kan “manyan wuraren ta’addanci da ’yan ta’adda” a matsayin martani ga keta yarjejeniyar tsagaita wuta da Hamas ta yi, wacce Amurka ta shiga tsakani wajen cimmawa.
Ministan tsaron Isra’ila ya zargi Hamas da kai hari a Gaza wanda ya kashe wani sojin Isra’ila da kuma karya sharuɗɗan yarjejeniyar da ta shafi dawo da gawarwakin fursunonin da suka mutu.
Sai dai Hamas ta musanta wannan zargi, tana mai cewa ba ta da hannu a harin, kuma tana bin yarjejeniyar tsagaita wuta.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce “babu abin da zai kawo cikas” ga yarjejeniyar, amma ya ƙara da cewa Isra’ila na da ’yancin “ramawa” idan sojojinta aka kai wa hari.
Hare-haren sun auka kan gidaje da makarantu a birnin Gaza da Beit Lahia a arewa, da kuma a yankunan Bureij, Nuseirat da Khan Younis a tsakiyar da kudancin Gaza.
Rahotanni sun nuna cewa cikin waɗanda suka mutu akwai yara 46 da mata 20, yayin da sama da mutane 250 suka jikkata.

Asalin hoton, Getty Images
Cibiyar bin diddigi kan cin zarafi ta lalata a Katsina SARC ta ce tun kafuwarta a watan Disamba 2023, ta samu korafe-korafe 110 na cin zarafi ta hanayar lalata kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Daga cikin wadannan, 60 ne aka saka a cikin tsarin tattara bayanan yara ta CPIMS.
Babban sakataren ma’aikatar Ilimin yara mata da cigaban yara, mista Aminu Badaru-Jikamshi, ya bayyana hakan ne a wajen buɗe wani horon kwanaki uku da aka gudanar a Katsina ranar Talata.
Horon, wanda UNICEF ta taimaka wajen shirya shi, ya samu halartar masu ruwa da tsaki daga jihohin Jigawa da Kano da Katsina, ciki har da ma’aikatan lafiya da jami’an shari’a da ‘yan sanda da ma’aikatan jin kai da jami’an yaƙi da cin zarafin mata da wakilan ma’aikatar harkokin mata, da kuma ma’aikatan SARC.
Badaru-Jikamshi ya ce, “Manufar horon shine karfafa bin diddigi da samun tallafi ga wadanda suka fuskanci cin zarafi, ta hanyar mayar da hankali kan yara da wadanda abin ya shafa.”
Ya kara da cewa, "Muna kuma duba yiwuwar ziyartar wasu jihohi da suka riga suka kafa cibiyar SARC domin ƙara horar da su kan irin waɗannan lammuran."

Asalin hoton, Getty Images
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana cewa tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan ya ƙi cire tallafin man fetur ne a shekarar 2011 saboda matsalar tsaro da Boko Haram ke haifarwa a lokacin.
Sarki Sanusi, wanda ya riƙe muƙamin gwamnan Babban Bankin Najeriya daga 2009 zuwa 2014, ya bayyana hakan ne a taron Oxford Global Think Tank Leadership da aka gudanar a Abuja ranar Talata.
Ya ce babban dalilin da yasa gwamnati ta sassauta niyyarta na cire tallafin gaba ɗaya shi ne Boko Haram.
“A lokacin, akwai dubban ‘yan Najeriya a titunan Lagos da Kano da Kaduna da sauran birane sabodsa haka akwai fargabar cewa wasu daga cikin masu kai hare-haren ka iya amfani da wannan dama su kai harin bam wanda zai yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.” in ji shi.
Sanusi ya ce Shugaba Jonathan a lokacin ya dage kan cire tallafin man fetur, amma daga bisani ya fasa saboda jefa rayukan ‘yan Najeriya cikin haɗari.
“Idan da a ce a an cire tallafin mai a 2011, tabbas za a ji raɗaɗin yin hakan, amma radadin zai kasance ƙaramin kaso ne idan aka kwatanta da abin da muke fuskanta a yau."
Ya jaddada cewa da a ce an aiwatar da matakin cire tallafin man fatur a lokacin Jonathan. da Najeriya ba za ta kasance tana fuskantar hauhawar farashin kayayyaki sama da kashi 30 cikin 100 ba a yau.
Sarkin ya kuma ƙara da cewa Babban Bankin Najeriya ya riga ya yi lissafin illar matakin a lokacin.

Asalin hoton, STATE HOUSE
Majalisar dattijan Najeriya na aikin tantance manyan hafsoshin sojin ƙasar waɗanda shugaban ƙasar Bola Tinubu ya zaɓo domin jan ragamar ɓangaren tsaro na ƙasar.
Manyan hafsohin sojin sun isa harabar majalisar da misalin ƙarfe 10 zuwa 11 na safe.
Da farko majalisar ta bayyana cewa za ta gudanar da tantancewar ne a mako mai zuwa, sai dai daga baya ta yanke shawarar matso da tantancewar zuwa yau Laraba
Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, a ranar Talata, ya ce akwai buƙatar gaggauta tantance shugabannin tsaron domin ba su damar ci gaba da gudanar da ayyukansu.
A ranar 24 ga watan Oktoba ne Shugaba Tinubu ya gudanar da sauye-sauye a jagorancin ɓangaren tsaro na ƙasar, inda aka sauya hafsan hafson ƙasar Christopher Musa da Laftanar-Janar Olufemi Olatubosun Oluyede.
Haka nan shugaban ya naɗa Manjo-janar Waidi Shaibu a matsayin hafsan sojojin ƙasa, da Air Vice Marshall S.K. Anekea matsayin hafsan sojin sama sai kuma Rear Admiral Idi Abbas a matsayin hafsan sojojin ruwa.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi a yankin karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina sun tabbatar da cewa ƴan bindiga sun hallaka mutum biyu tare da yin garkuwa da wasu mutum 15 a wasu garuruwa wajen shida da ke yankin.
Wannan na faruwa ne duk da cewa an cimma yarjejeniyar sasanci da wasu daga cikin ƴan bindigar, abin da ya sa jama’ar yankin ke cewa suna cikin zaman ɗar-ɗar.
Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa hare-haren sun zama tamkar ruwan dare, inda ƴan bindigar ke shiga ƙauyuka suna kashe mutane da sace dukiya ba tare da tsoro ba.
Wani mazaunin yankin ya ce, "Babu ranar da waɗannan ƴan bindigar ba su zuwa suna shiga ƙauyuka suna yin ta’addanci kamar yadda suka ga dama."
"Rana ta ƙarshe da suka kai mana hari ita ce jiya da dare, inda suka kashe mutum wajen biyar zuwa shida." Ya ƙara da cewa fiye da mutum 40 sun tsere daga gidajensu bayan harin.
Ya ƙara da cewa jami’an tsaro sun san da lamarin, amma babu wani mataki mai ƙarfi da aka ɗauka domin daƙile hare-haren
"Abin ya riga ya yi yawa, babu abin da jami’an tsaro za su iya yi. Ƴan bindigar da muke sulhu da su ne ke ci gaba da kai mana hari," in ji shi.
Rahotanni sun nuna cewa mazauna garuruwan da abin ya shafa sun tsere zuwa garin Dutsen Rimi da kuma hedikwatar karamar hukumar mulki ta Bakori domin neman mafaka.
Haka kuma, wata mata daga garin Layin Ajiya ta tabbatar da cewa sun tsere daga gidajensu saboda tsananin hare-haren da suka ki ƙarewa.
"Yanzu haka mun tsere zuwa Dutsen Rimi, babu kwanciyar hankali kuma ba mu da tabbacin komawa gida," in ji ta
A nasa ɓangaren, shugaban ƙaramar hukumar Bakori, Abubakar Musa Barde, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an tattauna da waɗanda aka yi sasanci da su, amma sun musanta hannu a harin.
"Mun yi magana da su, sun tabbatar da cewa ba su ne suka kai harin ba. Amma har yanzu babu wanda ya fito fili ya ɗauki alhakin kai hare-haren," in ji shugaban ƙaramar hukumar.

Asalin hoton, Samia Suluhu Hassan/X
Shugabar ƙasar Tanzania, Samia Suluhu Hassan ta kaɗa ƙuri’a a zaɓen shugaban ƙasar.
Zaɓen na gudana ne a duk fadin kasar, ciki har da yankin Zanzibar, inda fiye da miliyoyin masu rajista 37.7 ke sa ran kaɗa ƙuri’a.
Shugabar ƙasar na cikin jerin mata uku da ke fafatawa a zaɓen shugaban ƙasar, inda suke gwagwarmaya da sauran ’yan takara 14 daga sassa daban-daban na ƙasar.
Shugabar, wadda ke cikin jam’iyyar CCM, na neman ci gaba da shugabanci bayan karbar ragamar mulki a zaɓen da ya gabata.
Zaɓen ya gudana ne a yayin da wasu jam’iyyun adawa suka nuna rashin jituwa kan shiga zaɓen.

Asalin hoton, Samia Suluhu Hassan/X

Asalin hoton, Samia Suluhu Hassan/X

Asalin hoton, Samia Suluhu Hassan/X

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan takarar jam’iyyar adawa a Kamaru, Issa Tchiroma Bakary, zai gurfana a gaban kotu saboda bayyana kansa da yayi a matsayin wanda ya lashe zaɓe ba tare da izini ba, da kuma shirya zanga-zanga “ba bisa ka’ida ba” wacce ta haifar da asarar rayuka.
Ministan harkokin cikin gida na Kamaru, Paul Atanga Nji, ne ya bayyana hakan a wata taron manema labarai a babban birnin Yaoundé inda ya yi bayani kan girman tasiri da illolin zanga-zangar nuna adawa da sakamakon zaɓen da aka gudanar a ƙasar.
Ya ce masu zanga-zangar, a karkashin tasirin miyagun ƙwayoyi, sun mayar da martani ga kiran da Tchiroma Bakary ya yi na su ci gaba da zanga-zanga wanda ya haddasa ruɗani a birane da dama, ciki har da lalata gine-ginen gwamnati da tashoshin mai, da shaguna.
Ministan ya tabbatar cewa, “Za a gurfanar da Issa Tchiroma a gaban kotu.”
Har yanzu dai Tchiroma bai mayar da martani kan hukuncin gwamnati ba.
A wata hira da Tchiroma yayi da BBC kwanaki kafin sanar da sakamakon zabe, ya bayyana cewa ba ya jin tsoron a kama shi.
Ministan ya kuma ce an kaddamar da bincike domin gano abubuwan da suka faru kafin da bayan Shugaba Paul Biya ya bayyana a matsayin wanda ya lashe zaɓe da kaso 53.7 cikin 100.
Duk da cewa Ministan ya tabbatar da cewa an shawo kan lamarin, masu zanga-zangar suna ci gaba da fitowa a wasu wurare, musamman a Douala da Garoua, inda suka kafa shinge a kan tituna kuma suka ƙone tayoyi a kan hanyoyi.

Asalin hoton, Getty Images
Masu bincike a jami'ar Yale sun ce akwai shaidar da ke nuna cewa an yi wa fararen hula kisan gilla a birnin El-Fasher da ke yankin Darfur na ƙasar Sudan.
Shugaban sashen bincike a jami'ar Nathaniel Raymond, ya shaida wa BBC cewa wasu hotunan tauraron ɗan adam sun nuna yadda jinin mutane ya fallatsa da jikin wasu abubuwa da dama a kan hanya da ma bangon gine-ginen da ke wajen birnin inda rahotanni suka ce an kashe mutane da dama a yankunan.
Wasu bidiyo da aka sanya a intanet sun nuna yadda mayaƙan RSF din ke murnar kashe fararen hula.
Natahiel Raymond ya kuma shaida wa BBC cewa wasu majiyoyi daga El Fasher sun ce akwai yiwuwar an kashe fararen hula fiye da dubu 10 tun bayan da aka kwace iko da birnin.

An fara kaɗa kuri’a a ƙasar Tanzania, inda ake sa ran ’yan ƙasar miliyan 37.7 da aka yi wa rajista za su fito domin zaɓen shugaban ƙasar.
An buɗe fiye da rumfunan zaɓe 99,000 a fadin ƙasar da ya haɗa daga babban yankin ƙasar zuwa tsibirin Zanzibar.
Zaɓen ya zo ne a dai-dai lokacin da aka samu rarrabuwar kawuna tsakanin jam’iyyun adawa kan ko za su shiga zaɓen.

Babbar jam’iyyar adawa ta Chadema ta ƙaurace wa zaɓen, tana neman a gudanar da gyare-gyaren tsarin zaɓe tare da zargin cewa tsarin na fifita jam’iyya mai mulki.
Haka kuma, an hana ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ACT-Wazalendo, Luhaga Mpina, wanda tsohon mamba ne na jam’iyyar CCM tsayawa takara saboda wasu ƙalubalen shari’a.
An buɗe rumfunan zaɓe da misalin ƙarfe 7:00 na safe agogon cikin gida, kuma za su rufe da ƙarfe 4:00 na yamma.

’Yan takara 17 ne ke neman kujerar shugaban ƙasar, ciki har da Shugabar ƙasa mai ci, Samia Suluhu Hassan na jam’iyyar CCM mai mulki.
Hukumar zaɓen ƙasar ta bayyana cewa za a sanar da sakamakon zaɓe cikin sa’o’i 72 bayan kammala kaɗa kuri’a.
Ƴan Tanzaniya dai za su zaɓi Shugaban ƙasa da ƴan majalisar dokoki da kansiloli na ƙananan hukumomi.
Wannan shi ne zaɓe na bakwai da ƙasar ke gudanarwa tun bayan komawarta tsarin dimokuraɗiyya mai jam’iyyu da dama a shekara ta 1992.
