Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 13/01/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 13 ga watan Janairun 2026.

Taƙaitattu

  • Trump ya faɗa wa ƴan Iran su ci gaba da zanga-zanga
  • An fara binciken mutuwar matar da aka manta almakashi a cikinta a Kano
  • Amurka ta kai wa Najeriya tallafin 'kayan aikin soji'
  • An kashe fiye da ƴanbindiga 200 a jihar Kogi
  • Yara 100 sun mutu a Gaza tun bayan tsagaita wuta - MDD
  • 'Akwai ƴan gudun hijira 21,000 da ba a yi wa rajista ba a Najeriya'
  • Latsa nan domin shiga zaurenmu na Whattsapp
  • An bai wa Trump shawara kan matakan da zai iya ɗauka kan Iran, ciki har da na soji
  • Trump ya yi barazanar ƙarin haraji kan ƙasashen da ke kasuwanci da Iran
  • Nijar ta soke lasisin motocin da suka ƙi kai wa Mali man fetur
  • Jihohin Najeriya biyar da aka fi kashe mutane a 2025 - Rahoto

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida, Haruna Kakangi, Abdullahi Bello Diginza da Ahmad Bawage

  1. An bai wa Trump shawara kan matakan da zai iya ɗauka kan Iran, ciki har da na soji

    An bai wa Shugaban Amurka Donald Trump shawarwari kan matakai daban-daban da zai iya ɗauka kan Iran, ciki har da na soji da kuma waɗanda zai iya ɗauka ta ƙarƙashin ƙasa, kamar yadda wasu jami’an ma’aikatar tsaron Amurka biyu suka shaida wa kafar yaɗa labarai ta CBS, abokiyar hulɗar BBC a Amurka.

    Jami’an Pentagon sun ce har yanzu ana la’akari da yiwuwar kai hare-haren makamai masu linzami daga nesa idan Amurka za ta tsoma baki, amma an kuma gabatar wa Trump wasu matakan na daban da suka haɗa da kutse ta shafukan intanet da kuma dabarun sauya tunanin ƴan ƙasar ta Iran.

    A ranar Litinin Trump ya sanar da sanya harajin kashi 25 cikin 100 kan ƙasashen da ke kasuwanci da Iran.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama ke cewa fiye da masu zanga-zanga 600 ne aka kashe cikin makonni uku na zanga-zangar adawa da gwamnati a Iran.

    Ministan harkokin wajen Iran ya ce Tehran a shirye take domin tattaunawa da Amurka, amma ya jaddada cewa ƙasar “a shirye take da yaƙi” idan aka tilasta mata.

    Ana sa ran ƙungiyar tsaron ƙasa ta Trump za ta gudanar da taro a Fadar White House a yau Talata domin tattauna matakan da za a iya ɗauka waɗanda suka shafi Iran, sai dai har yanzu ba a tabbatar ko shugaban ƙasar da kansa zai halarci taron ba.

    A baya Trump ya ce sojojin Amurka na duba “matakai masu tsauri ƙwarai” na tsoma baki idan aka ci gaba da kashe masu zanga-zanga a Iran.

  2. Trump ya yi barazanar ƙarin haraji kan ƙasashen da ke kasuwanci da Iran

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce duk wata ƙasa da take harkar kasuwanci da Iran za ta fuskanci ƙarin haraji na kashi 25 cikin 100 a kasuwancinta da Amurka.

    Sanarwar da ya yi a shafinsa na sada zumunta, ita ce mataki na farko na zahiri da ya ɗauka a matsayin martani kan yadda hukumomin Iran ke kokarin murƙushe zanga-zngar da ake yi a kasar.

    A iya cewa a taƙaice wannan abu ne mai sarkakiya, domin China ce babbar mai sayen man Iran - kuma daman akwai dambarwar haraji tsakanin Amurka da China.

    Nan gaba a yau Talata ne ake sa ran Trump din zai gana da manyan masu ba shi shawara, domin duba wasu hanyoyin martanin da suka hada da matakin soji.

    Ita dai Iran na gargadi ga Amurka da kada ta kuskura ta shiga lamarin - da cewa a shirye take da yaki - yayin da kuma a daya bangaren take neman a tattauna.

  3. Jihohin Najeriya biyar da aka fi kashe mutane a 2025 - Rahoto

    Matsalar tsaro na daga cikin abubuwan da suka fi ci wa Najeriya tuwo a ƙwarya, inda matsaloli da dama masu alaƙa da tsaro ke ci ga da yi wa ƙasar katutu.

    Matsalolin tsaron da ƙasar ke fuskanta sun haɗa da hare-haren masu iƙirarin jihadi da ƴanbindiga ko ƴanfashin daji masu satar mutane domin neman kudin fansa da rikicin manoma da makiyaya.

    Kamfanin Beacon Security and Intelligence Limited, mai nazari kan al'amuran tsaro a Najeriya da ƙasashen yankin Sahel ya ce an samu raguwar matsalar tsaron a shekarar da ta gabata idan aka kwatanta da 2024.

    Cikin rahotonsa na shekara-shekara da yake fitarwa, Beacon Security ya ce an samu ragi na mutanen da hare-haren ƴanbindiga suka kashe da waɗanda aka sace idan aka kwatanta da 2024.

  4. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Talata

    Kamar kullum, yau ma za mu kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida da Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.