Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 10/09/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 10/09/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Ahmad Bawage

  1. Wane ne ya yi nasara tsakanin Harris da Trump a muhawara?

  2. Bankwana

    Ƙarshen rahotannin shafin kai tsaye na BBC Hausa kenan a yau Talata.

    Sai kuma Laraba za mu sake kawo mu ku wasu sabbin rahotannin.

  3. Likitoci masu neman ƙwarewa a Indiya na ci gaba da yajin aiki duk da gargaɗin kotu

    Likitoci masu neman ƙwarewa a birnin Kolkata da ke gabashin Indiya na ci gaba da yajin aiki duk da cikar wa'adin da kotun ƙolin ƙasar ta ba su na su koma bakin aiki.

    Likitoci kusan 7,000 suka shiga yajin aikin, inda suke neman a yi wa abokiyar aikinsu adalci wadda aka kashe bayan yi mata fyaɗe a babban asibitin koyarwa na birnin.

    Suna kuma neman wasu daga cikin manyan jami'an lafiya na yankin da su sauka daga muƙamansu.

    A lokacin da suka gudanar da zanga-zangar, likitocin sun ce za su duba yiyuwar janye yajin aikin ne kaɗai idan aka biya musu buƙatunsu.

  4. Amurka ta zargi Iran da taimakawa Rasha da makamai

    Sakataren harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken, ya zargi Iran da samar da makamai masu linzami masu gajeren zango ga Rasha - kuma ya yi gargadin cewa za a yi amfani da su a kan Ukraine nan da makonni masu zuwa.

    Da yake magana a wata ziyara da ya kai birnin Landan, ya bayyana matakin a matsayin yunƙurin rura wutar tashin hankali -- kuma ya ce Iran za ta fuskanci sabbin takunkumai sakamakon wannan matakin.

    Birtaniya da Jamus da Faransa sun ba da sanarwar cewa su ma za su ɗauki mataki makamancin haka a kan Iran inda suka bi sahun Amurka wajen kiran lamarin a matsayin barazana ga tsaron Turai.

    Tuni dai Iran ta baiwa Rasha jiragen yaƙi marasa matuka da ake amfani da su wajen kai hari a garuruwan Ukraine.

    Iran dai ta ƙaryata cewa ta aika da makamai masu linzami.

  5. Sama da mutum 26 sun mutu bayan kifewar jirgin ruwa a Senegal

    Aƙalla mutane 26 ne suka mutu bayan da wani jirgin ruwa dauke da bakin haure ya kife a gaɓar tekun Senegal.

    Hukumomi sun ce sama da mutane ɗari ne ke cikin jirgin ruwan kamun kifin a lokacin da ya nutse bayan ya yi tafiyar kilomita huɗu kacal.

    An ceto mutane huɗu kuma ana ci gaba da gudanar da aikin ceto domin lalubo waɗanda suka yi ɓatan dabo.

    Jirgin ruwan ya taso ne daga Mbour mai tazarar kilomita 80 kudu da Dakar babban birnin ƙasar, inda ya nufi tsibirin Canary na ƙasar Sifaniya da ke gaɓar tekun yammacin Afirka.

    Ƙasar Senegal na ganin ƙaruwar jiragen ruwa ɗauke da ƴan ci-rani da ke ƙoƙarin ƙetarawa zuwa tsibirin Canary na ƙasar Sifaniya, inda aka samu baƙin haure kusan dubu talatin da suka yi wannan balaguron a bana..

  6. Gwamnatin jihar Katsina ta tura ɗalibai karatu ƙasar China

    Gwamnatin jihar Katsina a arewacin Najeriya ta mika takardun shaidar fara karatu ga ɗalibai 68 da za su nufi ƙasar China domin karatu a ɓangarorin ilimi da suka haɗa da ƙrƙirarriyar basira ta AI.

    Da yake jawabi a bikin salllamar ɗaliban da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar, Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa an zaɓi daliban ne bisa cancanta daga makarantun sakandare na gwamnati.

    An zaɓo ɗalibai biyu-biyu daga kowace ƙaramar hukumar jihar, a cewarsa.

    Gwamnatin jihar dai ta sha alwashin ɗaukar nauyin duk wani ɓangare na karatun daliban har zuwa ƙarshen karatun nasu.

    Wannan ne kashi na biyu na ɗaliban Katsina da za su fita karatu ƙasashen waje bayan kashi na farko su 41 sun tafi Masar.

  7. Zan wanke kaina a gaban Majalisar Wakilan Najeriya - Farfesa Armayau

    Shugaban Jami'ar Tarayya ta Dutsin-Ma da ke jihar Katsina a Najeriya ya ce zai amsa gayyatar da majalisar wakilan ƙasar ta yi masa bayan wani ma'aikacin jami'ar ya kai ƙararsa gabanta.

    Kazalika, Farfesa Armayau Hamisu Bichi ya musanta zargin "rashin iya jagoranci" da mutumin mai suna Shehu Abubakar Tadda ya zarge shi, yana mai cewa ba shi ne ya kore shi daga aiki ba.

    "Majalisar zartarwa ta jami'a ta kore shi daga aiki ne bayan wani kwamati ya gayyace shi ya je ya kare kansa kan wani rubutu da ya yi inda a ciki ya zagi ministan ilimi, shi kuma ya ƙi zuwa," kamar yadda farfesan ya shaida wa BBC.

    "Sai shi kuma yake yawo yana cewa ni ne na kore shi daga aiki. Ni ban isa na kori kowa daga aiki ba. Ɗauka da kora daga aiki aikin majalisar jami'a ne, amma zan je majalisa [ta wakilai] domin na yi musu bayani."

    Wani kwamatin majalisar wakilai ya buƙaci shugaban jami'ar ya bayyana a gabansa ranar Laraba, 18 ga watan Satumban 2024. Majalisar ta kuma buƙaci wanda ya shigar da korafin ya bayyana gabanta.

    Majalisar wakilan ta ce sashe na 88 da 89 na kundin mulkin Najeriya ne suka ba ta damar gudanar da bincike kan batutuwa da suka shafi al'ummar ƙasar.

  8. Ambaliya ta kashe mutum 24 a jihar Bauchi

    Majalisar zartarwa ta jihar Bauchi ta tabbatar da cewa kawo yanzu mutane 24 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da ake ci gaba da yi a ƙananan hukumomi 16 na jihar.

    An kuma samu rahotannin asarar dukiya da ta kai sama da naira biliyan 22.

    Majalisar ta bayyana cewa ta kafa wani kwamiti domin tantance irin ɓarnar da bala’in ya janyo.

    Da take magana da manema labarai bayan taron majalisar, kwamishinar kula da ayyukan jin ƙai da kula da bala’o’i, Hajara Wanka, ta bayyana cewa ma’aikatar na ci gaba da tattara rahotonta kan ɓarnar da ambaliyar ta yi.

    Ta ce, “Daga rahotonnin da aka tattara, ya zuwa yanzu mutum 24 sun rasa rayukansu, 163 kuma sun samu raunuka, a kananan hukumomi 16.''

    Ta ƙara da cewa ambaliyar ta shafi mutane 122,330 da dabbobi 11,183 inda gidaje 52,000 suka ruguje. Ta kuma datse manyan tituna 12, tare da lalata turakun wutar lantarki 178.

    Kwamishinar ta kuma tabbatar da cewa majalisar ta amince da sakin kuɗaɗe don gyara gine-ginen da suka lalace, da suka haɗa da magudanan ruwa da tituna da kuma makarantu.

  9. Isra'ila ta ce mai yiwuwa dakarunta ne suka kashe ƴar Turkiyya a Falasɗinu

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce akwai yiyuwar sojojinta ne suka harbe matashiya ƴar asalin ƙasar Turkiyya a wata zanga-zanga a gaɓar yamma da kogin Jordan da ta mamaye a makon da ya gabata.

    Aysenur Ezgi Eygi, mai shekaru 26, tana zanga-zanga ne a garin Beita, kusa da Nablus, don nuna adawa da faɗaɗa matsugunan Yahudawa a ranar 6 ga Satumba.

    Shaidu da jami'an Falasdinawa sun ce sojojin Isra'ila ne suka harbe ta, lamarin da ya sa rundunar sojin Isra'ila ta gudanar da bincike.

    Sakamakon binciken da suka fitar a ranar Talata ya kammala da cewa "akwai da yuwuwar rundunar IDF ta harbe ta ne cikin kuskure yayin d ta ke harin jagorar zanga-zangar.''

    A cikin sanarwar nasu sun ƙara da cewa: "Rundunar IDF ta bayyana matuƙar baƙin cikinta game da rasuwar Aysenur Ezgi Eygi."

    Duk da haka, Amurka - babbar ƙawar Isra'ila - ta mayar da martani cikin fushi. kan lamarin inda sakataren harkokin wajen ƙasar, Antony Blinken, ya ce binciken da IDF ta yi ya nuna cewa kisan da aka yi wa Ba'amurkiyar ba shi da tushe balle makama.

    Ya ce ya goyi bayanrahotannin da ke cewa Ms Eygi na gudanar da zanga-zangar lumana ne lokacin da aka harbe ta kai tsaye.

  10. MDD ta yi tir da harin da Isra'ila ta kai sansanin ƴan gudun hijira a Gaza

    Wakilin tabbatar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) a Gabas ta Tsakiya ya yi tir da hari ta sama da Isra'ila ta kai kan wani sashe da aka warewa ƴan gudun hijira a Gaza.

    Tor Wannes-land ya ce dole ne a kiyaye dukkan ƙa'idojin ayyukan jin ƙai na ƙasa da ƙasa a kowane lokaci.

    Ya kuma yi kira ga dukkan ɓangarorin da su amince da yarjejeniyar tsagaita wuta da sako waɗanda aka yi garkuwa da su nan take.

    Ma'aikatar lafiya ta Hamas ta ce harin ya yi sanadiyar rasuwar mutum 19. Isra'ila ta yi iƙirarin cewa wasu jagororin Hamas ta hara a lokacin da take zargi suna cikin tantunan.

  11. Ana samun ƙaruwar yara masu fama da tamowa a Zamfara - MSF

    Kungiyar agaji ta likitoci watau MSF ta nuna damuwa kan yadda ake ci gaba da samun ƙaruwa a yawan yara da ke fama fa lalurar tamowa ko rashin abinci mai gina jiki a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.

    Ta ce matsalar tafi kamari a yankunan Shinkafi da Zurmi inda ta yi wa yara fiye da dubu 97 gwaji kuma sakamakon ya nuna cewa kashi 27 cikin 100 daga cikinsu na fama da tamowa.

    Gwaje-gwajen da aka yi a watan Yuni da ya gabata a yankunan ya nuna cewa fiye da kashi 20 cikin ɗari na yaran da aka yi wa gwajin na fama da rashin abinci mai gina jiki a matakin farko watau lalurar ba ta yi tsanani a jikinsu ba.

    Sai dai ƙungiyar ta nuna damuwa kan rashin maganin da ke ɗauke da sinadarin abinci mai gina jiki da ake amfani da shi wajen magancewa yaran matsalar sakamakon dakatar da aikin samar da abinci da asusun kula da yara na UNICEF ya yi a farkon shekarar da mu ke ciki.

    MSF ta ce rashin wannan magani mai ɗauke da sinadaran ƙarin kuzari da ake ba wa yaran masu lalurar ta tamowa a yankin arewa maso yammacin Najeriyar zai iya saka rayuwar yaran cikin haɗari tare da tsananta lalurar a jikinsu in ba a yi gaggawar ɗaukar mataki ba.

    Ta jaddada buƙatar ganin cewa an ɗauki ƙarin matakan shawo kan matsalar saboda a cewarta matsalar ta riga ta kai kololuwa kuma rashin maganin ya sa ana cigaba da samun ƙaruwa a yawan yara masu fama da wannan lalura.

    MSF ta ce ma’aikatanta sun yi wa yara fiye da dubu bakwai magani tun daga watan Janairun zuwa watan Yulin bana a yankunan Shinkafi da da Zurmi da Gummi da kuma Talata Mafara.

    Kuma a cewarta adadin yaran da aka kwantar a daidai wannan lokaci a shekarar 2023 ya zarce da kashi talatin da biyar cikin ɗari.

    "Mun kuma lura da yadda ake cigaba da samun ƙaruwar yara da ke kamuwa da wasu cututtuka da ake iya magancewa da allurar rigakafi ciki har da ƙyanda da malariya da amai da gudawa, a shekarar nan kaɗai mun warkar da yara masu fama da kyanda kusan 5,700," in ji MSF.

  12. Kotun EU ta ci tarar Google yuro biliyan 2.4

    Kotun ƙolin Turai ta yanke hukuncin cewa dole ne kamfanin Google ya biya tarar yuro biliyan 2.4 saboda amfani da ƙarfin ikonsa wajen yinkakagida a harkar kasuwanci.

    Google dai ya yi kokarin kalubalantar tarar da Hukumar Tarayyar Turai ta fara bayar wa a shekarar 2017, amma a yanzu kotun ta ki amincewa da ɗaukaka ƙarar da kamfanin ya shigar.

    Wannan ita ce tara mafi girma da hukumar ta taɓa yi, kodayake tun a wancan lokacin an ci tarar Google fiye da haka a wani lamari na daban.

    Wannan shawarar ta kawo ƙarshen shari'a na tsawon lokaci wanda aka fara a 2009 lokacin da kamfanin Birtaniya Foundem ya shigar da kara.

  13. Atiku ya soki Tinubu kan ƙoƙarin tauye haƙƙin ƙungiyoyin jama’a da kafafen yaɗa labarai

    Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana matukar damuwarsa game da abin da ya kira a matsayin cin zarafin ƙungiyoyin fararen hula da masu fafutuka da kafafen yaɗa labarai a ƙarƙashin gwamnatin shugaba Bola Tinubu.

    A wata sanarwa da Atiku ya fitar a shafinsa na X, ya kwatanta irin yanayin da ake fama da shi a halin yanzu da mafi tsananin kwanaki na mulkin kama-karya na sojoji, yana mai nuna fargaba kan yadda gwamnati ke ƙara tauye haƙƙin jama'a da ƙara dabarunta na tsoratarwa.

    Atiku ya ce "Kamen da aka yi wa shugaban NLC, Joe Ajaero misali ne ƙarara na kokarin da gwamnatin ke yi na rufe bakin ƙungiyoyin fararen hula da na ƙwadago."

    "Wannan matakin wani ɓangare ne na fafutukar da gwamnatin ke yi na tsoratar da manyan muryoyin jama’a a Najeriya." in ji Atiku.

    Atiku ya soki batun ƙaruwar barazanar ‘yancin ‘yan jarida.

    Ya kuma bayyana matakin DSS na mamaye ofishin SERAP a matsayin cin zarafi ga kimar dimokraɗiyya.

    Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya yi kira ga gwamnatin Tinubu da ta karkata akalarta daga murkushe ƙungiyoyin farar hula zuwa magance matsalar tsaro da ke addabar ƙasar.

  14. Tinubu ya taya al'ummar Maiduguri jimami kan iftila'in ambaliya

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya nuna matukar damuwarsa game da ambaliyar ruwa da ta afku a wasu sassan Maiduguri babban birnin jihar Borno.

    Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan harkokin yaɗa labarai Bayo Onanuga ya fitar.

    Ambaliyar ruwan ita ce mafi muni a cikin shekarun baya-bayan nan da birnin ya fuskanta yayin da ta raba dubban mutane da muhallansu tare da yin ɓarna a karamar ofishin gidan waya da asibitin koyarwa na Maiduguri.

    Tinubu ya jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar, musamman waɗanda suka yi asara sakamakon bala’in da ambaliyar ruwan ta haddasa.

    Tinubu ya kuma yi kira da a gaggauta kwashe mutane daga yankunan da abin ya shafa yayin da hukumomi ke ci gaba da tantance irin ɓarnar da ambaliyar ta yi.

    Shugaban ya kuma umurci hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) da ta taimaka wa waɗanda ambaliyar ta shafa.

  15. Jami'an Nema sun fara kai agaji Maiduguri

    Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) ta ce ta fara kai agaji domin kwashe mutanen da ambaliyar ruwa ta ɗaiɗaita a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

    Ambaliyar ta biyo bayan fashwar madatsar ruwa.

    Wata sanawar da babbar darektar hukumar Zubaida Umar ta fitar a shafinta na X, ta ce sun kuma fara shirye-shiryen tallafa wa mutanen da lamarin ya shafa da abinci, matsuguni da kuma magaunguna.

    Yankunan da ambaliyar ta shafa sun haɗa da Shehuri, rukunin gidaje da ke G.R.A, Gambomi, Budum, Bulabulin, Adamkolo, Millionaires Quarters, kasuwar Monday Market da kuma Gwange.

    NEMA ta ce gwamnatin jihar Borno ta buɗe sansanin Bakassi domin tsugunar da mutanen da ambaliyar ta shafa.

    Ta ce suna aiki da hukumar ba da agaji reshen jihar ta Borno domin tallafa wa mutanen da ke cikin sansanin.

  16. Mahawarar Harris da Trump da za ta zama zakaran gwajin dafi

    Muhawarar ƴan takarar shugaban ƙasa na da muhimmanci a siyasar Amurka. Kuma muhawarar da za a yi tsakanin Donald Trump da Kamala Harris a ranar Talata da daddare - wanda shi ne karo na farko da za su fafata - zai iya zama zakaran gwajin dafi.

    Rashin taɓuka abin kirki da shugaba Joe Biden ya yi a muhawarar shugaban ƙasa ta farko a karshen watan Yuni, ya janyo matsin lamba a cikin jam'iyyarsa ta Democrat har ta kai shi ga janye aniyarsa ta sake tsayawa takarar shugaban ƙasa.

    Duk da cewa Kamala Harris ta kasance mataimakiyar shugaban ƙasa na tsawon shekara uku da kuma ƴar takarar shugaban ƙasa na makonni bakwai, har yanzu wasu ƴan Amurka da dama ba su san ita wacece ba.

  17. An saki tsohuwar da aka zarga da maita bayan ta shekara 10 a kurkuku

  18. Mutum ɗaya ya mutu a harin jirgi mara matuki da Ukraine ta kai Rasha