Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Labarin wasanni daga 9 zuwa 15 ga watan Agustan 2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 9 zuwa 15 ga watan Agustan 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail da Abdulrazzaq Kumo

  1. Manchester United na iya dawowa ganiyarta - Sesko

    Sabon ɗan wasan gaba na Manchester United, Benjamin Sesko ya tattauna da gidan talbijin na kulob ɗin, MUTV a karon farko, bayan kammala atisayensa na farko gabanin wasansu da Arsenal a gasar Premier League, ranar Lahadi.

    A lokacin da yake tattaunawa kan abubuwan da yake son United ta cimma, Sesko ya ce:"Kawai mu ƙara bajinta da kusanci a matsayinmu na tawaga, mu yi ƙoƙari mu ƙara ƙwarewa kaɗan-kaɗan".

    "Lokaci kaɗan ya rage mu dawo ganiyarmu." Sesko ya ƙara.

    Kan dalilin da ya sa ya koma United, ɗan wasan mai shekara 22 ya ce: "Na farko saboda ƙungiya ce mai cike da tarihi".

    Ɗan wasan na Slovenia ya ƙara da cewa "A ganina tana hanya mai kyau kuma ba zan iya jira na fara ba."

  2. Kotu ta tabbatar wa da Palace taka leda a Conference League

    Hukuncin da kotu ta yanke ta tabbatar da cewa Crystal Palace za ta buga Europa Conference League sannan Nottingham Forest za ta buga Europa League a madadin Palace.

    Palace dai ta garzaya kotu ne domin ƙalubalantar hukuncin da hukumar ƙwallon ƙafar turai, uefa ta yi na hana ta damar buga gasar Europa League a kaka mai zuwa sakamakon hana kulob biyu da mutum ɗaya ke mallaka shiga gasar a lokaci guda.

    Ɗan kasuwar Amurka John Textor shi ne ya mallakin kashi 43 na Palace kafin ya sayar a watan Yuni, kuma shi ne mamallakin Lyon ta Faransa wadda ta samu gurbin buga Europa League.

    Hukuncin na zuwa ne kwana guda bayan Palace ta lashe kofin Community Shield bayan doke Liverpool.

    Kulob ɗin ya samu damar zuwa Europa League ne bayan lashe kofin FA Cup a kakar da aka kammala amma UEFA ta hana shi damar saboda rashin cika ƙa'idoji.

    Kotun ta ce Textor bai sayar da rabonsa na Palace da wuri ba.

  3. Grealish na daf da komawa Everton

    Everton na ci gaba da tattaunawa da Manchester City domin ɗaukar ɗan wasan Ingila Jack Grealish a matsayin aro.

    Ɗan wasan mai shekara 29 ba ya cikin waɗanda Guardiola ke shirin amfani da su a kaka mai zuwa bayan da ya ƙi sanya shi cikin jerin ƴan wasan ƙungiyar da suka buga gasar Club World Cup a Amurka.

    Rahotanni sun ce albashin Grealish a Manchester City ya kai fam 300,000 duk mako, lamarin da zai iya kawo cikas a cinikin, amma har yanzu ana ci gaba da tattaunawa.

    Grealish ya koma Man City ne daga Aston Villa kan fam miliyan 100 - a lokacin shi ne ɗan wasan Birtaniya mafi tsada a tarihi - inda ya buga fiye da wasanni 150 tare da lashe kofin Premier League sau uku, da Champions League guda, da kuma FA Cup.

    Amma a kakar wasan da aka kammala, wasanni bakwai kacal Grealish ya fara, har ta kai ga Guardiola ya gwammance ya saka Claudio Echeverri maimakon sa a wasan ƙarshe na gasar FA Cup.

  4. Tottenham na tattaunawa da Manchester City kan Savinho

    Ƙungiyoyin biyu sun fara tattaunawa a cikin ƴan kwanakin nan kan ɗan wasan na Brazil domin ya koma Tottenham.

    Majiyoyi sun shaida wa BBC cewa City ba ta da niyyar sayar da Savinho sai dai idan aka yi mata tayin fiye da fam miliyan 50.

    Idan har Spurs ta biya City wannan kuɗin, ta samu riba sosai kan ɗan wasan da ta saya daga ƙungiyar Troyes ta faransa kan fam miliyan 30.8 a shekarar da ta gabata.

    Savinhho ya buga wasanni da dama a kakar wasan da aka kammala amma ƙwallo uku kawai ya zura a cikin wasa 48.

    City ta kuma sayi Cherki daga Lyon kan fam miliyan 30, lamarin da zai iya rage damar Savinho ta buga wasanni.

    Kocin Spurs Thomas Frank ya nace domin maye gurbin ɗan Son Heung-min wanda ya bar ƙungiyar a makon jiya.

  5. Za mu sayar da Guehi - Shugaban Crystal Palace

    Shugaban ƙungiyar Crystal Palace Steve Parish ya ce ƙungiyar za ta sayar da kyaftin ɗinta Marc Guehi domin guje wa asara idan ya bar ƙungiyar a kyauta a shekara mai zuwa.

    Ɗan wasan na Ingila na da shekara ɗaya kacal da ya rage a kwantiraginsa kuma ba shi da niyyar sanya hannu kan sabuwar kwantaragi.

    A watan Janairu Palace ta ƙi sayar da shi ga Newcastle kan fam miliyan 65 saboda sa ran zai tsawaita zamansa.

    Guehi dai na son zama a ƙungiyar domin ya bar ta ba kyauta a 2026 amma ƙungiyar ta gwammace ta sayar da shi yanzu ta samu kuɗi.

  6. Labarai da dumi-dumi, Crystal Palace ta ɗauki kofin Community Shield a hannun Livepool

    Crystal Palace ta lashe kofin ƙalubale na Community Shield bayan doke zakarun gasar Premier League Liverpool a bugun finareti.

    Wasa ya tashi 2-2 a tsakaninsu, abin da ya sa aka wuce zagayen bugun finareti kai-tsaye ba tare da ƙarin lokaci da ake kira extra time ba.

    Ekitike ne ya fara ci wa Liverpool ƙwallo bayan minti huɗu kacal da take wasa, kafin Mateta ya farke ta daga bugun finareti.

    Sai kuma a minti 21 Frimpong ya ci wa Liverpool ƙwallo ta biyu, wadda Sarr ya farke wa Palace a minti na 77.

    Wannan ne kofi na biyu da Palace ta ɗauka cikin wata uku bayan lashe kofin FA a watan Mayu, inda ta doke Manchester City a wasan ƙarshen.

  7. Newcastle ta kusa kammala ɗaukar Thiaw daga AC Milan

    Newcastle United na gab da kammala ɗaukar ɗanwasan baya Malick Thiaw daga AC Milan.

    Ana sa ran ɗanƙwallon mai shekara 24 zai isa Ingila a yau Lahadi domin a gwada lafiyarsa da kuma kammala komawarsa filin wasa na St James' Park.

    Newcastle ta gaza sayen 'yanwasa da dama da ta yi yunƙurin ɗauka a bazarar nana, ciki har da Benjamin Sesko da ya koma Man United, da Hugo Ekitike, Joao Pedro, da James Trafford, amma an fahimci cewa Thiaw na son ya je kulob ɗin.

    Ɗan ƙasar Jamaus ɗin zai koma Newcastle ne kan fan miliyan 34.62 haɗi da tsarabe-tsarabe.

  8. Diakite zai koma Bournemouth daga Lille

    Bournemouth na gab da kammala cinikin ɗanwasan baya Bafode Diakite daga Lille kan kuɗi fan miliyan 34.6.

    Za ta biya fan miliyan 30 nan take da kuma 4.3 a tsarabe-tsarabe kan Diakite mai shekara 24, wanda zai zama na biyu mafi tsada da Bournemouth ta saya a tarihinta.

    Ɗanwasan bayan ya buga wasa 85 a gasar Ligue 1 ta Faransa bayan koma Lile daga Toulouse a 2022, kuma ya buga wasa 10 a gasar zakarun Turai ta Champions League.

    Yanzu haka Diakite na Birtaniya domin a gwada lafiyarsa kuma zai zama na uku da ta ɗauka a wannan bazarar bayan Adrien Truffert da mai tsaron raga Djordje Petrovic.

  9. Barau FC ta ɗauki 'yanwasa 10 kafin fara firimiyar Najeriya ta bana

    Ƙungiyar Barau FC da ke ta sayi 'yanwasa 10 zuwa yanzu a shirye-shiryen da take yi na tunkarar gasar firimiya ta Najeriya NPFL.

    Wannan ne karon farko da ƙungiyar ta garin Kano za ta taka rawa a babbar gasar tamaula ta Najeriya bayan samun nasarar haurorwa a ƙarshen kakar da aka kammala daga ƙaramar gasar NNL.

    Jerin 'yanwasan da ta ɗauka su ne:

    • Abraham Nana Kwame
    • Sunday Anthony
    • Yusuf Muhammed
    • Hillary Ekawu
    • Emmanuel Okoko Jnr
    • Adamu Usaini
    • Kabiru Abdullahi
    • Mike Zaruma
    • Samuel Mathias
    • Abubakar Shuaibu
  10. Sunderland ta ɗauki ɗanwasa na 10 kafin fara kakar wasa ta bana

    Ƙungiyar ƙwallom ƙafa ta Sunderland ta sayi ɗanwasa na 10 a bazarar nan a shirye-shiryen da take yi na komawa buga gasar Premier League ta Ingila.

    Kulob ɗin ya sanar da ɗaukar Arthur Masuaku, ɗanwasan baya a ɓangaren hagu daga West Ham, kan yarjejeniyar shekara biyu.

    Ɗanƙwallon na ƙasar Dimokuraɗiyyar Kongo ya bi sawun 'yanwasa kamar: Enzo Le Fee, Habib Diarra, Noah Sadiki, Reinildo Mandava, Chemsdine Talbi, Simon Adingra, Granit Xhaka, Robin Roefs, da kuma Marc Guiu.

    Masuaku mai shekara 31 ya buga wa West Ham wasa 128 daga 2016 zuwa 2022 kafin ya koma taka wa Besiktas ta Turkiyya leda.

  11. 'Yanwasan da Katsina United ta saya kafin kakar wasa ta bana

    Ƙungiyar Katsina United mai buga gasar firimiyar Najeriya ta NPFL ta ƙarfafa tawagarta da sababbin 'yanwasa kafin fara kakar wasa ta bana.

    Zuwa yanzu ƙungiyar ta garin Katsina ta ɗauki 'yanwasa takwas da zimmar neman lashe kofin NPFL na bana da za a fara ranar 22 ga watan Agustan nan.

    Shugaban ƙungiyar Surajo Umar Dalibi ya yi wa dukkan 'yanwasan maraba a filin wasansu na Muhammadu Dikko da ke garin Katsina.

    Ƙungiyar ta ƙare a mataki na 15 a teburin NPFL na kakar da aka kammala da maki 50, inda ta ci wasa 14, ta yi cvanjaras 8, kuma aka ci ta 16.

    Ga jerin 'yanwasan da ta ɗauka zuwa yanzu:

    • Segun Adekunle = daga Kwara United
    • Adekunle Oluwasegun Samuel = daga Kwara United
    • Philip Clement Ogwuche = daga Abia Warriors
    • Uche Collins = daga Bendel Insurance
    • Adiku Moses = daga Enyimba FC
    • Bashir Usman = daga Rangers International
    • Falolu Azeez Olamilekan = daga Alnaser Zliten, Libya
    • Innocent Arigu = daga Sunshine Stars
  12. Rodri zai sake yin jinyar watanni, in ji Guardiola

    Ɗanwasan tsakiya na Manchester City Rodri ya sake jin rauni kuma da wuya ya murmure kafin hutun watan Satumba, in kocinsa Pep Guardiola.

    Ɗanƙwallon na Sifaniya ya shafe mafi yawan kakar bara a gadon jinya saboda turguɗe gwiwa da ya yi a watan Satumban 2024.

    Mai riƙe da kambin Ballon d'Or na 2024, ya koma taka leda a matsayin canji a wasan ƙarshe na Man City na gasar Premier League da ta buga da Bournemouth.

    Sai kuma wasan da Al-Hilal ta fitar da su daga gasar Club World Cup a Amurka, inda aka yi canjinsa daga baya.

    "Rodri na samun sauƙi saboda ya ji babban rauni a wasan da muka kara da Al-Hilal," in ji Guardiola.

  13. Man United ta ɗauki kofin sada zumunta na biyu

    Manchester United ta lashe kofin Snapdragon Cup bayan doke Fiorentina a bugun finareti bayan wasa ya tashi 1-1.

    Wasan sada zumuntar da aka buga a filin wasa na Old Trafford, shi ne na ƙarshe da United za ta yi a shirye-shiryen kakar wasa ta bana.

    Ƙwallon da Robin Gosens ya ci gidansu ce ta bai wa United damar farke ƙwallon da Simon Sohm na Fiorentina ya ci tun a minti na takwas.

    Wannan ne kofin sada zumunta na biyu da Man United ta ɗauka bayan lashe Premier League Summer Series a Amurka ranar Lahadi.

    Mai tsaron ragar United Altay Bayindir ne ya bige bugun finareti ɗaya, inda daga baya Kobbie Mainoo ya ci wa United ɗin na ƙarshe.

    Sai da aka gabatar da sababbin 'yanwasan da United ta cefano a kasuwar bazarar nan kafin take wasan: Matheus Cunha, Diego Leon, Bryan Mbeumo, Benjamin Sesko.

  14. West Ham ta sayi mai tsaron raga Hermansen kan fam miliyan 20

    West Ham ta sanar da sayen mai tsaron raga Mads Hermansen daga Leicester City kan fam miliyan 20.

    Ɗan wasan ɗan asalin Denmark ya amince da kwantiragin shekara biyar da zaɓin ƙarin shekara ɗaya.

    Mai shekara 25 ɗin ya haskaka a Leicester a kakar da ta gabata, duk da cewa sun koma gasar Championship.

    Ya buga wasanni 72 a Leicester, inda ya lashe gasar Championship a 2024.

    Ya bi sahun Wilfred Ndidi wajen barin ƙungiyar, wanda ya koma Besiktas ta Turkiyya ranar Juma'a - bayan shafe tsawon shekara tawkas da rabi a filin wasa na King Power.

  15. Ɗanwasan Real Madrid Reinier Jesus ya koma Brazil da taka leda

    Ɗanwasan tsakiya na Real Madrid Reinier Jesus ya koma Atlético Mineiro ta Brazil da taka leda.

    Saura shekara ɗaya kwantaraginsa ya ƙare a Madrid amma duk da haka Real ta cimma yarjejeniyar cinikinsa da Atletico.

    Ɗan shekara 23 ɗin ya koma Real ne a watan Janairun 2020 kan yuro miliyan 30 daga Flamengo ta Brazil ɗin, amma bai taɓa buga wa babbar tawagar Madrid wasa ba.

    An tura shi wasa aro sau huɗu zuwa Borussia Dortmund, da Girona, da Frosinone, da Granada.

    Reinier ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara huɗu da Mineiro zuwa 2029, amma Real ce ke da alhakin samun rabin kuɗinsa idan Mineiro za ta sake sayar da shi nan gaba.

  16. Real Madrid ta tsawaita zaman Gonzalo Garcia da shekara biyar

    Real Madrid ta tabbatar da cewa matashin ɗanwasa Gonzalo García ta sanya hannu kan yarjejeniyar shekara biyar a ƙungiyar zuwa watan Yunin 2030.

    García ya koma Real ne a 2014 yana da shekara 10 kacal kuma ya ci gaba da zama a kwalejin horon ƙwallo tsawon shekara 10.

    Ya fara taka wa babbar tawagar kulob ɗin leda a watan Nuwamban 2023, inda ya taimaka mata wajen lashe gasar La Liga a shekarar.

    Shi ne ya fi zira ƙwallo a raga a gasar Club World Cup da aka yi a kakar wasa ta bara.

    Real ta tabbatar cewa yanzu zai koma taka leda a babbar tawaga ƙarƙashin mai horarwa Xavi Alonso, har ma an ba shi sabuwar lamba 16.

  17. Galatasaray ta ɗare saman teburin firimiyar Turkiyya

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Galatasaray mai buga gasar Super Lig ta Turkiyya ta ɗare saman teburin gasar bayan nasara a wasan farko.

    Mai riƙe da kofin gasar Galatasaray ta doke Gaziantep FK har gida 3-0 a wasan da suka buga jiya Juma'a.

    Baris Yilmaz ne ya fara cin ƙwallo daga bugun finareti a minti na 12, sai Evren Elmali da ya ƙara ta biyu a minti na 16.

    Ɗanwasan gabanta kuma ɗan Najeriya Victor Osimhen bai buga wasan ba saboda wani ƙaramin rauni da ya ji.

    Yilmaz ya ƙara ta uku ana gab da tafiya hutun rabin lokaci, yayin da Gaziantep ta ƙare wasan da 'yanwsa 10 a cikin fili bayan korar Mustafa Bozan.

  18. CHAN 2024: Algeria da Afirka ta Kudu sun tashi canjaras

    Afirka ta Kudu da Aljeriya sun tashi 1-1 a wasan cikin rukuni a gasar kofin ƙasashen Afirka ta 'yanwasan cikin gida wato CHAN.

    Shi ne wasa na biyu da suka gwabza a Rukunin C, wanda ya ƙunshi Guinea da Nijar da Uganda.

    Sakamakon ya sa Aljeriya ta ɗare saman teburin rukunin da maki 4, da Uganda ta biyu da maki 3, Guinea ta uku da maki 3, sai kuma Afirka ta Kudun 1.

    Nijar ce ta ƙarshe a rukunin maras maki amma wasa ɗaya ta buga.

    Ƙaasashen Tanzania da Kenyua da Zanzibar ne ke karɓar baƙuncin gasar ta 2024.

  19. Man United ta kammala ɗaukar Sesko

    Manchester United ta kammala ɗaukar Benjamin Sesko daga RB Leipzig kan fan miliyan 73.7.

    Ɗan ƙasar Slovenia ya koma Old Trafford kan yarjejeniyar shekara biyar, kuma ta ƙunshi cewa United za ta biya fan miliyan 66.3 nan take tare da biyan sauran a matsayin tsarbe-tsarabe.

    Shi ne na babban ɗanwasa na uku da United ta ɗauka bayan zuwan Mtheus Cunha da Bryan Mbeumo.

    Newcastle ta sha neman Sesko mai shekara 22 amma sai ya zaɓi ya koma tawagar ta Ruben Amorim.

    "Tabbas tarihin Man United na musamman ne amma kuma abin da ya fi ɗaukar hankalina shi ne abin da zai faru nan gaba," in ji Sesko.

  20. Maraba

    Barkanmu da haɗuwa a shafin labarin wasanni na kai-tsaye.

    Ku biyo mu domin halin da ake ciki a duniyar wasannin daga yau har zuwa ranar Juma'a mai zuwa a wannan shafi.