Rufewa
Jama'a masu bibiyarmu a wannan shafin da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye, a nan muke muku sallama da bankwana sai gobe Lahadi idan Allah ya kai mu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 14/06/2025
Ahmad Bawage da Muhammad Annur
Jama'a masu bibiyarmu a wannan shafin da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye, a nan muke muku sallama da bankwana sai gobe Lahadi idan Allah ya kai mu.

Asalin hoton, Reuters
Kasar Iran ta ci gaba da yin ruwan makamai masu linzami a daren Lahadi kan Isra’ila, yayin da ita ma Isra’ilar ta ce ta tana ci gaba da kai hare-hare kan cibiyoyin soji a Tehran.
Hukumar agaji ta Isra’ila ta bayar da rahoton mutuwar wata matsahiya da kuma raunata mutane da dama a harin da irin ta kai na baya-bayan nan.
Kafar talabijin ta gwamnatin Iran ta ce makamai masu linzami kimanin 100 kasar ta harba kan Isra’ila musamman kan biranen Tel Aviv da Haifa.
A bangare daya hukumar kula da arzikin man fetur ta Iran ta ce Isra’ila ta kai hari kan cibiyar man fetur ta Shahran da ke birnin Tehran.
Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya yi barazanar mayar da “mummunan maryani” matukar Isra’ila ta ci gaba da kai wa Iran hari.

Asalin hoton, NPF
Masu kwacen waya sun kashe wani ma'aikacin Jami'ar Northwest da ke Kano, Buhari Imam, ta hanyar daba masa wuta.
Bayanai sun nuna cewa barayin sun ritsa shi ne a yankin unguwar Sheka da ke karamar hukumar Kumbotso, inda suka sossoke shi da wuka a ciki kuma suka kwace wayarsa, a ranar Laraba.
Marigayin ya rasu bayan da aka garzaya da shi asibitin koyarwa na Mallama Aminu Kano, a jiya Juma'a.
Shugaban kungiyar ma'aikatan jami'ar (NASU), Kwamared Bashir Muhammad, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya yi kira ga gwamnatin jihar kano da sauran hukumomi da su dauki tsattsauran mataki a kan kisan.

Asalin hoton, EPA
Shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Amurka Donald Trump sun tattauna a game da rikicin Isra'ila da Iran ta waya tsawon minti hamsin.
Fadar gwamnatin rasha, Kremlin ta bayyana tattaunawar a matsayin ta keke-da-keke, mai tsawo kuma mai amfani.
Kakakin fadar ta Rasha, Yuri Ushakov, ya yi Allah-wadarai da harin da Isra'ila ta kai wa Iran, yana mai gargadin cewa zai iya haifar da illar da ba a taba tsammani ba ga gaba dayan yankin Gabas ta Tsakiya.
Mista Ushakov, ya ce, shugabannin na Rasha da Amurka sun bar kofa a bude ta sabuwar tattauna a kan shirin nukiliyar Iran.
Haka kuma Rasha ta nuna alamun aniyarta ta komawa tattaunawa da Ukraine nan gaba a cikin watan nan na Yuni.

Asalin hoton, Reuters
'Yansanda a jihar Minnesota ta Amurka na ci gaba da farautar wani danbindiga da ya harbe wata 'yar majalisar dokokin jihar ta jam'iyyar Democrat tare da mijinta, ya kuma raunata wasu mutum biyu.
Mutumin wanda yake sanye da kayan 'yansanda ya harbe Melissa da Mark Hortman a gidansu da sanyin safiyar yau Asabar, a harin da aka bayyana a matsayin shiryayye.
Jim kadan kafin wannan harin, an harbi wani dan jam'iyyar ta Democrat na jihar ta Minnesota, John Hoffman da matarsa, to amma sun tsallake rijiya da baya kasancewar rauni aka ji musu a harbin.
An samu wata alama da 'yansanda suka bayyana a matsayin alamar wurare da mutanen da dan bindigar zai kai wa hari, a cikin motar maharin.
Shugaba Dpnald Trump ya ce ba a lamunci irin wannan tashin-tashinar a Amurka ba.
Wadanda suke jagorantar zanga-zangar kin jinin gwamnatin Trump a jihar ta Minnesota sun soke gangamin, sakamakon harbin.
Haka su ma 'yansanda sun bukaci jama'a da kada su halarvci gangamin domin tsaron lafiyarsu.

Asalin hoton, Getty Images
An fargabar cewa an kashe akalla mutum 100 a wani hari da 'yanbindiga suka kai a garin Yelewata da ke yankin karamar hukumar Guma da ke jihar Benue.
Maharan sun far ma al'ummar garin na Yelewata ne a cikin daren da ya gabata wayewar garin Asabar din nan, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Haka kuma jaridar ta labarta cewa a wani harin na daban kuma an kashe sojoji biyu a garin Daudu, shi ma a yankin karamar hukumar ta Guma.
Wannan harin shi ne na uku a baya-bayan nan a garin Yelewata wanda ke kan iyakar jihar ta Benue da Nasarawa a cikin mako daya.
Shi kuwa garin na Daudu yana nisan kilomita kusan 20 ne daga Makurdi, babban birnin jihar.
Wadanda suka ga harin na Yelewata sun ce maharan sun mamayi garin ne kafin karfe 12 na dare, inda suka kwashe sama da sa'a biyu, suna ta'annati ba tare da wani dauki daga jami'an tsaro ba.

Asalin hoton, GPO
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce burin ƙasarsa shi ne ta daƙile barazana biyu daga gwamnatin Iran - barazanar makaman nukiliya da ta manyan makamai masu linzami, kuma ya ce Isra'ila ta cimma burinta.
Ya ce Isra'ila ba za ta taba barin Iran ta samu ƙarfin ƙera makamai masu linzami 20,000 ba, ''saboda haka muka dauki matakin lalata fasaha da ƙarfinsu, kuma wannan shi ne abin da rundunar sojin Isra'ila ke yi a yanzu,'' in ji shi.
Ya ƙara da cewa: ''Mun bude hanyar shiga Tehran. Nan gaba kadan za ku ga jiragen yaƙin Isra'ila, da sojojin sama na Isra'ila, da matuka jiragenmu, a sararin samaniyar Tehran.''
Netanyahu ya ce Isra'ila za ta kai wa Iran hari a duk inda ta nufa, bayan da Iran din ta mayar da martani kan harin da Isra'ilar ta kai mata ranar Juma'a.
Iran ta harba makamai masu linzami cikin sassan biranen Isra'ila a jiya dadaddare, inda hukumomin Isra'ilar suka ce harin ya kashe mutum uku.

Asalin hoton, Reuters
Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi alwashin mayar wa Isra'ila martani "mai tsanani" idan har suka ci gaba da kai musu hare-hare.
"Sojojin Iran za su mayar da martani mai zafi idan gwamnatin Isra'ila ta ci gaba da far mana," in ji Pezeshkian.
An ruwaito cewa ya yi kalaman ne a lokacin da yake tattaunawa ta wayar tarho da Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif.

Asalin hoton, Getty Images
Yayin da manoma a sassa daban-daban na Najeriya suka koma gona, masana sun yi gargaɗin cewa daminar bana za ta zo da kalubale kamar na sauyar yanayin ruwan sama - inda ruwan zai yi jinkirin sauka ya kuma ɗauke da wuri a wasu wuraren, da tsadar kayan noma irin su taki da kuma matsalar tsaro a wasu wuraren.
To dangane da waɗannan - wane irin tanadi kuka yi wa daminar ta bana?
Kuma yaya za a yi a rage tasirin waɗannan matsaloli da za ta zo ko ma ta zo da su?
Waɗannan na daga cikin batutuwan da shirinmu na ra'ayi riga na wannan makon ya tattauna a kai.
An soke ci gaba da tattaunawa tsakanin Amurka da Iran kan shirin nukiliyar Tehran da aka tsara yi gobe Lahadi.
Ministan harkokin wajen Oman, Badr Albusaidi ne ya bayyana haka a shafinsa na X.
"Tattaunawar Amurka da Iran kan shirin nukiliyar Tehran da aka tsara yi ranar Lahadi a birnin Muscat ba zai yiwu ba," in ji Albusaidi.
"Sai dai diflomasiyya da kuma tattaunawa shi ne kaɗai hanyar samar da zaman lafiya mai ɗorewa."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

A garin Rishon LeZion da ke wajen birnin Tel Aviv, harin Iran ya mayar da wani titi a wurin zuwa ɓaraguzai da kuma ƙura ko ta na.
Girman harin ya janyo lalacewar motoci, ruguza gidaje da faɗuwar itatuw, inda aka kashe aƙalla mutum biyu.
Takardun yara da kuma abin wasansu na cikin abubuwa da suka koma ɓaraguzai.
Tun sanyin safiyar yau, iyalai vna ta komawa wurin da lamarin ya faru, domin ƙoƙarin samun abin da ya rage a gidajensu.

Asalin hoton, Reuters
A halin yanzu rikicin da ya ɓarke tsakanin Isra’ila da Iran ya taƙaita ne ga ƙasashen biyu.
Majalisar Ɗinkin Duniya da sauran ƙasashe na ta kira kan cewa a yi taka-tsantsan.
To amma me zai faru idan ƙasashen biyu suka ki jin shawarar yin taka-tsantsan? Haka nan me zai faru idan yaƙin ya bazu kuma ya faɗaɗa?

Asalin hoton, Ambaliya
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya NiMet ta ce akwai yiwuwar wasu jihohin Najeriya su fuskanci ambaliya a daminar bana.
Wata sanarwa da NiMet ta fitar a shafinta na X, ta ce jihar Akwa Ibom ce tafi barazanar fuskantar ambaliyar a yanzu.
Sauran jihohin sun haɗa da Sokoto, Zamfara, Plateau, Yobe, Bauchi da kuma Bayelsa.
Sai Nasarawa da Benue da Ogun da Ekiti da Delta da kuma Ribas.
Don haka ne hukumar ta gargaɗi jama'a, musamman waɗanda ke jihohin da lamarin zai iya shafa, da su riƙa yashe magudanan ruwa domin buɗe wa ruwa hanyar wucewa.
Ta shawarce su da su riƙa yin nesa da wuraren da ke da haɗarin ambaliya, inda ta ce in ta kama su tashi daga waɗannan wurare.
A kowace shekara dai, ambaliya na yin sanadiyyar rayukan mutane da dama da kuma lalata gidaje a Najeriya.
Ko a kwanaki nan ambaliya ta afka wa garin Mokwa da ke jihar Neja, abin da ya janyo mutuwar aƙalla mutum 230.
Dakarun tsaron Isra'ila sun ce masana nukuliyar Iran biyar a hare-hare da suka kai.
A baya, sojojin Isra'ila sun ce sun kashe shida bayan kaddamar da hari kan Iran ranar Alhamis.
Yanzu Isra'ila ta ce mutum tara ne suka mutu a farkon harin.
A ɗaya gefe, wani jami'in sojin Isra'ila ya ce sun lalata wuraren nukiliya na Esfahan da Natanz, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.
Jami'in ya faɗa wa Reuters cewa an far wa wurare sama da 150 a Iran.
An kakkaɓe yawancin jirage marasa matuki da aka harba cikin Isra'ila, in ji jami'in.

Gomman masu aikin ceto da kuma jami'an tsaro, riƙe da bindigogi na duba gine-ginen da harin Iran ya lalata a birnin Rishon LeZion, da ke wajen Tel Aviv.
Ɗaya daga cikinsu ya shaida wa BBC cewa suna amfani da karnuka don duba ko akwai sauran abubuwan fashewa da aka datsa a wurin.
Ana kuma amfani da manyan motoci wajen yashe ɓaraguzai gefe.
Isra'ila ta ce harin na daren jiya Juma'a ya hallaka mutum uku.

Asalin hoton, Bola Tinubu/Facebook
Gwamnatin Najeriya ta yi Alla-wadai da harin da Isra'ila ta kai wa Iran, abin da ya janyo yaɗuwar rikici tsakanin ƙasashen biyu.
Wata sanarwa da ma'aikatar harokokin wajen ƙasar ta fitar, ta ce Najeriya na nuna damuwa da kuma kiran kai "zuciya nesa" tsakanin ɓangarorin biyu, don samar da zaman lafiya a duniya.
Ta ce ci gaba da kai hari da kuma ramuwa tsakanin ƙasashen biyu, yana ƙara saka rayukan fararen hula cikin barazana da kuma jefa Gabas Ta Tsakiya cikin bala'i, abin da zai janyo matsala a ɓangaren tsaron ƙasa da ƙasa da kuma cigaban tattalin arziki.
"A matsayin mu na ƙasar da ke son zaman lafiya, da ganin kyautatuwar hulɗar diflomasiyya, muna kira ga dukkan ɓangarori da ke rikici da su fifita tattaunawa maimakon faɗa da juna," in ji sanarwar.
Najeriya ta kuma buƙaci al'ummomin ƙasashen waje, musamman kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, da su ɗauki matakan kauce wa yaɗuwar rikicin, da kuma laluɓo hanyar warware rikicin.
"Ɗaukar matakin soji ba zai taɓa haifar da ɗa mai ido ba.
Gwamnatin Najeriyar ta ce a shirye take wajen bayar da gudummawa a ƙoƙarin hana yaɗuwar rikicin, da kuma ganin an ɗabbaka zaman lafiya a yankin.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Kafofin yaɗa labaran Iran sun ruwaito cewa mutum 60 ne aka kashe, ciki har da yara 20, bayan harin da Isra'ila ta kai kan gine-gine a Tehran ranar Juma'a.
Isra'ila ta ce tana kai hare-hare ne kan sansanonin sojin Iran, ciki har da cibiyoyin nukiliya.
Alkaluman da muka samu daga wakilin Iran a kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ranar Juma'a, ya ce mutum 78 aka kashe a hare-haren na Isra'ila.
Ba a dai san cewa ko mutum 60 ɗin na cikin waɗancan alkaluma na baya ba, kuma BBC ba ta kai ga tantance alkaluman ba.

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar ƴansandan jihar Katsina ta ce ta ceto mutum 73 da aka yi garkuwa da su.
Ta kuma ce ta kama mutum 75 waɗanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban a faɗin jihar.
Wata sanarwa da mai magana da yawun ƴansandan jihar, Abubakar Sadiq ya fitar, ta ce ana zargin mutum 15 cikin mutanen da laifin fashi da makamai, yayin da wasu 20 kuma da laifin kisa.
"An kama mutum guda da laifin mallakar bindiga, 30 da zargin aikata fyaɗe sannan 108 kuma an kama su ne da wasu laifukan," in ji sanarwar.
Sadiq ya ce makaman da aka ƙwato daga wajen mutanen sun haɗa da bindigar AK-49, karamar bindiga ƙirar pistol, ɗaruruwan harsasai, babura biyu da kuma shanu 174 da ake zargin sun sace.
Ya ce ana ci gaba da kula da waɗanda aka kuɓutar daga hannun masu garkuwan.

Asalin hoton, EPA
Minisan tsaron Isra'ila, Israel Katz, ya ce "Tehran za ta ƙone" idan Iran ta ci gaba da kaddamar da makaman linzami.
Kalamansa na zuwa ne yayin aikin duba irin ɓarnar da harin ramuwa na Iran ya yi da jami'ai.
Katz ya ce: "Masu mulkin kama-karya a Iran sun mayar da ƴan ƙasar zuwa ƴan mafaka, kuma suna yin abin da zai sa mazauna Tehran su ɗanɗana kuɗarsu saboda far wa fararen hular Isra'ila."

Asalin hoton, Social Media
Allah ya yi wa Malam AbdulMannan Abubakar Giro Argungu rasuwa.
Ya rasu a safiyar yau Asabar a garin Argungu da ke jihar Kebbi, bayan fama da rashin lafiya.
Malamin ya kasance ɗa ga marigayi Sheikh Abubakar Giro Argungu.
Wani sako da Sheikh Isa Ali Pantami ya wallafa a shafinsa na X, ya ce za a yi jana'izar malamin a Masallacin Idi da ke garin Argungu yau Asabar.