Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 1 ga watan Mayu, 2024.

Taƙaitattu

  • Gwamnatin Najeriya ta yi wa ma’aikata ƙarin albashi
  • Abin da ya sa ake biyan wasu ma'aikata albashin da 'bai taka kara ya karya ba' a Borno
  • An kama ɗaliban da ke zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Amurka
  • Mutum 24 sun mutu a China sanadiyyar zaftarewar titi
  • An yi artabu tsakanin ɗalibai masu goyon baya da masu ƙin jinin Falasɗinawa
  • Ya kamata a daɗaɗa wa ma'aikatan Najeriya - Tinubu
  • Ƙungiyoyin ƙwadago sun yi fatali da ƙarin albashin ma'aikata a Najeriya

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi, Buhari Fagge

  1. Abin da ya sa ake biyan wasu ma'aikata albashin da 'bai taka kara ya karya ba' a Borno

    Batun albashin ma’aikatan a jihar Borno ya ja hankali a kafofin sada zumunta a Najeriya inda aka riƙa yaɗa sakon banki da ke nuna kuɗi ƙasa da naira 10,000 wasu har 4,000 da wasu ma’aikatan jihar ke karɓa a matsayin albashi.

    Wani mutum da BBC ta zanta da shi ya ce ya kwashe sama da shekara 10 ya na aiki a matsayin ma'aikacin gwamnatin jihar ta Borno amma har yanzu albashinsa bai wuce naira 15,000.

    Ya ce hakan na faruwa ne duk kuwa da cewa karatunsa ya kai matakin digiri na biyu, duk da dai a farko an ɗauke shi aiki ne da takardar shaidar kammala sakandare.

    Ya bayyana wa BBC cewa "mutane na cikin hali na ha'ula'i, ma'aikata na kwashe kwana 30 suna jiran albashi amma a ƙarshe sai a ba su 15,000 ko 8,000 ko 7,000".

    Sai dai ya ce hakan ya samo asali ne tun gwamnatocin da suka gabata.

    A ɓangare ɗaya, gwamnatin jihar Borno ta ce ma'aikatan da ba su ƙware ba ne ke samun ƙaramin albashi.

    Kwamishinan ilimi na jihar, Injiniya Lawan Abba Wakilbe ya ce "duk wani ƙwararren malami muna biyan shi albashi da kyau, waɗanda ake biya irin wancan albashi ba ƙwararru ba ne, kamata ya yi a ce mun sallame su".

    Ya ce "masu NCE satifiket muna biyan su naira 52,000, BEd kuma daga 60,000 zuwa sama, waɗanda kuma suka yi nisa muna biyan su 100,000 har ma sama da haka".

    Saurari rahoton Awwal Ahmed Janyau:

  2. Gwamnatin Najeriya ta yi wa ma’aikata ƙarin albashi

    Gwamnatin tarayya a Najeriya ta yi wa ma’aikatanta ƙarin albashi da kimanin kashi 25 cikin ɗari zuwa kashi 35 cikin ɗari.

    Hakan na zuwa ne a daidai lokacin bukin ranar ma’aikata ta duniya.

    A ranar Talata ne wata takarda daga shugaban hukumar kula da albashi ta Najeriya, Ekpo Nta ta tabbatar da ƙarin albashin.

    Takardar ta nuna cewa ƙarin albashin zai fara ne daga ranar ɗaya ga watan Janairun 2024.

    Kamar akasarin al'umma ƙasar, ma’aikatan gwamnati a Najeriya sun faɗa cikin mawuyacin hali sanadiyyar matsin tattalin arziƙi.

    Kayan masarufi sun yi tashin gwauron zabi sannan darajar naira ta zube idan aka kwatanta da dalar Amurka duk kuwa da sabbin matakan da gwamnatin ƙasar ke ci gaba da ɗauka.

    Yanzu haka akwai wani kwamiti da gwamnatin ƙasar ta kafa wanda ke aiki tare da ƙungiyoyin ƙwadago na ƙasar domin samar da matsaya kan ƙarancin albashi ga ma'aikata a ƙasar.

    A baya ƙungiyoyin ƙwadago sun sha yin barazanar shiga yajin aiki da durƙusar da lamurra a ƙasar domin tursasa wa gwamnatin tarayya ɗaukan matakan bunƙasa walwalar ma'aikata.

    A halin yanzu mafi ƙarncin albashin ma'aikata a hukumance shi ne naira 30,000.

    Kuma duk da haka akasarin gwamnatocin jihohi ba su iya biyan ma'aikatansu albashin mafi ƙaranci, inda akan samu wasu ma'aikata na bin bashin albashin watanni da dama.

    Wannan sabon albashin da gwamnatin ta amince da shi zai shafi ma’aikatan gwamnati da ke bisa tsarin CONPSS, da na ma’aikatan kwalejojin bincike na CONRAISS, da jami’an ƴansanda (CONPOSS) da ma’aikatan tattara bayanan sirri (CONICCS) da sauran masu ɗamara (CONPASS) da kuma dakarun ƙasar (CONAFSS).

  3. Barka da warhaka!

    Barkan mu da warhaka, da fatan duk muna cikin ƙoshin lafiya kuma da fatan za ku kasance tare da wannan shafi na BBC Hausa wanda zai kawo muku bayanai kan muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Ya kamata kuma ku je shafukanmu na sada zumunta: facebook, X, Instagram domin bayyana ra'ayoyinku kan abubuwan da muke wallafawa.

    Akwai ƙayatattun hotuna da za ku ji daɗin kallo a wannan rana ta ma'aikata.