Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 1 ga watan Mayu, 2024.

Taƙaitattu

  • Gwamnatin Najeriya ta yi wa ma’aikata ƙarin albashi
  • Abin da ya sa ake biyan wasu ma'aikata albashin da 'bai taka kara ya karya ba' a Borno
  • An kama ɗaliban da ke zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Amurka
  • Mutum 24 sun mutu a China sanadiyyar zaftarewar titi
  • An yi artabu tsakanin ɗalibai masu goyon baya da masu ƙin jinin Falasɗinawa
  • Ya kamata a daɗaɗa wa ma'aikatan Najeriya - Tinubu
  • Ƙungiyoyin ƙwadago sun yi fatali da ƙarin albashin ma'aikata a Najeriya

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi, Buhari Fagge

  1. Akwai 'yan fanshon da ke karɓar 4,000 a wata a Borno - NLC

    Ƙungiyar 'yan kwadagon Najeriya reshen jihar Borno ta ce wasu mutanen da suka yi ritaya a jihar har yanzu ana biyansu dubu hudu a matsayin kuɗin fanshonsu a wata.

    Shugaban ƙungiyar Mista Yusuf Inuwa ne ya bayyana haka yayin bayanin da ya gabatar a bikin ranar ma'aikata na 2024 wanda aka yi a jihar Borno.

    Ya nemi a sake duba yadda za a kyautata kudin da ake biya domin faranta rayuwar 'yan fanshon.

    "Muna miƙa ƙoƙon bararmu gabanka mai girma gwamna kan wasu 'yan fansho da har yanzu ake bai wa naira dubu hudu kowanne wata a matsayin kudin fansonsu, kuma babu shakka wadannan kudi ba za su isa ba.

    "Muna roko da gwamna ya shiga wannan lamari ta yadda za a sake duba abin da ake biyansu", kamar yadda shugaban ya roƙa.

  2. Timo Werner ba zai sake buga wasa a Premier ba

    A tattaunawar da ya yi da manema labarai a yau, kocin Tottenham Ange Postecoglou ya yi ƙarin haske kan raunin da dan wasan ƙungiyar ɗan kasar Jamus Timo Wener ya ji.

    Ya ce ɗan wasan zai yi jinyar makonni biyu da rabi ne kawai, wanda hakan na nufin ba zai buga sauran wasannin Premier ba.

    Dan wasan mai shekara 28 na zaman aro ne a Spurs daga RB Leipzig tun daga watan Janairu, kuma ya ci kwallo biyu cikin wasan 13 daya buga a Premier.

    "Shi ma Ben Davies na fama da matsala a gwiwarsa zai yi jinya kuma watakila shi ma ya gama wasannin kakar bana.

    "Bayan su dai kowa yana nan ƙalau. Skipp zai dawo shi kuma Richarlson ya fara warwarewa sosai. Yana buƙatar wasu 'yan wasanni ne kaɗan."

  3. Gidaje sun yi yawa a Japan, sama da miliyan hudu babu kowa cikinsu

    Alkaluman gwamnatin Japan sun nuna cewa kasar na da gidaje kusan miliyan hudu da aka yi watsi da su, yayin da raguwar yawan jama'a ke rage bukatar gidaje.

    Gidaje da dama na nan babu kowa a cikinsu, tun bayan mutuwar tsofaffin da ke zaune a ciki.

    Akwai ma gidaje da dama da yanzu haka suka lalace ciki kuwa har da na magada, sabida rashin bukatarsu.

    Yanzu haka dai adadin gidajen da babu kowa a cikinsu a Japan ya kai miliyan tara.

  4. Tanzania da Kenya sun daidaita kan rikicin cinikin kajin da ke tsakaninsu

    Tanzania da Kenya sun samu nasarar shawo kan dogon rikicin da ke tsakaninsu na ciniki da kiwon kaji, kamar yadda wata sanarwa da East African Community (EAC) ta fitar a ranar Talata.

    Sanarwar ta ce an shawo kan matsalar ne sakamakon wata tuntuba da aka yi ta kwana biyu a hedikwatar kungiya da ke Arysha a arewacin Tanzania.

    Shugaban taron Rabson Wanjala ddaga Kenya shi ne ya wakilci ambasadan Kenya a Tanzania, yace duka ƙasashen biyu sun dauki aniyar alaƙar ciyar da kasuwancinsu gaba, yana cewa alaƙarsu za ta taimakawa burinsu na ciyar da kasuwancinsu gaba.

    Muƙaddashin Darakatan Ma'aikatar da ke lura da harkokin kiwo a Tanzania, Benezeth Lutege Malinda ya ce Tanzania ta shawo kan matsalolin kasuwanci da take fuskanta, kuma hukumomin na ta mayar da hankali kan kasuwanci musamman wanda babu kudin ruwa a ciki.

    A 2018, Tanzania ta kona kaji 5,000 da take zargin an shiga da su ƙasar daga iyakar arewaci tsakaninta da Kenya.

  5. Dortmund ta jefa kwallo ɗaya a ragar PSG, Dortmund 1-0 PSG

    Dortmund ta jefa kwallo ɗaya a ragar PSG ta hannun Niclas Fullkrug a minti na 35 da fara wasa.

    Tun farkon wasan su ke jan ragamar wasan tare da kai hare-hare masu dama ga PSG.

  6. 'Sai an ba mu lokacin saboda matasan 'yan wasan da muka tara'

    Kocin Chelsea Mauricio Pochettino ya ce akwai buƙatar a bashi ƙarin lokaci saboda matasan 'yan kwallon da ya tara fal a ƙungiyar.

    Kocin ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a taron manema labarai, lokacin yake nuna farin cikinsa kan canjaras ɗin da ya yi da Aston Villa a wasansa na ƙarshe da aka tashi 2-2.

    "Abubuwan duka na koyo ne, dan haka koyo sai an baka lokaci.

    "Muna buƙatar wannan kwarewar da kuma koya daga wajen kwararru. kalubale ne na kowa da kowa, babu sauki samun wadannan matasan 'yan wasan a wannan lig din mafi wuya a duniya."

    An tambaye shi yayi saurin koyon da suke yi lokacin da ake nuna musu lamura.

    Pochettino sai ya ce " Ba shakka duk da wannan tashi faɗin da ake fama da shi amma suna ƙoƙari. Koyo suke kuma koyo abu ne da ke ɗaukar lokaci".

  7. Yadda aka yi arangama tsakanin 'yansanda da masu zanga-zanga a Turkiyya

    'Yan sanda a Istanbul sun harba barkonon tsohuwa da harsasai na roba a kokarin da suke yi na hana mutane gudanar da wani gangamin taron ranar 1 ga watan Mayu.

    An rufe dandalin Taksim da ke tsakiyar kasar, inda shugaban kasar Turkiyya ya yi gargadi kan abin da ya kira tada hankali.

    Sai dai masu zanga-zangar sun yi yunkurin kawar da shingayen, lamarin da ya kai ga yin arangama da 'yan sanda a can da sauran yankunan birnin.

    Rahotanni sun ce an kama akalla mutane dari da hamsin.

    Shugaban babbar jam'iyyar adawa ta kasar, CHP, ya ce za su ci gaba da fafatawa, har sai sun ‚yanta kasar

  8. Blinken ya tattauna da Netanyahu

    Babban jami'in diflomasiyyar Amurka, Antony Blinken ya gana da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da wasu manyan jami'an gwamnatin kasar a birnin Kudus a rana ta karshe ta ziyararsa a Gabas ta tsakiya.

    An fahimci cewa tattaunawar ta mayar da hankali ne kan batun shigar da kayan agaji Gaza, da kuma sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta da ake jiran Hamas ta yi martani kanta.

    Mista Blinken ya ce ya kuduri aniyar ganin an kulla yarjejeniya don sako mutanen da aka yi garkuwa da su, sai dai abun da ke hana hakan shi ne Hamas.

    Masu shiga tsakani na jiran martanin kungiyar Hamas kan sabuwar yarjejeniyar tsagaita bude wutar da aka mika masu, wadda aka rawaito cewa ta kunshi tsagaita wuta na kwana 40, da sakin fursunonin yakin Isra'ila 33, da kuma sakin Falasdinawa.

    Jiya Talata ne Netanyahu ya ce Isra'la za ta kai hari Rafah ko Hamas ta amince ko ba ta amince ba.

  9. Muna so a binciki El-Rufai kan korar ma'aikata 27,000 da ya yi - PDP

    Jam'iyyar hamayya ta PDP jihar Kaduna da ke warewacin Najeriya ta bai wa kwamitin da Majalisar jihar ta kafa domin binciken kashe-kashen kudaden da gwamnatin El-Rufai ta yi, da ya binciki tsohon gwamnan kan korar ma'aikata 27,000 da ya yi a faɗin ƙasar ba tare da biyansu haƙƙoƙinsu ba.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa cikin wata sanarwa da Sakataren hulɗa da jama'a na Jam'iyyar Abraham Alberah Catoh ya fitar, ta ce, PDP ta yi watsi da abin da ta kira 'lalata aikin gwamnati' a jihar Kaduna.

    Catoh ya bayyana haka a yayin bikin Ranar Ma'aikata ta 2024, inda ya ce jam'iyyar a ko da yaushe na nuna goyon bayanta ga ma'ikata kan juriya da yadda suke gudanar da ayyukansu a Najeriya baki daya.

    "Muna kira ga kwamitin da Majalisar Jihar Kaduna ta kafa da zai yi bincike kan El-Rufa'i da ya sake fadada bincikensa har zuwa kan korar ma'aikata 27,000 da aka yi bisa rashin adalci a fadin jihar ba tare da an biya su hakkokinsu ba, kuma wannan 'nuna halin ko in kula ne ga aikin gwamnati," kamar yadda yake cikin sanarwar.

  10. 'Da gangan Isra'ilawa ke kashe fararen hula'

    Wani dan kasar Lebanon da aka tilasta wa barin gidansa da ke kudancin kasar ya zargi Isra'ila da kai wa fararen hula hari da gangan - zargin da Isra'ilawan suka musanta.

    Ya ba da labarinsa ga wakiliyar BBC wanda ya yi nasarar samun damar shiga kudancin Lebanon, wata dama da ba kasafai ake samunta ba.

    Ta bayyana ganin yadda ake lalata wurare a yankin da aka kashe fararen hula sama da 70 tare da tada kauyuka ko kuma aka yi watsi da su tun lokacin da aka fara yakin Gaza.

    Hakan ya biyo bayan musayar wuta da ake yi a kusan kullum a kan iyakar kasar da mayakan Hizbullah da sojojin Isra'ila.

    Dubun dubatar mutane ne aka tilasta wa barin gidajensu a bangarorin biyu na kan iyaka.

  11. Burina halartar gasar Turai - Emery

    Kocin Aston Villa Unai Emery ya ce ba shi da wani babban buri bayan ganin ya kai Ƙungiyarsa ta Aston Villa zuwa gasar Zakarun Turai.

    Unai na cikin kungiyoyi hudu na saman teburin gasar Premier, yana bin bayan Liverpool da ke matsayi na uku da maki 67.

    "Muna farin ciki da kofin da muke bugawa na Conference, ƙoƙarinmu na Premier ne ke ƙara mana kwarin gwiwa.

    "Hakan kuma bai sauya sakona na farko ba, cewa wasannin 38 na Premier sune mafiya muhimmanci a wurina - sai mu ƙara da FA da Carabao da kuma shi kan shi Conference ɗin," in ji Unai.

    Wannan ne karon farko da Villa ta halarci wasan kusa da na ƙarshe a wata gasar Turai tun 1982.

    Shekara mai zuwa kuma da yiwuwar ƙungiyar ta halarci gasar Champion Lig.

  12. Cutar da ke sa ana yanke wa mazan Brazil mazakuta

  13. Magajin garin Los Angeles ya yi Allah-wadai da tashin hankalin da aka samu

    An samu yamutsi tsakanin masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa da kuma masu wata zanga-zangar ta boyon bayan Isra'ila a jami'an California da ke Amurka.

    Bidiyon da aka yada a Internet ya nuna yadda masu zanga-zangar goyon bayan Isra'ila ke jifan masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa, bayan sun lalata shingayen da aka kafa musu.

    Kazalika an ga yadda suke dukan wani mutumi da ke dauke da tutar Falasdinu.

    Magajin garin Los Angeles, ya yi Allah-wadai da tashin hankalin, yana mai cewa abin kyama ne da ba za a lamunta ba.

  14. Mun kai samame Jami'ar Columbia don dawo da zaman lafiya - Yan sanda

    Ana ta mayar da martani kan samamen da 'yan sanda suka kai kan daliban jami'ar Columbia da suke zanga-zanga, yanzu kuma magajin gari da 'yan sandan New York sun ce "sun kai samamen ne domin dawo da doka da oda".

    Shugaban 'yan sandan New York Edward Caban ya ce yanayin jami'ar ya jefa al'uma cikin haɗari.

    Ya tabbatar da kama mutum 300 yayin wani samame da suka kai da daddare a jami'ar.

    Kakakin 'yan sandan ya ce masu ziga daga ƙasashen ketare na taka rawa wajen rura wutar rikicin Jami'ar.

    Yadda daliban suka sanya shingen hana 'yan sandan shiga wajen kwanansu ya nuna cewa wani ne ya koya musu wannan dabarar.

  15. Tarihin haɗuwa tsakanin Dortmund da PSG a Champions Lig

    Wato dukkansu ba wani tarihin azo a gani ba ne da su a wannan gasar.

    Wannan ne karo na hudu da Dortmund take kai wa irin wannan matsayi a gasar zakarun Turai, kuma a guda biyu ta je wasan karshe, su ne a 1996/97 sai kuma 2012/13 wanda suka yi da takwarata ta Jamus Bayern Munich.

    An cireta a guda daya a 1997/98 wanda Real Madrid ta cinye ta.

    Ita kuma PSG ta je wannan matsayin sau hudu a tarihi ta yi rashin nasara gida da waje a shekarar 1994/5 da AC Milan,Sai wanda ta yi a hannun Man City a 2020/21.

    An yi haduwa shida tsakanin Dortmund da PSG a tarihi, kuma Dortmund wasa daya ta taba samun nasara a kann PSG shi ne a duka gasar turai da suka taba haduwa, amma a Champions Lig a 2019/20, ta samu nasara sau daya da ci 2-1, kafin a dawo wasa na biyu a cire ta daga gasar da ci 3-2….

    Sun yi canjaras 3, ta yi kuma rashin nasara sau biyu a hannun PSG.

  16. Ƙungiyoyin ƙwadago sun yi fatali da ƙarin albashin ma'aikata a Najeriya

    Ƙungiyar ƙwadago ta TUC a Najeriya ta yi watsi da ƙarin albashin da gwamnatin tarayyar ƙasar ta sanar a ranar Talata, kwana ɗaya gabanin bikin ranar ma'aikata ta duniya.

    A jiya ne wata sanarwa wadda ta samu sa hannun shugaban hukumar kula da albashin ma'aikata ta Najeriya, Ekpo Nta, ta bayyana cewa an yi ƙarin kashi 25 zuwa 35 cikin ɗari a kan albashin ma'aikatan gwamnati.

    Hakan ya nuna cewa mafi ƙarancin albashi zai koma kimanin naira 37,000 daga naira 30,000 da ake da shi a baya.

    Sai dai a tattaunawar sa da BBC, sakataren ƙungiyar ƙwadago ta TUC, kwamared Nuhu Abbayo Toro ya ce ba da sanin ƙungiyoyin ƙwadago aka yi ƙarin albashin ba kuma ba su amince da shi ba.

    Toro ya ce "abin da dokar ƙasa ta ce shi ne sai an zauna an tattauna an yi yarjejeniya an samu matsaya kafin a amince da albashi mafi ƙanƙanta".

    Ya ƙara da cewa "ba daidai ba ne shugaban ƙasa ya furta cewa ya yi ƙarin albashin ma'aikata alhali akwai kwamitin da ke aikin samar da sabon albashi mafi ƙaranci".

    Shi ma shugaban ƙungiyar ƙwadago ta NLC, Joe Ajaero a wata tattaunawa da kafar talabijin ta Channels da safiyar Talata ya ce "sanarwar da aka bayar an yi ta ne da wata manufa domin kuwa babu wani ƙarin albashi da aka yi".

    A watan Janairu ne Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ƙaddamar da wani kwamiti wanda zai duba tare da yanke shawara kan ƙarancin albashin ma'aikata a ƙasar.

    An ɗauki matakin ne bayan barazanar da ƙungiyoyin ƙwadago na ƙasar suka yi kan cewa za su tsayar da lamurra cak a ƙasar har sai gwamnatin tarayya ta samo mafita game da matsin rayuwa da ma'aikatan ƙasar ke fuskanta.

    Al'ummar Najeriya na fuskantar tashin farashin kayan masarufi tun bayan da shugaban ƙasar ya sanar da janye tallafin man fetur da gwamnati ke bayarwa a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

  17. Ya kamata a daɗaɗa wa ma'aikatan Najeriya - Tinubu

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce akwai buƙatar ganin an kyautata wa ma'aikata a Najeriya ta hanyar biyan su albashin da ya dace da kuma inganta walwalarsu.

    Shugaban ya bayyana haka ne a cikin saƙon da ya fitar na taya murnar ranar ma'aikata ta duniya, wanda ake gudanarwa a ranar ɗaya ga watan Mayu na kowace shekara.

    Bukin ranar ma'aikatan na zuwa ne a lokacin da ma'aikatan Najeriya ke kokawa kan tsananin rayuwa sanadiyyar tashin farashin kayan masarufi da kuma zubewar darajar kuɗin ƙasar.

    A cikin saƙon shugaba Tinubu, wanda ya fitar ta hannun mai taimaka masa kan harkar yaɗa labaru, Ajuri Ngelale, ya ce ba wai kawai albashin ma'aikata ya kamata a inganta ba, har ma da kayan aiki.

  18. An yi artabu tsakanin ɗalibai masu goyon baya da masu ƙin jinin Falasɗinawa

    An samu hatsaniya a jami'ar University of California da ke Amurka tsakanin masu zanga-zangar nuna goyon baya da kuma masu ƙin jinin Falasɗinawa.

    Lamarin ya faru ne lokacin da gungun masu zanga-zangar goyon bayan Isra'ila ne suka rika yin jifa da turakun da aka sanya domin killace masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa.

    Bidiyon da aka yaɗa ya nuna yadda ɓangarorin biyu suka riƙa jifan juna da tartsatsin wuta.

    Haka nan bidiyon ya nuna yadda aka lakaɗa wa wani mutum sanye da rigar nuna goyon baya ga Falasɗinawa duka.

    Daga baya ƴansanda sun samu shiga tsakanin masu husumar.

    Zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasɗinawa na ci gaba da yaɗuwa a jami'o'in Amurka.

    Sama da mutum 1000 ne aka kama cikin mako biyu sanadiyyar zanga-zangar.

    Kalli yadda aka yi artabun a ƙasa:

  19. Mutum 24 sun mutu a China sanadiyyar zaftarewar titi

    Mutum 24 ne suka mutu a China bayan yankwar wata babbar hanya da ke lardin Guangdong na kudancin ƙasar.

    Wani ɓangare ne na titin da ke kusa da wani tudu ya zaftare, lamarin da ya haifar da mummunan hatsari.

    Faifan bidiyo ya nuna tarin motoci da suka afka cikin katoton ramin da ya buɗe bayan zaftarewar ɓangaren titin.

    Babu tabbas kan ko mamakon ruwan da aka tafka a cikin makwannin da suka gabata a yankin kudancin China ne ya raunana turakun babbar hanyar.

    An kai gwamman mutane asibiti inda suke samun kulawa sanadiyyar raunuka da suka samu.

  20. An kama ɗaliban da ke zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Amurka

    Daruruwan jami'an ƴansanda ne suka mamaye jami'ar Columbia da ke birnin New York na Amurka, domin tarwatsa masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa.

    Wasu hotuna sun nuna yadda ƴansanda ke amfani da kwaranga wajen dirar wa ɗalibai a cikin makarantar. Tun da farko, jami'ar ta gargadi ɗaliban makarantar kan su dakatar da zanga-zangar ko su fuskanci hukuncin kora.

    An ga yadda ƴansandar suka yi awon gaba da wasu daga cikin masu zanga-zangar.