Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 9 ga watan Satumba, 2025.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Isiyaku Muhammed da Aisha Babangida

  1. Habasha za ta ƙaddamar da tashar lantarki mafi girma a Afirka bayan shekara 14 ana aikinsa

    Kasar Habasha za ta kaddamar da wani babban dam da aka gina a kan kogin Nilu bayan shafe shekaru goma sha hudu ana aikin.

    Babbar madatsar ruwa ta Habasha, wacce za ta kasance tashar samar da wutar lantarki mafi girma a Afirka.

    Tasha ce za ta riƙa samar da wuta mai karfin wutar lantarki fiye da megawatt 5000.

    Aikin kogin dai ya haifar da rikicin diflomasiyya domin Sudan da Masar sun kasance suna adawa da aikin.

  2. Firaiministan Faransa na dab da murabus

    Firaiministan Faransa, Francois Bayrou na dab da yin murabus bayan rasa yin rinjaye a kuri'ar yankan kaunar da aka kada a majalisar dokokin kasar a jiya Litinin.

    Yana dai son ya rage kudaden da ake kashe wa al'ummar kasar ne domin magance bashin da kasar ke fama da shi, to amma ya rasa samun cikakken goyon baya akan hakan.

    Murabus din nasa zai jefa kasar cikin rikicin siyasa inda a yanzu doke shugaba Emmanuel Macron ya nada sabon firaiministansa karo na bakwai tun bayan da hau mulki a shekarar 2017.

  3. Syria ta zargi Isra'ila da kai mata hare-hare

    Kafar yada labaran Syria ta ce Isra'ila ta kaddamar da hare-hare ta sama a wasu sassa na tsakiya da kuma yammacin kasar.

    Rahotanni sun ce an kai hare haren ne a kusa da Homs da Palmyra da kuma birnin Latakia da ke gabar ruwa.

    Ana ganin Isra'ilan ta kai hare-haren kan sansanonin Soji ne.

    Ba a bayar da rahoto akan mutanen da hare haren ya shafa ba, haka ita ma Isra'ilan ba ta ce komai a kan harin ba.

    Isra'ila dai na kai hare-hare ta sama tun bayan hambarar da gwamnatin shugaba Bashar al- Assad a watan Disambar bara.

  4. Buɗewa

    Jama'a barkanmu da safiya daga nan sashen Hausa na BBC. A yau ma za mu ci gaba da kawo muku labaran abubuwa da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Ku kasance tare da mu.