Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 29/11/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 29/11/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Umar Mikail

  1. 'EFCC ta sallami Abubukar Malami bayan yi masa tambayoyi'

    Tsohon Ministan shari'ar Najeriya, Abubakar Malami, SAN ya ce hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci ta sallame shi bayan ya amsa wasu tambayoyi da hukumar ta gayyace shi domin samun amsarsu.

    Cikin wata saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, jim kaɗan bayan fitowa daga ofishin hukumar, Malami ya ce yana gode wa Allah da ya ba shi ikon kammala amsa tambayoyin hukumar lafiya.

    Tsohon ministan shari'ar ya kuma ce ganawar tasa da jami'an EFCCn ta kasance mai kyau.

    Sai dai ya ce hukumar ta sake sanya wani lokaci domin ya sake halarta ofishinta domin ci gaba da ganawar.

  2. An ci gaba da juyayin rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi a Najeriya

    Ana ci gaba da juyayi da alhinin rasuwar fitaccen malamin addinin musuluncin nan na Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi wanda aka yi jana'izarsa ranar Juma'a a birnin Bauchi.

    Dubban mutane daga ciki da wajen Najeriya ne suka halarci jana’izarsa inda aka yi masa sallah a masallacin Idi na garin Bauchi kafin a binne shi a masallacinsa.

    Shiekh Khalid Muhammad wanda ya zo daga jamhuriyar Nijar na cikin waɗanda suka halarci jana’izar ya kuma ce shehin malamin ya bar abubuwan da ba za a manta da shi ba a rayuwa.

    ''Ya assasa abubuwa na alkairi da har duniya ta tashi za a ci gaba da tunawa da shi'', in ji shi.

    Ya ƙara da cewa za a riƙa tuna malamin da tsayuwarsa ga addini da taimakon da yake yi wa bayin Allah, da kuma ƙoƙarin wanzar da zaman lafiya.

    Malamin mai shekara 100 ya rasu ne ranar Alhamis a wani asibitin sojoji bayan fama da jinya.

  3. Sallama

    Masu bin shafinmu na BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Asabar.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Kuna iya bibiyarmu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.