Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 08/01/2025.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed, Abdullahi Bello, Usman Minjibir, da Umar Mikail

  1. Dubban mutane sun tsere daga Los Angeles saboda wutar daji

    An sanya dokar ta-ɓaci a birnin Los Angeles na jihar California sakamakon wata gagarumar wutar daji da ta tashi a birnin, inda ta tilasta kwashe mazauna wani yanki na masu hali a tsaunukun kusa da gaɓar tekun Pacific.

    Yaɗuwa wutar ce ta sa hukumar kashe gobara ta California ta yi gargaɗin cewa akwai matsala a cigaba da zama a yankin.

    Hakan ya sa hukumomi a yankin suka yi kira ga aƙalla mutum 30,000 da ke zaune a yankin da su bar gidajensu, domin komawa yankunan da suke da aminci zuwa wani lokaci.

  2. An kusa fara biyan masu yi wa ƙasa hidima alawus na naira 77,000 — NYSC

    Gwamnatin Najeriya ta ce an kusa fara biyan masu yi wa ƙasar hidima alawus na naira 77,000 da aka amince za a riƙa biyansu na wata-wata.

    Darakta-janar na NYSC, Birgediya Janar YD Ahmed ya bayyana haka a ranar Talata a wata sanarwa da kakakin NYSC, Caroline Embu ta fitar kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

    Ahmed ya ce zai mayar da hankali kan jin daɗin masu yi wa ƙasa hidima, inda ya ƙara da cewa tuni shirye-shirye sun kammala domin fara biyan sabon alawus ɗin.

    An dai ƙara alawus ɗin ne tun bayan da gwamnatin Najeriya ta ƙara mafi ƙarancin albashin ma'aikata a ƙasar.

  3. 'Babu tabbacin ana samar da ƙwayar fentanyl a Mexico'

    Shugaban Ƙasar Mexico ya ce ba a gano wata ƙwaƙƙwarar shaida mai ƙarfi da za ta tabbatar da samar da muguwar ƙwayar fentanyl a ƙasar.

    Ana ganin ƙwayar fentanyl dai ta fi hodar iblis haɗari, kuma ta yi ajalin dubun dubatar Amurkawa, wani yanayi da ya sanya jakadan Amurka mai barin gado a Mexico ya yi zargin a ƙasar ake samar da ita.

    Sai dai shugaba Claudia Sheinbaum ta ce babu shaidar tabbatar da zargin nasa, a ɓangare guda kuma hukumomin Mexico sun sanar da ƙwace miyagun ƙwayoyi a ƙasar.

    Zaɓaɓɓen shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar ƙara harajin kashi 25 cikin 100 kan duk wasu kayayyaki da ƙasar ke fitarwa, matuƙar ba ta magance matsalar kwararar ƴan-cirani da ƙwaya ba.

  4. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Laraba daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta irin su X da Facebook da Instagram domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo.

    Ku kasance tare da mu.