Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da makwabtanta da sauran sassan duniya kai tsaye

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Annur Muhammad

  1. Shugaban Dimokuradiyyar Kongo ya zargi wanda ya gada da goyon bayan ƴantawaye

    Shugaban Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ya zargi wanda ya gada Joseph Kabila, da goyon bayan ƴantawaye a gabashin kasar.

    A wata hira, Felix Tshisekedi ya zargi tsohon shugaban wanda ya kaurace wa zaben bara da shirin tayar da kayar baya.

    Ya yi wannan ikirarin ne bayan ƴantawayen M23 sun kwace ikon wani gari da ke kusa da kan iyaka da Uganda jim kadan kafin yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma da sojojin Kongo ta soma aiki.

    Ita dai jam'iyyar Mista Kabila, People's Party for Reconstruction and Democracy, ta yi watsi da zargin.

    Duk da kokarin shiga tsakani da ake yi, rikici a yankin gabashi mai arzikin mai na ci gaba da kamari.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce sama da mutum miliyan bakwai aka raba da mahallansu sakamakon rikicin na fiye da shekara 10.

  2. Isra'ila ta nanata shirinta na kashe sabon shugaban Hamas

    Isra'ila ta nanata iƙirarin da ta yi a baya cewa tana shirin kashe Yahya Sinwar, mutumin da aka naɗa a matsayin sabon shugaban Hamas a Gaza.

    Ministan harkokin wajen ƙasar ya ce naɗa Sinwar muƙamin, wani babban dalili ne na halaka shi.

    Mista Sinwar ne yanzu ya gaji Ismail Haniyeh Isma'il Haniya wanda aka kashe a Iran a makon da ya gabata.

    Wakiliyar BBC ta ce nadinsa wani babban sako ne ga Isra'ila, wata 10 bayan yaƙi mafi muni a Gaza inda Isra'ila ta zargi Sinwar da kitsa harin ranar bakwai ga watan Oktoba inda aka kashe mutum 1200 tare da yin garkuwa da wasu da dama.

    Tuni kungiyar Hezbollah ta aika wa Simwar da sakon taya murna kan sabon mukaminsa

  3. Nijar ta yanke hulɗar diflomasiyya da Ukraine

    Jamhuriyar Nijar ta sanar da yanke duk wata huldar diflomasiya da kasar Ukraine.

    Kakakin gwamnatin sojin Nijar, Amadou Abdramane ya zargi gwamnatin ta Ukraine da goyon bayan kungiyoyin ƴanta'adda.

    Ita ma Mali ta sanar da irin wannan matakin kwana biyu da suka gabata - inda ta zargi Ukraine ta taimaka wa ƴantawaye wajen kisan sojojin kasar da dama a watan da ya gabata.

    Sai dai Kiv ba ta fito fili kai-tsaye ta amince cewa tana da hannu a hare-haren na mayaka da 'yantawayen Abzinawa suka kai ba, inda aka kashe har da sojojin hayar Rasha.

    Nijar da Mali da Burkina Faso da dukkaninsu sojoji ke mulki, sun karfafa alaka da Rasha yayin da suke fama da matsalar mayaka masu da'awar jihadi.

  4. Hukumar kula da ilimin almajirai ta nuna damuwa kan shigar yara zanga-zanga a Najeriya

    Hukumar kula da ilimin almajirai da yara masu gararanba a titi ta Najeriya ta nuna rashin jin dadinta kan yadda yara kanana suka shiga zanga-zangar matsin rayuwa da ake yi a kasar.

    A wata sanarwa da ta fitar hukumar ta ce duk da cewa zanga-zangar 'yanci ne da jama'a suke da shi na su bayyana ra'ayinsu to amma ta ce bai dace ba a jefa rayuwar yara cikin hadari ta hanyar barinsu shiga wannan zanga-zanga.

    Sakataren zartarwa na hukumar Dr Muhammad Sani ya ce, ganin yadda yara, wadanda ya kamata a ce suna makaranta, da kuma kila ba sa zuwa makarantar suke shiga zanga-zangar musamman a arewacin kasar hakan ya nuna irin gagarumin aikin da ke gabansu.

    Ya ce ganin yadda zanga-zangar take rikidewa ta zama tarzoma hakan ba karamin hadari ba ne ga yaran kuma tamkar ci da guminsu ne.

    A don haka shugaban ya yi kira ga iyaye da masu kula da 'ya'ya da yaransu, sannan su rika bayar da fifiko ga lafiya da rayuwarsu.

  5. Buɗewa

    Jama'a masu bibiyarmu a wannan shafin da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da maƙwabtanta da sauran sassan duniya kai tsaye, muna muku maraba a wannan safiya ta Laraba ta Bawa ranar samu.

    Ni Muhammad Annur Muhammad zan kasance da ku daga yanzu zuwa wani lokaci a nan gaba. A yi jimirin kasancewa da mu.

    Mu fara da wannan karin maganar - Duk abin da aka yi wa tuwo sai gara ta rama masa