APC ta fara sayar da fom na zaɓukan cike giɓin ƴan majalisu
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta fara sayar da fom na takarar zaɓukan cike gibi na ƴan majalisu dokokin ƙasar.
A makon da ya gabata ne hukumar zaɓen ƙasar INEC ta saka ranar 16 ga watan Agusta mai zuwa domin gudanar da zaɓukan cike giɓin ƴan majalisun dokokin ƙasar.
Ana gudanar da irin wadannan zaɓuka domi cike guraben ƴan majalisun da suka mutu ko suka sauka daga kujerun saboda wani dalili.
Hukumar zaɓen ta ce za a gudanar da zaɓukan ne a jihohin ƙasar 12.
Tuni dai ƴan jam'iyyar ta APC suka fara zuwa sakatariyar jam'iyyar domin sayen fom na takarar.
Jam'iyyar ta APC ta saka ranar 16 ga watan Yulin da muke ciki a matsayin ranar gudanar da zabukan fitar da gwani na waɗannan kujeru.