Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 03/07/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Usman Minjibir da Aisha Babangida

  1. Jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji 65 ya nutse a Indonesia

    Wani jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji sittin da biyar ya nutse a kusa da tsibirin Bali na kasar Indonesiya.

    Aƙalla mutane ashirin da uku ne aka ceto yayin da aka gano gawarwakin mutum hudu.

    Jirgin na hanyar zuwa Bali ne daga Ketapang a Gabashin Java lokacin da ya nutse.

    Jami'an tawagar aikin ceto sun bayyana cewa jirgin ya fuskanci matsalar inji gabannin nutsewarsa.

    Rashin kyakyawan yanayi dai na kawo cikas a aikin ceton da ake gudanarwa

  2. 'Abin da ya sa muka zaɓi ADC a matsayin jam'iyyar haɗaka'

    A ranar Laraba ne manyan ƴan adawar siyasa na Najeriya suka tabbatar da amincewa da jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) a matsayin wadda za su yi aiki da ita domin tunkarar zaɓen 2027.

    Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, wanda jigo ne a haɗakar ya ce: "mun kwashe wata tara zuwa shekara ɗaya muna tattaunawa domin ganin yadda za mu haɗa kanmu mu shiga jam'iyya ɗaya da ba za a iya soke rajistarta ba, mu gyara jam'iyyar da shugabancinta da aƙidarta da fito da tsarin da zai ceci ƙasarmu daga wannan hali da aka shiga."

    Hakan na zuwa ne bayan yunƙuri daban-daban da ƴan adawar suka yi na ganin sun samar da ƙwaƙƙwarar adawa da za su iya tunkarar shugaban ƙasar mai ci Bola Ahmed Tinubu, wanda suke zargi da gazawa a mulkinsa.