Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya 30/03/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 30 ga watan Maris 2026.

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Haruna Kakangi

  1. 'Iran ta fara jerin hare-harenta na 87 kan mafakar sojin Amurka da Isra'ila'

    Rundunar juyin juya halin Iran (IRGC) ta bayyana cewa ta fara jerin hare-haren makamai da jirage marasa matuki karo na 87 kan maɓoyar sojojin Amurka da Isra’ila da cibiyoyin su.

    A cikin sanarwar da rundunar ta fitar, ta ce dakarunta sun kai hari kan “cibiyoyin kula da zirga-zirgar jiragen Amurka a UAE da wurin ma’ajin kayan makamai da moɓoyar sojojin Amurka da Isra’ila ciki har da “tsofaffin sansanonin Amurka guda biyar da kuma cibiyoyin soji a kudanci da tsakiya da arewa.”

    Sanarwar ta ƙara da cewa dakarun Iran ɗin sun kai hari kan wuraren Isra'ila da suka haɗa da “Haifa Bay, da Kiryat Shmona da Tel Aviv da Beersheba da Dimona da Al-Kharj da Juffair, da kuma Victoria.”

    Sanarwar ta ce "rundunar ta fara wannan jerin hare-haren ne tun farkon daren jiya kuma har yanzu yana ci gaba.”

    IRGC ta bayyana cewa wannan gagarumin hari an aiwatar da shi ne da “makaman masu linzami da suka haɗa da Imad, Qiyam, da Khorramshahr 4 da kuma jiragen sama marasa matuka.

  2. Gawuna ya ajiye muƙamin da Tinubu ya ba shi

    Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano kuma ɗan takarar gwamnan Jihar na jam’iyyar APC a 2023, Nasiru Yusuf Gawuna, ya ajiye muƙaminsa na Shugaban Hukumar Gudanarwar bankin bayar da lamunin gidaje na Najeriya.

    Sanarwar da tsohon mataimakin gwamnan ya fitar ta nuna cewa ajiye aikin zai fara ne daga gobe Talata, 31 ga Maris, 2026.

    A cikin sanarwar, Gawuna ya ce "na ajiye aikin ne domin bin umarnin shugaban ƙasa da ya buƙaci duk mai riƙe da muƙamin siyasa kuma yake son yin takara, ya ajiye muƙami domin yin biyayya ga dokar zaɓe".

    A cikin wasiƙar ta Gawuna wadda ya tura wa Sakataren gwamnatin Tarayya, Gawuna ya nuna godiya ga shugaba Tinubu kan amincewa da shi da ya naɗa shi a matsayin shugaban Hukumar Gudanarwar bankin bayar da lamunin gidaje na Najeriya.

    A makon da ya gabata ne aka yi ta raɗe-raɗin cewa tsohon mataimakin gwamnan, wanda ake wa kallon na hannun damar tsohon shugaban jam'iyyar APC ne ƙasa, Abdullahi Ganduje, cewa zai fice daga jam'iyyar APC, wadda ya yi takarar gwamna ƙarƙashinta a 2023.

    A watan Janairun 2024 ne kotun ƙolin Najeriya ta ayyana Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kano duk kuwa da cewa a watan Satumban 2023 kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen jihar Kano ta ayyana Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

    Tun farko hukumar zaɓen Najeriya ta ayyana Abba Kabir a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar ta Kano da aka yi a watan Maris ɗin 2023, inda ya samu ƙuri'u 1,019,602, yayin da Nasiru Gawuna ya zo a matsayi na biyu da ƙuri'u 890,705.

  3. 'Iran na shirin kafa sabon tsarin kula da Mashigar Hormuz'

    Iran ta bayyana shirin kafa sabon tsarin da zai kula da Mashigar Hormuz, wanda Majalisar Dokokin ƙasar za ta amince da shi cikin gaggawa, in ji ɗan majalisa, Alaeddin Boroujerdi.

    Alaeddin Boroujerdi ya ce "A ƙarkashin wannan sabon tsarin, ba za a ba kowanne jirgi damar wucewa ba sai da izinin Iran."

    Haka zalika, Boroujerdi ya ce Iran na shirin sanya haraji ga duk jiragen da ke wucewa ta mashigar.

    “Idan aka yi la’akari da tsaro da kuma samar da ayyuka ga jiragen da ke wucewa, akwai buƙatar a kafa tsarin karbar haraji na wucewa ta mashigar,” in ji shi.

    Ɗan majalisar ya kuma bayyana cewa “lokaci ya yi” da Iran za ta fice daga yarjejeniyar hana yaɗuwar makaman nulkiliya, inda ya ce yarjejeniyar ta rasa muhimmancinta bayan hare-haren da Isra’ila da Amurka suka kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran.

  4. Borno: Zulum ya sauke dukanin kwamishinoninsa

    Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya amince da sauke dukkan mambobin Majalisar Zartarwa ta Jihar nan take.

    Wannan matakin na zuwa ne domin samar da yanayi mai kyau ga duk wani memba da zai so tsayawa takarar muƙaman zaɓe a zaɓuɓɓukan gaba masu zuwa.

    Gwamna Zulum ya umurci dukkan kwamishinoni da su miƙa al’amuran ma’aikatunsu ga Sakatarorin Dindindin kafin ranar Jumma’a, 3 ga Afrilu, 2026.

    Wannan umurni zai tabbatar da cewa dukkan ayyuka da al’amuran gwamnati suna ci gaba da gudana ba tare da tangarda ba.

    A cikin sanarwar da ofishin Gwamnan ya fitar, Zulum ya yi godiya ta musamman ga kwamishinonin da suka sauka bisa sadaukarwa da jajircewa, da gudummawar da suka bayar wajen ci gaban jihar da hidimar al’ummar Borno.

    Ya bayyana cewa irin wannan himma ta taimaka matuƙa wajen ganin an samu cigaba a fannoni daban-daban na jihar.

    Sanarwar ta kuma tabbatar da cewa matakin zai bai wa duk wanda ke da burin takara damar mai da hankali kan shirin neman muƙaminsa cikin sauƙi.

  5. Mun kai hari kan cibiyoyin kula da zirga-zirgar jiragen Amurka a UAE - Iran

    Sojojin Iran sun bayyana cewa sun kai hari da jiragen sama marasa matuƙa kan cibiyoyin kula da zirga-zirgar jiragen Amurka da ke cikin Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).

    A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce daga daren jiya zuwa safiyar yau, an kai hare-hare kan na'urorin abokan gaba da ke UAE, waɗanda ke da alhakin gano da kuma daƙile makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa.

    Sanarwar ta kuma ƙara da cewa jiragen nasu sun kai hari kan wasu wurare da ke da alaƙa da sojojin Amurka a cikin ƙasar.

  6. Za mu kai hari kan gidajen jami’an Amurka da Isra’ila - Iran

    Hedikwatar Khatam al-Anbiya, wacce ita ce babbar cibiyar da ke kula da daidaita ayyukan rundunonin sojin Iran, ta yi barazanar kai hare-hare kan gidajen jami’an Amurka da Isra’ila da ke yankin.

    Mai magana da yawun hedikwatar, Ebrahim Zolfaghari, ya ce wannan mataki na ramuwar gayya ne inda ya zargi Amurka da Isra’ila da kai hare-hare kan gidajen fararen hula a birane daban-daban na Iran.

    A cewarsa, hare-haren da ake kai wa Iran sun haddasa asarar rayukan manyan kwamandojin soja da jami’ai a lokacin rikicin.

    Daga cikin waɗanda aka kashe har da Ali Khamenei, tsohon jagoran addinin Iran, wanda rahotanni suka ce an kashe shi a hare-haren hadin gwiwar Amurka da Isra’ila a ranar 28 ga Fabrairu, ranar farko ta barkewar yakin.

  7. Wace jam'iyya Kwankwaso zai koma bayan fitarsa daga NNPP?

    Tun bayan da tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sanar da ficewa daga jam'iyyarsa ta NNPP, masana da masu bibiyar siyasa ke ci gaba da hasashen jam'iyyar da zai koma.

    Cikin sanarwar ficewar ta sa, Sanata Kwanwaso ya ce matakin ya zama tilas ne la'akari da yanayin siyasar Najeriya ke ciki ''wanda ke bukatar haɗin kai''.

    ''Matakin ya zama tilas domin haɗa kai da wasu jam'iyyun don kawo wa ƙasarmu sauyi nagari'', kamar yadda Kwankwason ya bayyana.

    Tuni dai masana da masu sharhin siyasa suka fara bayayna hasashensu na inda Kankwason zai koma.

  8. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Litinin ga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.