Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 28/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 28 ga watan Yulin 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida, Haruna Kakangi da Muslim Muhammad Yusuf

  1. Trump da Netanyahu sun fara ganawa a Fadar White House

    Jim kaɗan bayan isowarsa Fadar White House, an fitar da hotunan ganawar Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da Shugaban Amurka Donald Trump.

    An kuma wallafa hotunan da ke nuna Netanyahu yana musabaha da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio, yayin da Sakataren Tsaro Pete Hegseth ke bayansu.

    Ana sa ran babban abin da shugabannin biyu za su tattauna shi ne batun Iran da kuma halin tsaron yankin Gabas ta Tsakiya.

  2. Netanyahu ya isa Fadar White House domin ganawa da Trump

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya isa Fadar White House, inda zai gana da Shugaban Amurka Donald Trump.

    Masu ɗaukar hoton kafafen yaɗa labarai sun ɗauki hotunan lokacin da Netanyahu ya isa fadar shugaban ƙasar.

    Ana sa ran babban abin da shugabannin biyu za su tattauna shi ne batun Iran, a daidai lokacin da ake ci gaba da takun-saƙa kan rikicin yankin.

    Bayan ganawar da Trump, Netanyahu zai halarci jana'izar Sanatan Amurka Lindsey Graham.

  3. Fararen hula da dama sun mutu a hare-haren sama a Kordofan

    Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta Sudan ta ce gwamman farar hula ne suka mutu a hare-hare ta sama da aka kai arewacin jihar Kordofan.

    Lauyan gaggawa na kungiyar da ke sa ido kan cin zarafin farar hula, ya ce jirage marassa matuka sun faɗa wata makaranta da cibiyar lafiya da motoci da wurin ajiyar ruwa, tsakanin 24 zuwa 26 ga watan nan.

    Hare-haren sun faru lokacin da sojojin gwamnatin Sudan ke gwabzawa da ƴan tawayen RSF a kusa da El-Obeid da su kai wa kawanya.

    Tuni sojojin suka sanar da karɓe ikon babbar hanyar da ta taso daga birnin Khartoum zuwa El-Obeid, wadda ƴan tawayen RSF ke iko da shi tun shekarar 2023 da yaƙin basasa ya ɓarke a ƙasar.

  4. Mutum huɗu sun mutu yayin da ƴansanda suka ceto mutum 32 a Sokoto

    Rundunar ƴansandan jihar Sokoto ta sanar da cewa mutum huɗu sun mutu bayan da wasu ’yanbindiga suka kai hari a ƙauyen Maikujera da ke ƙaramar hukumar Rabah a jihar Sokoto.

    Rundunar ta ce maharan sun kutsa yankin ne suna harbe-harbe tare da yin garkuwa da mutane da kuma satar dabbobi kafin jami’an tsaro su isa wurin.

    A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce jami'anta tare da haɗin gwiwar dakarun soji sun bazama yankin bayan samun kiran gaggawa cewa ’yanbindiga suna wucewa da shanu da suka sace tare da mutane da suka yi garkuwa da su inda suka toshe hanyoyin da ake zargin ’yan bindigar za su bi wajen tserewa.

    Hakan ya janyo musayar wuta mai tsanani tsakanin jami’an tsaro da maharan, lamarin da ya tilasta wa ’yan bindigar tserewa cikin daji tare da barin mutanen da suka yi garkuwa da su da kuma dabbobin da suka sace.

    Rundunar ta ce ta samu nasarar kuɓutar da mutum 32 da aka yi garkuwa da su ba tare da sun ji rauni ba.

    Waɗanda aka ceto sun haɗa da maza shida da mata 26, yawancinsu yara ne.

    Kwamishinan ƴansandan jihar, Hayatu Hassan Shaffa, ya miƙa sakon ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka mutu tare da jaddada cewa jami’an tsaro na ci gaba da farautar ’yan bindigar domin gurfanar da su a gaban kuliya.

  5. Uba Sani ya zaɓi mataimakinsa a zaɓen 2027

    Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya sanar da zaɓen mista Jerry Adams a matsayin mataimakinsa a zaɓen gwamnan 2027, bayan shawarwari da addu’o’i da ya ce sun jagoranci wannan mataki.

    A cikin wata sanarwa da gwamnan ya fitar a shafinsa na X, Uba Sani ya ce zaɓar Adams ya yi daidai da manufar gwamnatinsa ta haɗin kai, adalci da bai wa kowane ɗan jihar damar jin yana da muhimmanci a harkokin gwamnati, ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ba.

    Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi ƙoƙarin tabbatar da ci gaba a dukkan ƙananan hukumomin jihar tare da ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai tsakanin al’ummomi.

    Gwamnan ya yaba wa Jerry Adams a matsayin gogaggen jami’in gwamnati kuma ƙwararren mai kula da harkokin haraji, yana mai cewa mutumin ne mai gaskiya, ƙwazo da kishin zaman lafiya, wanda zai taimaka wajen ci gaba da gina Kaduna mai haɗin kai da ci gaba.

  6. Masu kashe gobara na ƙoƙarin shawo kan wutar dajin da ta bazu a sassan Faransa

    Masu kashe gobara a Faransa sun kwatanta ƙoƙarin da suke yi na shawo kan gobarar daji da ta bazu a sassan ƙasar da labarin gwabza yaƙi tsakanin David da Goliath da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki, saboda girman ƙalubalen da suke fuskanta.

    Mai magana da yawun hukumar kashe gobarar ya ce duk da yadda gobarar ke ci gaba da ƙaruwa da yaɗuwa, jami'ansu na samun nasarori ta hanyar amfani da sabbin dabaru wajen dakile ta.

    Gobarar dai ta tilasta wa sama da mutum dubu 250 barin gidajensu domin tsira da rayukansu.

    Wakilin BBC ya ce har yanzu ba a kammala aikin kashe gobarar da ke ci gaba da ƙone dazuka a yankin Bowdow ba.

    Wani jami'in kashe gobara ya bayyana cewa har yanzu lamarin na da matuƙar tsanani a yankin Jirond da wasu wurare a kudancin Faransa, inda jami'an ke ci gaba da fafatawa da gobarar.

    A maƙwabciyar ƙasar Sifaniya ma ana ci gaba da fama da gobarar daji.

    Firaministan ƙasar, Pedro Sanchez, ya ce ma'aikatan agaji da masu kashe gobara na aiki ba dare ba rana a yankuna takwas da gobarar ta fi ƙamari.

  7. Ministan harkokin wajen Iran ya tattauna da na Oman da Saudiyya kan mashigar Hormuz

    Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, ya tattauna ta wayar tarho daban-daban da ministocin harkokin wajen Oman da Saudiyya kan halin da ake ciki a yankin da kuma hanyoyin rage tashin hankali.

    Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta ce tattaunawar ta mayar da hankali ne kan halin da ake ciki a mashigar ruwan Hormuz da kuma ƙoƙarin diflomasiyya na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

    A kwanan nan, Iran da Oman sun gudanar da tattaunawa mai ƙarfi ta kwanaki biyu, wadda ta zo daidai da dakatar da hare-haren sojin Amurka.

    Jami’ai daga ɓangarorin biyu sun bayyana tattaunawar a matsayin mai amfani, sai dai Kazem Gharibabadi ya ce jiya Iran ba ta amince da tayin da Oman ta gabatar a yayin tattaunawar ba.

    A gefe guda kuma, tattaunawar tsakanin Iran da Saudiyya ta zo ne a daidai lokacin da Saudiyya ta sanar a jiya cewa ta kakkaɓo wasu jirage marasa matuƙa da aka harba daga Iraq zuwa cikin ƙasarta.

    A cikin ‘yan kwanakin nan, takun saƙa tsakanin Saudiyya da mayaƙan Houthi masu samun goyon bayan Iran ya sake tsananta, lamarin da ke ƙara tayar da hankali kan tsaron yankin Gabas ta Tsakiya.

  8. INEC ta ƙi amincewa da ƙara lokaci ga rijistar masu zaɓe

    Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) ta ce ba za ta ƙara wa’adin rijistar masu zaɓe ba, duk da kiraye-kirayen da jam’iyyun adawa da ƙungiyoyin farar hula suka yi na a ƙara lokaci domin bai wa ƙarin mutane damar yin rajista.

    Mataimakin daraktan sashen wayar da kan masu zaɓe da hulɗa da jama’a na INEC, Wilfred Ifogah, ne ya bayyana hakan a wata hira da Gidan talabijin na Channels.

    Ya ce, “Dole ne mu kawo ƙarshen aikin rajistar a wannan lokaci. Don haka ga waɗanda ba su samu damar kammala rajistar ba, muna ba su haƙuri, amma a halin yanzu babu abin da za mu iya yi.”

    Tun da farko, INEC ta riga ta ƙara wa’adin rajistar da makonni biyu kafin daga bisani ta rufe a ranar Lahadi.

    A cewar Ifogah, ƙarin wa’adin da aka bayar tun farko ma ya jefa hukumar cikin ƙarin matsin lamba wajen kammala shirye-shiryen rijistar masu zaɓe kafin babban zaɓen shekara mai zuwa.

    Ya ƙara da cewa, “Bisa jadawalin ayyukanmu, muna buƙatar fiye da kwanaki 75 bayan an rufe rijistar domin tattarawa, tantancewa da shirya cikakken rijistar masu zaɓe kafin gudanar da zaɓe.”

  9. Ma’aikatan gwamnati fiye da 350 sun mutu a hare-haren Amurka - Iran

    Mai magana da yawun gwamnatin Iran, Fatemeh Mohajerani, ta ce fiye da ma’aikatan gwamnati 350 ne suka mutu yayin hare-haren da Amurka ta kai, lokacin da suke gudanar da ayyukansu na hidimtawa jama’a.

    Ta kuma bayyana cewa hare-haren sun lalata manyan kayayyakin more rayuwa da suka haɗa da gadoji 12.

    A cewarta, filin jirgin saman Bushehr ya lalace gaba ɗaya kuma zai buƙaci a sake gina shi, yayin da wani sabon jirgin fasinja da aka saya kwanan nan ya kasance cikin abubuwan da hare-haren suka shafa.

  10. An kashe ƴan Najeriya 98 a rikicin ƙyamar baƙi a Afrika ta Kudu

    Akalla ’yan Najeriya 98 ne suka mutu a hare-haren ƙyamar baƙi a Afirka ta Kudu tun daga shekarar 2022, a cewar gwamnatin Najeriya.

    Haka kuma, kusan mutum 1,500 aka tilasta musu tserewa daga ƙasar bayan an lalata gidajensu da dukiyoyinsu.

    A wata ganawa da aka yi a Abuja, ƙaramin ministan Harkokin Wajen Najeriya, Sola Enikanolaiye, ya zargi Afirka ta Kudu da gaza kare ’yan Najeriya da sauran baƙi a ƙasar.

    Ya ce da dama daga cikin waɗanda aka kashe ko suka jikkata mazauna ƙasar ne bisa ka'ida, yana mai allawadai da abin da ya kira ci gaba da hare-haren ƙyamar baƙi.

    Sai dai gwamnatin Afirka ta Kudu ta musanta goyon bayan ƙyamar baƙi, inda ministan hulɗar ƙasa da ƙasa, Lamola, ya ce an kama wasu da ake zargi da kai hare-haren kuma za a gurfanar da su a kotu.

    Ƙasashen biyu sun amince da ƙara tattaunawa kan batutuwan tsaro da hijira domin kare dangantakarsu.

  11. Oman ta gabatar wa Iran da sabon shawara kan yadda za a tafiyar da mashigar Hormuz

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa ƙasar Oman ta gabatar wa Iran da wata sabuwar shawara kan kafa wata haɗaɗɗiyar hanyar gudanar da harkokin mashigar Hormuz tare da haɗin gwiwar ƙasashen yankin.

    Rahoton ya ce shawarar zai bai wa ƙasashen da za su shiga cikinsa damar ba da gudunmawa bisa raɗin kansu.

    Wani jami'in yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Reuters cewa shirin na Oman ya samu goyon bayan wasu ƙasashen yankin.

    Wannan na zuwa ne bayan da Iran ta sanar a ranar Litinin cewa ta yi watsi da wani shawara da Oman ta gabatar a baya na buɗe hanyar kudancin mashigar Hormuz har sai an cimma yarjejeniya.

    Sai dai duk da haka, ƙasashen biyu sun bayyana cewa tattaunawa mai ƙarfi da suka yi na tsawon kwanaki biyu a Tehran, a daidai lokacin da hare-haren Amurka suka tsaya, ta kasance mai amfani.

  12. Iraq ta musanta kai harin jirgi mara matuƙi zuwa Saudiyya

    Ƙungiyar Dakarun Turjiyar Musulunci na Iraq ta musanta zargin da Saudiyya ta yi cewa Iraq ta harba jiragen yaƙi marasa matuƙa zuwa cikin ƙasar tana mai cewa ba ta da hannu a harin da aka kai kan cibiyoyin man fetur.

    Ƙungiyar, wadda ta ƙunshi ƙungiyoyin Shi'a masu goyon bayan Iran, ta ce hare-haren da ’yan tawayen Houthi na Yemen suka kai na da alaƙa da takunkumin da Saudiyya ke ƙaƙabawa Yemen.

    Haka kuma ta yi gargaɗi ga Riyadh kan ɗaukar matakin ramuwar gayya.

    A halin da ake ciki, firaministan Iraq, Ali Zaidi, ya ba da umarnin gudanar da bincike bayan Saudiyya ta ce ta kakkaɓo wasu jirage marasa matuƙa da aka harba daga Iraq.

    Gwamnatin Iraq ta kuma jaddada cewa ba za ta bari a yi amfani da ƙasarta wajen kai hare-hare kan maƙwabtan ƙasashe ba, yayin da Saudiyya ke zargin ƙungiyoyin mayaƙa masu goyon bayan Iran da kai harin.

  13. Tinubu ya ƙi ganawa da tawagar Afirka ta Kudu kan rikicin ƙyamar baƙi

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ƙi ganawa da wata tawagar Afirka ta Kudu da Shugaba Cyril Ramaphosa ya aika domin tattauna rikicin kyamar baƙi da ke addabar ’yan Najeriya da sauran baƙi a ƙasar.

    Tawagar ƙarƙashin jagorancin ministan harkokin wajen Afirka ta Kudu, Ronald Lamola, ta gana da ƙaramin ministan harkokin wajen Najeriya, Sola Enikanolaiye, wanda ya ce hare-haren da ake kai wa baƙi bai kamata su lalata dangantakar ƙasashen biyu ba.

    Ya kuma bayyana cewa an kwashe kusan ’yan Najeriya 1,500 daga Afirka ta Kudu sakamakon rikicin.

    A nasa ɓangaren, Lamola ya sake jaddada cewa gwamnatin Afirka ta Kudu ba ta goyon bayan kyamar baƙi, yayin da Najeriya, Ghana, Kenya da Malawi ke ci gaba da kwashe wasu daga cikin ’yan ƙasarsu daga Afrika ta Kudu saboda hare-haren da ake kai wa baƙi tun watan Yuni.

  14. Netanyahu ya isa Washington domin ganawa da Trump

    Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya isa birnin Washington na Amurka domin ganawa da shugaban ƙasar Donald Trump.

    Ziyarar ta janyo hankalin jama’a a makon da ya gabata bayan maganganun ɗan takarar magajin garin New York, Zahran Mamdani, wanda ya bayyana yaƙin Gaza a matsayin “laifin yaƙi.”

    Ya kuma ce idan yana da ikon doka, zai iya bayar da umarnin kama Netanyahu idan ya je New York saboda zarge-zargen da ake yi masa a Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC).

    Sai dai washegari Mamdani ya janye kalamansa, yana mai cewa matsayinsa na magajin garin New York ba zai ba shi damar ɗaukar irin wannan mataki ba a hukumance.

    A wani ra'ayi da tsohon ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif ya wallafa a shafin Al Jazeera ranar Litinin, ya ce ziyarar Netanyahu zuwa Washington na da nufin rinjayar Trump kada ya kawo ƙarshen yaƙin da ake yi da Iran.

  15. Za mu biya Iran diyyar ɓarnar yaƙi da kuɗinta da ke hannunmu - Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce gwamnatinsa za ta yi amfani da kuɗaɗen Iran da ke ƙarƙashin ikon Amurka wajen biyanta diyyar ɓarnar da yaƙin baya-bayan nan ya haddasa.

    Da yake magana da manema labarai a cikin jirgin shugaban ƙasa na Air Force One, Trump ya kuma yi watsi da rahotannin da ke nuna damuwa kan ƙarancin makamai a hannun Amurka bayan watanni ana kai hare-hare kan Iran.

    Ya ƙara da cewa tsohon shugaban ƙasar Joe Biden ya aika makamai masu yawa zuwa Ukraine, lamarin da ya sa Amurka ke ƙoƙarin sake cike ma'ajiyarta a yanzu.

    "Duk da haka, har yanzu muna da makamai masu yawa. A gaskiya muna da tarin makamai fiye da yadda za mu iya amfani da su," in ji Trump.

  16. An ji ƙarar fashewa da dama kusa da ofishin jakadancin Amurka a Iraq

    An ji ƙarar fashe-fashe da dama a yankunan da ke kusa da ofishin jakadancin Amurka a birnin Erbil na yankin Kurdistan da ke arewacin Iraq, a cewar rahotanni daga kafafen yaɗa labarai na yankin.

    Tashar Al Jazeera ta ruwaito cewa an samu aƙalla fashewa bakwai a yankunan da ke kusa da ofishin jakadancin Amurka da wasu muhimman gine-ginen diflomasiyya a birnin.

    Sai dai kamfanin dillancin labaran Tasnim, wanda ake alaƙanta shi da dakarun kare juyin juya halin Iran, ya wallafa hotunan da ke nuna harin da aka kai kan sansanonin ƙungiyoyin Kurdawa masu adawa da gwamnatin Iran.

    Kamar yadda Al Jazeera ta ruwaito, Tasnim ma ta ce an samu fashewa bakwai, amma ta bayyana wuraren da hare-haren suka auku da Khalifan da Soran, waɗanda ke yankin Erbil a Iraq.

    Har zuwa yanzu, babu wani bayani a hukumance kan yawan asarar da aka yi ko irin ɓarnar da hare-haren suka haddasa.

  17. Iran ta ce duk wani yunƙurin toshe tasoshin ruwanta zai haifar da ƙazancewar yaƙi

    Iran ta gargaɗi cewa duk wani yunƙurin toshe tasoshin jiragen ruwanta da hana zirga-zirgar jiragen ruwanta ko na kasuwanci zai haifar da ƙazancewar yaƙin da ke tsakaninta da Amurka, tana mai cewa za ta mayar da martani ga duk wata barazana.

    A wata sanarwa da Hedikwatar rundunar sojin Iran, Khatam Al anbiya ta fitar, ta zargi Amurka da barazanar kai wa jiragen ruwa da tankokin man Iran hari kwanaki uku da suka gabata, tana mai cewa yin hakan tamkar faɗaɗa yaƙi ne a yankin.

    Gargaɗin na zuwa ne yayin da rikicin tsakanin ƙasashen biyu ke ƙara ƙamari, bayan tattaunawar diflomasiyya ta tsaya cik, yayin da shugaban Amurka, Donald Trump, ke ci gaba da yin barazanar ɗaukar matakin soja idan ba a samu gamsasshen sakamako ba.

  18. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Talata daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Aisha Babangida ce za ta kasance da ku a wannan lokaci.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.