Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 24/03/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na 23 ga watan Maris 2025.

Taƙaitattu

  • An miƙa wa hukumar INEC ƙorafin yi wa Sanata Natasha kiranye
  • Ba mu yi wa kowa alƙawarin tikitin takarar shugaban ƙasa ba - SDP
  • Mutum miliyan 9 za su kamu da HIV cikin shekara huɗu - Hasashen MDD
  • Firaministan Pakistan ya yi alla-wadai da kashe mutane a Masallaci a Nijar
  • Tankar mai ta fashe a jihar Neja
  • Kotu ta yi watsi da tsige Firaministan Koriya ta Kudu
  • Hamas ta tabbatar da kashe mata kwamandojoji a asibiti a Gaza

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed, Aisha Aliyu Jaafar da Ahmad Bawage

  1. Tankar mai ta fashe a jihar Neja

    A ranar Lahadi ne wata tankar man fetur ta fashe a garin Kontagora da ke jihar Neja, lamarin da ya jefa firgici a zukatan mutanen yankin da masu motoci.

    Sai dai ba a samu rahoton wani ya mutu ba a fashewar, wadda ta auku a gidan man AA Rano da ke daura da babban asibitin Kontagora.

    Wani ganau ya ce tankar ta kama da wuta, sannan baƙin hayaƙi ya turnuƙe, amma tankar ce kawai ta ƙone, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

    Daraktan yaɗa labarai na hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja, Hussaini Ibrahim, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce jami'an kashe gobara sun isa da sauri domin hana gobarar faɗaɗa, sannan ya ce babu wanda ya rasa ransa.

  2. Kotu ta yi watsi da tsige Firaministan Koriya ta Kudu

    Kotun kundin tsarin mulki ta Koriya ta Kudu ta yi watsi da matakin tsige Firaministan ƙasar Han Duk Soo.

    Matakin na nufin Mr Han ya dawo matsayinsa na shugaban riƙo a ƙasar.

    Kotun ba ta samu hujjojin da ke tabbatar da yana da hannu a ayyana dokar soji da shugaban ƙasar Yook suk Yeol ya ayyana a Disamba ba.

    Majalisar ƙasar ta kaɗa ƙuri'ar tsige Mr Han ne a mako biyu da maye gurbin shugaban ƙasa wanda shi ma aka tsige.

    Mr Han ya yi maraba da hukuncin na kotun, inda ya ce yana neman haɗin kan ƴan ƙasar, sannan ya ce bai kamata bambancin siyasa ya raba kan ƙasar ba.

  3. Hamas ta tabbatar da kashe mata kwamandojoji a asibiti a Gaza

    Jami'an Hamas sun shaida wa BBC cewa an kashe wasu shugabannin ƙungiyar a wani harin Isra'ila a asibitin Nesser a kudancin Gaza.

    Isma'il Barhoum, shugaban kula da harkokin kuɗi na ƙungiyar yana jinya a asibiti sakamakon raunukan da ya samu a harin da ya rutsa da shi kwana huɗu da suka gabata.

    Isra'ila ta ce ta kai hare-haren ne kan shugabannin Hamas.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce tana shirin ƙaddamar da sabon farmaki tana mai cewa za ta ƙara tura dakarunta zuwa Gaza.

    Ta wallafa hotuna da ke nuna tankokin yaƙi a kudancin Isra'ila da kuma dubban sojoji suna shiri.

  4. Buɗewa

    Jama'a barkanmu da safiya, barkanmu da sake haɗuwa a shafinmu na labaran kai-tsaye daga nan sashen Hausa na BBC.

    A yau Litinin za mu kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za kuma ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta irin su Facebook da X da Instagram domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo.

    Da fatan za ku kasance tare mu.