Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Afcon: Moroko 4-2 Najeriya [Bugun Fenariti]

Karawar Moroko da Najeriya a matakin kusa da wasan ƙarshe domin tantance ƙasar da za ta buga wasan ƙarshe da Senegal a ranar Lahadi a Gasar Kofin Ƙwallon Ƙafa ta Nahiyar Afirka 2025.

Taƙaitattu

  • Domin samun ƙarin bayani kan yadda BBC ke amfani da fasahar AI, latsa nan
  • Wannan shafi ba ya sabunta kansa. A danna 'refresh' domin ganin sabon labari
  • Senegal ta doke Masar a wasan kusa da na karshe na Afcon ta hannun Mane wanda ya lashe gasar cin kofin zakarun Turai
  • Moroko da Najeriya sun fara wasa da ƙarfe 9:00 na dare agogon Najeriya
  • Ana wasan ne a filin wasa na Prince Moulay Abdallah a birnin Rabat
  • Ƙasar da ta yi nasara za ta kara a wasan ƙarshe da Senegal a ranar Lahadi

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Haruna Kakangi tare da taimakon fasahar AI

  1. , Najeriya 0-0 Moroko

    An yi karon-batta a mintuna bakwai na farkon wannan wasa. Kowa jininsa a ƙumba.

    Ana goge raini.

  2. , Najeriya 0-0 Moroko

    Babban jami'in hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya Fifa, Arsene Wenger, yana halartar wannan karawa.

  3. , Najeriya 0-0 Moroko

    Semi Ajayi ya yi asarar ƙwallo inda Ismael Saibari ya ɗauka, amma an ƙwace nan take domin hana ɗan wasan na Moroko doka ta.

    Magoya bayan masu wasa a gida sun shirya fashewa da sowa in da ƙwallon ta je raga.

  4. , Najeriya 0-0 Morocco

    Ian Williams, wakilin BBC Sport a Rabat

    Wannan filin wasa ba a cewa komai. Ko ina ya yi ja jajir.

    Lokacin da alƙalin wasa ya hura usur domin fara wasa ko ina ka duba ana kaɗa jan ƙyalle.

    Wannan ne abin da ake kira fa'idar wasa a gida.

  5. AN FARA WASA, Najeriya 0-0 Morocco

    Moroko ce ta fara wasa.

  6. Wasannin Moroko kafin zuwa wasan kusa da ƙarshe, Najeriya da Morocco

    Matakin rukuni:

    Morocco 2-0 Comoros

    Morocco 1-1 Mali

    Zambia 0-3 Morocco

    Zagaye na 16

    Morocco 1-0 Tanzania

    Kwata-fainal

    Kamaru 0-2 Morocco

  7. Wasannin Najeriya kafin zuwa wasan wasan kusa da na karshe:, Najeriya da Morocco

    Matakin rukuni:

    Najeriya 2-1 Tanzania

    Najeriya 3-2 Tunisia

    Uganda 1-3 Najeriya

    Zagaye na 16

    Najeriya 4-0 Mozambique

    Kwata-fainal:

    Algeria 0-2 Najeriya

  8. Ƴanwasan Najeriya

    Mai tsaron raga: Nwabali

    Masu tsaron baya: Osayi-Samuel, Ajayi, Bassey, Onyemaechi

    Tsakiya: Onyeka, Onyedika, Iwobi

    Gaba: Osmihen, Lookman, Adams

  9. Ƴanwasan Moroko

    Mai tsaron raga: Bounou

    Masu tsaron baya: Hakimi, Aguerd, Masina, Mazraoui

    Tsakiya: Diaz, El Khannouss, El Aynaoui, Saibari, Ezzalzouli

    Gaba: EL Kaabi

  10. An sanar da sunayen ƴanwasa kuma ƴanwasan suna motsa jini.