A ranar Litinin ne ƙungiyar Manchester United ta sallami mai horas da ƴan wasanta Ruben Amorim bayan kwashe lokaci ƙungiyar na faɗi-tashi.
Ƙungiyar ta sanar da cewa Darren Fletcher ne zai jagoranci wasanta na gaba da ƙungiyar Burnley.
To amma yanzu wane ne zai maye gurbin Amorim a matsayin kociyan ƙungiyar na dindindin?
Bayan gazawar Erik
ten Hag, da Ralf Rangnick da kuma Amorim a yanzu, shin ko ya kamata United ta nemo
wani kociyan da ya yi abin a zo a gani a gasar Premier?
Unai Emery na yin kyakkyawan aiki a Aston Villa, inda ya ɗago
ƙungiyar daga can ƙasar teburin Premier zuwa gasar nahiyar Turai, ga shi kuma a
wannan kakar suna gogayya don lashe Premier.
To amma bai taɓuka abin kirki ba a lokacin da ya riƙe
Arsenal, ko duk da haka United za ta ce tana son shi?
Andoni Iraola shi ma babu shakka za a samu ƙungiyoyin da ke
son shi bayan jagorantar Bournemouth har ta ƙare a matsayi na 9 a kakar da ta
gabata.
Zai yi wahala ya ce a’a idan Manchester United ta neme shi.
Kwantaragin Oliver Glasher zai kare a Crystal Palace a ƙarshen kaka, kuma ƙungiyar ce ta lashe kofin ƙalubale na FA a kakar da ta gabata.
Shi kuwa Eddie Howe ya kawo ƙarshen tsawon shekarun da Newcastle
ta kwashe babu kofi, inda ya ci mata kofin Carabao.
Ko kuwa United za ta fi son ta ɗauki ɗan cikin gida?
Tsohon ɗan wasan tsakiya na ƙungiyar Darren Fletcher shi ne
mai horas da ƴan ƙasa da shekara 18 na ƙungiyar, kuma ya yi shekara 11 yana
wasa ƙarƙashin Alex Ferguson.
Wani da za a iya sa ran zai karɓi aikin shi ne Michael
Carrick.
Yanzu ba ya da aiki bayan Middlesbrough ta sallame shi a watan Yuni.
A wajen Ingila kuma akwai kociyoyi da yawa da United za ta
iya ƙyalla ido a kansu:
Ɗaya daga cikin irin waɗannan da aka sha alaƙanta United da
shi, shi ne Mauricio Pochetinho.
Wani da mutane da dama ke tunani a kai kuma shi ne tsohon
kocin Barcelona Xavi.
Shi ma Zinedine Zidane ya kwashe shekara huɗu yanzu ba ya aikin
horaswa tun bayan barin Real Madrid.
Wane ne ya kamata United ta ɗauko?