Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 03/02/25

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi, Umaymah Abdulmumin, Aisha Aliyu Jaafar da Ahmad Bawage

  1. Mu kwana lafiya

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Sai kuma gobe da safe - idan Allah ya kai mu.

    Daga nan sashen Hausa na BBC, muke cewa asuba ta gari.

  2. Shugabanni Afrika za su tattauna don warware rikicin Kongo

    Ana sa ran shugaban Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo da takwaransa na Rwanda za su halarci taron yankin domin tattaunawa kan rikicin gabashin Kongo.

    Yunkurin haɗa mutane a baya ya citura sai dai shugaban ƙasar Kenya ya ce shugabannin biyu za su kasance a birnin Dares Salaam na ƙasar Tanzania a ranar Asabar mai zuwa.

    An yi ammanar cewa taron haɗin gwiwar da za a yi tsakanin shugabannin ƙasashen gabashin Afrika da takwarorinsu na Kudancin Afrika zai taimaka wajan samar da hanyoyin da za a bi domin samun zaman lafiya.

    Haka kuma ƙungiyar ƙasashe bakwai masu karfin tattalin arziki a duniya wato G7 da Tarayyar Turai sun yi Alla-wadai da harin da ƴan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda suka kai gabashin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo, inda suka ce hakan keta hakkin ƴancin kasa ne.

  3. Agogon da ke hasashen tashin duniya ya ƙara matsawa da daƙiƙa ɗaya

    Agogon da ke hasashen tashin duniya ya ƙara matsawa da daƙiƙa ɗaya, inda yanzu ya rage daƙiƙa 89 ko kuma minti ɗaya da sakan 20 kafin tashin duniya - mafi kusa da ya taɓa kaiwa.

    Ƙungiyar masu nazari kan harkokin kimiyya ta Bulletin of Atomic Scientist (BAS) - wadda ke saita agogon a duk shekara, ta ce barazanar makaman nukiliya, da kuma fargabar yin amfani da abubuwan cigaba a fannin ilimin halittu ba yadda ya kamata ba.

    Daniel Holz, shugaban kwamitin kimiyya da tsaro na ƙungiyar, ya ce wannan matakin ''gargaɗi ne ga dukkan shugabannin duniya''.

  4. WHO ta ce an fara gwajin riga-kafin Ebola a Uganda

    Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce an fara gwajin allurar riga-kafin cutar Ebola a ƙasar Uganda bayan kwanaki uku da aka sanar da ɓullar wata sabuwar cutar.

    A halin yanzu babu wata allurar riga-kafi da aka amince da ita kan nau'in cutar Ebola ta Sudan wadda ta yi sanadin mutuwar wata ma'aikaciyyar jinya a Kampala babban birnin ƙasar.

  5. Aston Villa ta ɗauki aron Asensio daga PSG

    Aston Villa ta kammala ɗaukar ɗan wasan tsakiya na Sifaniya Marco Asensio daga Paris St-Germain a matsayin aro har zuwa karshen kakar wasanni ta bana.

    Asensio wanda ya lashe Champions League har sau uku da Real Madrid - ya kasance ɗan wasa na huɗu da Villa ta ɗauka bayan buɗe kasuwar sayar da ƴan kwallo a watan Janairu ɗin nan, bayan ɗaukar Marcus Rashford da Donyell Malen da kuma Andres Garcia.

    Rahotanni sun bayyana cewa Villa ce za ta biya albashin ɗan wasan mai shekara 29, sai dai babu zaɓin ɗaukarsa na dindindin.

    Asensio ya zura kwallaye bakwai a wasanni 47 da ya buga wa PSG tun komawa can daga Madrid a 2023.

    Ya taimakawa ƙungiyar lashe gasar Ligue 1 a bara, amma ya buga wasanni takwas kacal a bana.

    Yana cikin tawagar Sifaniya da ta lashe gasar Nations League a 2023.

  6. Bam ya kashe mutum aƙalla 20 a Syria

    Aƙalla mutum 20 ne suka mutu, yawanci mata bayan tashin wani bam da aka saka cikin wata mota a arewacin Syria, a cewar fadar shugaban ƙasar.

    Hukumar tsaro ta Civil Defence a Syria ta ce wata mota cike da abubuwan fashewa ta tashi ne a wata babbar hanya a wajen birnin Manbij a daidai lokacin da wata mota ɗauke da kayan gona ta zo wucewa.

    Tun da farko, hukumomi sun ce mutum 15 ne suka mutu - ciki har da mata 11 da yara mata uku.

    Wasu mata 15 kuma sun samu munanan raunuka.

    Fadar shugaban ƙasar ta sha alwashin hukunta waɗanda ta kwatanta da ƴan ta'dda da suka kai wannan hari.

    Babu wata ƙungiya da ta fito ta ɗau alhakin kai harin na bam, wanda shi ne mafi muni tun bayan da ƴan tawaye suka hamɓarar da gwamnatin Bashar al-Assad a watan Disamba.

  7. Sojoji sun ce sun kama ƴan bindiga 23, sun kashe ɗaya a Taraba

    Rundunar bataliya ta shida na sojojin Najeriya sun ce sun kashe wani ɗan bindiga, bayan yin dirar miƙiya kan sansaninsu da ke ƙauyen Kambari na karamar hukumar Karim Lamido a jihar Taraba.

    Lamarin ya faru ne ranar Lahadi bayan samun bayanan sirri na ayyukan ƴan bindigar, a cewar sojojin.

    Wata sanarwa da muƙaddashin mataimakin darektan rundunar, Captain Olubodunde Oni ya fitar, ya ce sun yi artabu da ƴan bindigar ta hanyar yin musayar wuta na sa'o'i.

    Ya ce lamarin ya kai ƴan bindiga 23 sun miƙa wuya, maza 19 da mata huɗu.

    Captain Oni ya kuma ce sun yi nasarar ƙwato tarin makamai da suka haɗa da bindigar AK-47 guda huɗu da harsasai da bindigar harbi ka ruga biyu da adduna 28 da wuƙaƙe 48 da kuma babura 16.

  8. Ban ji daɗin sumbatar da Rubiyales ya yi min ba - Hermoso

    Tauraruwar kwallon kafar SIfaniyar Jenni Hermoso, ta bayar da shaida a shari'ar da ake yi wa tsohon shugaban hukumar kwallon kafar ƙasar, Luis Rubiyales.

    Ana tuhumarsa da laifin cin zarafi ta hanyar lalata da kuma amfani da karfi a lokacin da ya rungumi Hermoso kuma ya sumbace ta bayan nasarar da Sifaniya ta samu a gasar cin kofin duniya ta mata a Australia.

    Ta faɗa wa masu taya alkali yanke hukunci cewa ba a girmama ta a matsayinta mace ba.

    Mista Rubiyales dai ya musanta aikata ba daidai ba.

  9. Kotu ta tura tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta ƙasa gidan yarin Kuje

    Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja, babban birnin Najeriya, ta tura tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta ƙasa, Farfesa Usman Yusuf zuwa gidan yarin Kuje.

    Hukumar cin hanci da rashawa ta EFCC ce ta kama Farfesa Yusuf kan zargin almundahahanar kuɗi da ya kai naira miliyan 90.

    Mai shari'a Chinyere E. Nwecheonwu ce ta bayyana haka lokacin yanke hukunci, inda ta ce za a ci gaba da tsare shi a gidan yarin.

    Don haka ne kotun ta ɗage zaman sauraron shari'ar har sai ranar 12 ga watan Febrairu.

    Sai dai farfesa Usman ya musanta zarge-zargen da ake yi masa.

  10. Babu wanda zai yi nasara a yaƙin cinikayya -Tarayyar Turai

    Shugababbin ƙasashen Turai sun yi gargaɗin mayar wa Amurka da martani idan shugaba Trump ya aiwatar da barazanar da ya yi na saka EU a cikin shirinsa na sanyawa wasu ƙasashe haraji.

    Babbar jami'ar kula da harkokin waje ta Tarayyar Turai, Kaya Kallas, ta ce babu wanda zai yi nasara a yaƙin cinikaya kuma China za ta riƙa yi wa ɓangarorin biyu dariya.

    Shi kuwa shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya jaddada buƙatar haɗin kai tsakanin abokan cinikayyar.

    Ya ce Amurka da Turai za su iya cin moriyar juna ta hanyar musayar kayayyaki da sauran abubuwa tsakaninsu.

    Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya ce ya zama dole Turai ta kare mutuncinta tare da mai da martani idan aka yi barazana ga muradun kasuwincinta.

  11. Isra'ila ta kashe mutum kusan dubu 60 a Gaza - Hamas

    Hamas ta yi ikirarin cewa adadin mutanen da Isra'ila ta kashe a zirin Gaza ya kusan dubu sittin da biyu.

    Alkaluma na Ma'aikatar lafiya ta yankin sun nuna cewa adadin wadanda suka mutu ya haura sama da dubu arba'in da bakwai .

    Sai dai a wata sanarwar da Hamas ta fitar ga manema labarai ta ce an yi ammanar cewa akwai ƙarin gawarwakin mutane dubu goma sha hudu a ƙarƙashin baraguzan gine-gine, ko kuma a wuraren da masu aikin ceto ba za su iya shiga ba .

    Masu shiga tsakani sun fara shirin fara tattaunawa kan mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta a Gaza, ko da yake ba a sanar da lokacin da za a fara tattaunawar ba .

  12. 'Rasha na kashe sojojin Ukraine da ta kama babu-ji babu-gani'

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ana samun ƙaruwar adadin fursunonin yaƙin Ukraine da sojojin Rasha ke kashewa.

    Hukumar kare haƙƙin biladama ta MDD a Ukraine ta ce ta samu rahotannin irin waɗannan kashe kashen guda 79 tun daga watan Agustan bara.

    MDD ta ce batun kisan ba shaci faɗi bane ganin cewa akwai manyan masu faɗa a ji a Rasha da sukayi kiran a kashe sojojin Ukraine da aka kama.

    Dokar kare ƴancin biladama ta duniya ta haramta kashe fursunonin yaƙi, kuma ta na kallon lamarin a matsayin laifin yaƙi.

    Zuwa yanzu Rasha ba ta ce komai ba kan rahoton.

  13. Shugaban Afirka ta kudu ya musanta zargin da Trump ya yi kan ƙwace filaye

    Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya musanta zargin da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi na cewa gwamnatin ƙasar na ƙwace filaye.

    Trump ya yi barazanar dakatar da duk wani tallafi zuwa ƙasar kan batun.

    A cewar shugaba Cyril, dokar baya-bayan nan da aka amince da ita ba kan ƙwace filaye ba ne, doka ce da za ta tabbatar da daidaito ga kowa wajen mallakar filaye.

    Ya bayyana cewa tun a baya ƙasarsa na da dokoki da ke kare tsarin mallakar filaye da haƙƙoƙin mutanen da suka mallaki filaye.

    Ya bayyana buƙatar tattaunawa da gwamnatin Trump inda ya kuma ce tallafin PEPFAR HIV ne kawai tallafin da ƙasarsa ta samu daga Amurka.

    Hamshaƙin mai kuɗin nan ɗan asalin Afirka ta Kudu Elon Musk, wanda ɗaya ne daga cikin masu bai wa Trump shawara, ya mayar da martani kan sanarwar Mista Ramaphosa a shafinsa na X inda ya kira sabuwar dokar da nuna 'wariyar launin fata'.

    Shekara 30 bayan kawo ƙarshen mulkin wariyar launin fata, akasarin filayen Afirka ta kudu na hannun fararen fata marasa rinjaye wanda hakan ke nuna sabuwar dokar za ta fi shafar su.

    Ƙarƙashin sabuwar dokar, gwamnati za ta iya ƙwace fili ba tare da biyan diyya ba, idan hakan ya zama zai amfani alumma.

  14. An ciro sunƙin hodar iblis 57 a cikin wani mutum ta hanyar tiyata

    Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Najeriya NDLEA ta ce an yi wa wani mutum mai shekara 59 tiyata domin ciro sunƙin hodar ibilis 57 cikin guda 81 da ya haɗiye kwanaki bakwai da suka gabata a Addis Ababa da ke Habasha.

    A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Femi Babafemi ya fitar, an kama mutumin ne a lokacin da ake tantance fasinjoji bayan isar su filin jirgin sama na Murtala Muhammad daga Habasha a ranar 26 ga watan da ya gabata.

    Kakakin hukumar ya ce bincike ya gano cewa mutumin wanda ya yi iƙirarin ɗan kasuwa ne a yankin Oshodi da ke jihar Lagos, ya tafi Addis Ababa inda ya haɗiyi sunƙi 81 na hodar ibilis ɗin, daga bisani kuma ya hau jirgi zuwa Beirut da ke Lebanon domin kaiwa a kan kuɗi dala 3,000.

    Ya kuma ce binciken nasu ya nuna cewa mutumin bai samu shiga ƙasar ba saboda kuɗin hannunsa ba su kai dala 2,000 ba da ake buƙata kafin shiga ƙasar wanda ya sa aka mayar da shi Addis Ababa inda ya yi yunƙirin fitar da miyagun ƙwayoyin amma ya kasa, daga nan kuma ya dawo Najeriya inda suka yi nasarar cafke shi.

    Femi ya ƙara da cewa bayan kwanaki 5 ƙarƙashin sa idon hukumar a asibitin koyarwa na Jami'ar Jihar Lagos, mutumin ya yi kashin sunƙin hodar ibilis guda 24, inda daga bisani saboda gujewa kamuwa da rashin lafiya, aka yi masa tiyata domin cire sunƙi 57 da suka rage bayan uwargidansa da ɗan'uwansa sun amince da yin hakan.

  15. Trump ya yi barazanar daina bai wa Afirka ta Kudu tallafi

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce zai katse duk wani tallafi da ƙasarsa ke bai wa Afirka ta kudu bisa zargin ta da kwace filaye da kuma nuna wariya ga wani ɓangare na al'umma.

    A watan da ya gabata ne Shugaba Cyril Ramaphosa ya sanya hannu kan wani ƙudirin doka da ya ba da damar kwace filaye ba tare da biyan diyya ba a wasu lokuta.

    A shafinsa na Truth, Trump ya ce ''zan katse duk wani tallafi ga Afirka ta kudu har sai an kammala gudanar da cikakken bincike kan lamarin.''

    A cewar alƙaluman gwamnatin Amurka, ƙasar ta ware dala miliyan 440 domin tallafi ga Afirka ta kudu a shekarar 2023.

    Sai dai wasu masu fashin baƙi na nuna fargaba kan mummunar sakamakon da dokar za ta iya samarwa kwatankwancin yadda aka samu a Zimbabwe wadda kwace filaye ya yi sanadin ruguza tattalin arziƙin kasar ya kuma kori masu zuba jari.

    Batun mallakar filaye matsala ce da ta daɗe tana damun Afirka ta kudu ganin cewa fararen fata ne ke cigaba da mallakar akasarin gonaki a ƙasar, shekaru 30 bayan kawo ƙarshen mulkin wariyar launin fata.

  16. Gwamnatin Najeriya ta musanta batun ƙarin kuɗin lantarki

    Gwamnatin Najeriya ta musanta rahotannin da ke nuna cewa tana da aniyar ƙara kuɗin wutar lantarki cikin watanni masu zuwa.

    A cikin wata sanarwa da ta fitar, mai bai wa shugaban Najeriya, Bola Tinubu shawara kan makamashi, Olu Arowolo Verheijen, wadda aka ruwaito tana cewa cewa "za a yi ƙarin kashi 65 na kuɗin", ta ce an yi wa kalamanta gurguwar fassara.

    Jami'ar dai ta yi wannan kalami ne a taron makamashi na Afirka da aka gudanar a birnin Dar es Salam na ƙasar Tanzaniya, inda jaridun Najeriya da dama suka wallafa batun.

    Ta ce bayan ƙara kuɗin wutar na Band A a shekarar 2024, a yanzu kuɗin da ake samu daga wutar lantarkin ya na biyan kashi 65 ne cikin kuɗin da ake kashewa wurin samar da wutar, inda gwamatin ƙasar ke cigaba da biyan giɓin da ake samu.

    Olu Verheijen ta kuma ce duk da dai gwamnatin ta duƙufa wajen samar da kuɗin wuta mai sauƙi nan gaba, abin da ta mayar da hankali kai a yanzu shi ne tabbatar da samar da ƙarin wutar lantarkin ga ƴan ƙasar, da tabbatar da rage ɗaukewar wutar, da kuma tabbatar da kare marasa ƙarfi.

    A shekarar 2024 ne gwamnatin Najeriya ta janye wani ɓangare na tallafin lantarki da take biya, lamarin da ya haifar da hauhuwar farashin kuɗin wuta ga masu tsarin 'Band A' a faɗin ƙasar.

    Lamarin ya janyo ƙorafi a faɗin ƙasar ganin irin halin taɓarɓarewar tattalin arziƙi da al'umma ke fuskanta.,

  17. Burkina Faso da Nijar da Mali za su kafa kamfanin sufurin jiragen sama

    Ministan sufuri a Nijar, Kanal Manjo Salissou Mahaman Salissou ya ce ƙawancen ƙasashen Sahel, da ya haɗa Burkina Faso da Nijar da Mali, na shirin kafa kamfanin sufurin jirgin sama domin ƙarfafa haɗin gwiwar sabuwar ƙungiyar, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta ActuNiger ta ruwaito.

    Salissou ya ce kafa kamfanin sufurin jirgin saman na AES abu ne mai muhimmanci da za su mayar da hankali a kai, kuma nan ba da jimawa ba za su samar da kamfanin mai launin ƙasashen, wanda zai haɗa manyan biranensu da ma wasu wuraren.

    Ministan ya kuma ce shugabannin mulkin soji a Niamey sun umurci hukumomin da ke kula da fannin sufurin jiragen sama su 'sassauta wasu dokoki'' domin a gaggauta samar da kamfanin jirgin sama na yankin da ma na ƙasar.

    A baya ƙasashen ƙawancen na AES waɗanda ke ƙarƙashin mulkin soji sun ƙaddamar da fasfo ɗin bai-ɗaya, sun kuma sanar da kafa dakarun haɗin gwiwa domin daƙile ƙungiyoyin ƴan bindiga da ke addabar yankin bayan ficewar su daga ƙungiyar ECOWAS.

  18. Najeriya ta tsananta tsaro kan iyakokinta saboda cutar Ebola

    Hukumar daƙile yaɗuwar cututtuka a Najeriya NCDC ta tsananta tsaro da sanya ido kan iyakokin shiga ƙasar kamar filayen jiragen sama, domin guje wa shigar cutar Ebola cikin ƙasar.

    A cikin wani bayani da shugaban hukumar Dakta Jide idris ya fitar, ya tabbatar da cewa ba a samu wani ɗauke da cutar ba zuwa yanzu.

    Hukumar ta kuma gargaɗi ƴan ƙasar su guje wa yin tafiyar da ba ta zame wajibi ba zuwa ƙasashen da aka samu ɓullar cutar.

    A ranar 30 ga watan Janairun 2025 ne Uganda ta tabbatar da ɓullar cutar Ebola a biranen Wakiso da Mukono da Mbale da ke yankin Mbale.

    Zuwa yanzu dai an tabbatar da mutuwar mutum ɗaya, yayin da hukumomi ke cigaba da sanya ido kan mutane 44 da ake tunanin sun haɗu da wanda ya mutu sanadiyyar cutar.

  19. An gano gawarwaki 55 na haɗarin jiragen saman Amurka

    Shugaban hukumar kashe gobara ta birnin Washington, John Donnelly, ya ce an gano gawarwaki hamsin da biyar na fasinsojojin jirgin sama da ya yi taho mu gama da jirgin soji mai saukar angulu.

    Ya ce an kuma gano dukkan iyalansu.

    Mutane 67 ne jiragen biyu ke ɗauke da su waɗanda dukkansu suka rasu.

    Shugaban hukumar ya kuma ce ana ci gaba da bincike kan lamarin.

  20. Donald Trump zai ƙara haraji kan kayan Tarayyar Turai

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ko shakka babu zai ƙara haraji kan kayan da ake ƙirawa ake shiga da su Amurka daga Tarayyar Turai.

    Mista Trump ya shaida wa manema labarai cewa zai sanya harajin nan ba da jimawa ba, ya kuma zargi kungiyar da cin gajiyar Amurka, yana mai bayyana hakan a matsayin zalunci.

    ''Ba su sayen motocinmu da amfanin gonarmu, kusan babu wani abu da suke saya daga wajenmu, amma mu kusan komai daga wajensu muke saye'' in ji shi.

    A yau Litinin ne ya kamata shugaba Trump ya tattauna da shugabannin ƙasashen Canada da Mexico bayan sanya wa ƙasashen biyu masu maƙwaftaka da Amurka haraji da kuma China.

    Tun da farko dai Trump ya gargaɗi Amurkawa cewa matakin nasa zai iya haifar da raɗaɗi, sai dai ya ce nan gaba hakan zai zama alheri ga Amurka.