Tsibirin da ƙasashen duniya ke rige-rigen mallaka saboda arzikinsa

    • Marubuci, Adrienne Murray
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Business reporter
    • Aiko rahoto daga, Greenland
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Kafin komawar Donald Trump mulki, ya bayyana cewa, Amurka na buƙatar sayen tsibirin Greenland domin ta ƙara haɓɓaka tattalin arzikinta, sai dai masu kula da tsibirin sun yi gaggawar mayar da martanin cewa ba na sayarwa ba ne.

Ana ci gaba da nuna tsananin buƙatar albarkatun ƙasa da tsibirin ke da shi.

Wasu dogayen tsaunuka sun bayyana a gabanmu a daidai lokacin da kwale-kwalenmu ke ci gaba da ƙoƙarin tsayawa a gaɓar tekun Greenland.

"Waɗancan manyan tsaunukan masu tsayi zagaye suke da zinari," cewar Eldur Olafsson, shugaban kamfanin haƙar ma'adanai na Amarog.

Bayan mun yi tafiya ta tsawon sa'a biyu, sai muka shiga wani kwari mai nisa da kamfanin ke haƙar zinari.

Har ila yau, shugaban kamfanin na zagayawa cikin tsaunukan da kwarurruka, domin neman wasu ma'adanai masu mahimmanci, saboda suna da lasisin binciken yankin da ya kai murabba'in kilomita 10,000.

"Muna neman Tagulla da duwatsu masu daraja"

Sansanin wani gungu ne na gidajen wucin gadi ne waɗanda suke ɗauke da ma'aikata 100, ciki har da da ƴan Greenland, da Australiya, da tsoffin masu hakar gwal na Birtaniya.

Daga nan ne muka hau wani tudu inda muka shiga mota zuwa inda ake haƙar zinari a cikin wani ginin ƙarƙashin ƙasa mai duhu.

"Duba nan!" in ji Mista Olafsson yana nuni da wani wuri mai haske da siririn layi mai duhu."Zinariya, Zinariya ne a wajen nan gaba ɗaya. Wannan ba abin mamaki ba ne?"

Kamfanin Amaroq ya fara aikin haƙar ma'adanai ne a shekarar 2015,wato shekara goma da suka gabata, amma an rufe shi saboda faɗuwar farashin zinare, da tsadar gudanar da aikin na haƙowa.

Amaroq yana da yaƙinin cewa a yanzu zai samu riba sosai, inda yake shirin bunƙasa masana'antar sarrafa ma'adinan da tace ƙarafa masu daraja zuwa dunƙulen zinariya.

"Kowane wata zamu iya cire zinari ton dubu 30" a cewarsa.

Mista Olafsson ya ƙara da cewa "tsibirin Greenland zai iya iya samar da dukkan ma'adanai da ƙasashen yammacin duniya za su buƙata tsawon shekaru da dama." "Kuma wannan matsayi ne na musamman."

Yanzu haka dai akwai kamfanonin haƙar ma'adainai biyu a tsibirin.

Greenland yankin ne mai cin gashin kansa, kuma wani ɓangare ne na ƙasar Denmark, sai dai shi ke kula da dukkan albarkatun tsibirin.

Tsibirin wani yanki ne da ke da wasu albakatun ƙasa da ake amfani da su wajen yin komai ciki har da wayar hannu da batira da motoci masu amfani da hasken rana.

Akwai kuma ɗanyen mai da iskar gas, sai dai an haramta haƙosu.

Shugaban sashen kasuwanci na Greenland, Christian Kjeldsen, ya ce halin da ake ciki na siyasa a duniya a yanzu yana haifar da sha'awar tsibirin mafi girma a duniya.

Ya ce ƙasar China ita ce ƙasar da ta fi kowace albakatun ƙarafa masu daraja da ba kasafai aka cika samun su ba, shi ya sa ƙasashen Yamma ke neman inda za su cike giɓinta da shi.

Hakan ne ya sanya da hankalin ƙasashe da dama ya fara komawa kan yadda za su samu damar shiga Greenland, haka ita ma China tana neman shiga sai dai ita taƙaitaccen izini take nema.

Ministar kasuwancin Greenland, Naaja Nathanielsen, ta ce an ƙara samun masu son shiga tsibirin sosai a cikin shekara biyar da suka wuce.

"Mun saba zama waɗanda ke taimakawa wajen ƙara ta'azzara sauyin yanayi , saboda haka muke son ba da gudumuwa wajen shawo kan matsalar."

Duk da Greenland ke kan gaba wajen arziƙin ma'adanai, amman ba a sarrafa zinari a tsibirin yadda ya kamata.

Tattalin arziƙinsu na kayan da suke iya sarrafawa cikin gida ya kai dalar Amurka biliyan uku, wanda yawanci ake samar da kuɗin daga ɓangaren gwamnati da kuma kamun kifi.

Kuma yankin ya ta'allaƙa ne kan kuɗin shiga na dalar Amurka miliyan 600 na tallafin da Denmark ke ba su.

Ƴan siyasar yankin na fatan kuɗin shiga na haƙo ma'adanai da tsibirin ke samu, zai rage yawan dogaro da tallafin Denmark domin ƙara musu ƙwarin gwiwa kan ƙoƙarinsu na samun ƴancin kai.

Sai dai yanzu haka Greenland na samun kuɗin shiga masu yawa daga masu yawon buɗe ido.

Aikin haƙar ma'adanai ba abu ne mai sauƙi ba, saboda yanayin garin.

Shi ne tsibiri mafi girma da kashi 80 cikin 100 nasa, ƙanƙara ce ta zagaye shi.

Yana da kuma tsaunuka masu duhu sannan babu titunan da suka haɗa unguwanni.

Wani mazaunin garin, Qaqortoq, Heidi Mortensen Møller ya nuna shakku kan ko sabbin kamfanonin haƙo ma'adanan za su samar da aikin yi ga mazauna yankin.

"Lokacin da suka ce za su ƙara ayyukan yi, wa suke magana?"

Jess Berthelsen, shugaban ƙungiyar ƙwadago , SIK, ya ce mutane da yawa suna tunanin cewa kuɗin shiga da ake samu na ma'adinai, ba zai amfani yankin ba.

"Amman muna goyon bayan a inganta ayyukan haƙo ma'adanai saboda Greenland na buƙatar hanyoyin kuɗin shiga da yawa ba ɓangaren kamun kifi kaɗai ba.

Ba a san yadda sabon tsarin na Trump kan Greenland zai kasance ba. Sai dai kuma firaministan yankin, Mute Egede ya faɗa a farkon wannan wata cewa "muna buƙatar mu yi hulɗa da Amurka" kuma "kofa a buɗe take ta fuskar hakar ma'adinai".

Mista Kjeldsen na ƙungiyar 'yankasuwa, yana fatan za a "zuba jari da ake buƙata" ga ɓangaren.