Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 01/01/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail da Haruna Kakangi

  1. Za mu ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen da suka zama dole - Tinubu

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da bijiro da sauye-sauyen "da suka zama dole" domin gina ƙasar.

    Tun daga hawa mulkinsa wata 19 da suka gabata, an ga yadda Tinubu ya cire tallafin mai, ya sauya kasuwar canjin kuɗaɗen waje, ya gabatar da sabbin dokokin haraji, ya ƙaddamar da tallafin karatu, ya ƙara mafi ƙanƙantar albashi.

    "Za mu ci gaba da bijiro da sauye-sauyen da suka zama dole domin tabbatar da cigaba mai ɗorewa da yalwa a ƙasarmu," in ji shi cikin saƙonsa na sabuwar shekara.

    "Muna kan hanya mai kyau ta gina Najeriya wadda za ta kyautata wa kowa da kowa. Kada mu bari wasu 'yan tsirari daga cikinmu da ke amfani da siyasa da addini da ƙabilanci su kawar da hankalinmu."

  2. Zelensky ya katse cinikayyar gas na Rasha zuwa ƙasashen Turai

    An kawo ƙarshen hada-hadar tura iskar gas daga Rasha zuwa Turai ta cikin Ukraine, matakin da zai kawo karshen cinikayya mai rahusa tsakanin Rasha da Tarayyar Turai.

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ƙi bari a ci gaba da wannan harkar yana cewa hakan na taimaka wa yakin da Rashar ke yi da ƙasarsa.

    Ya bai wa Turai shekara ɗaya ta shirya rufe bututan da ake amfani da su tsawon shekaru wajen tura gas mai sauƙi zuwa ƙasashensu.

    Hukumar gudanarwar Turai ta ce tasirin ba shi da wani yawa saboda tsare-tsare da suka aiwatar cikin tsanaki na samun gas daga ƙasashen Amurka, da Qatar da kuma Norway.

  3. Barka da sabuwar shekara

    Maraba da shigowa shafin labarai kai-tsaye na ranar Laraba - ta bawa ranar samu. Barkanmu da sabuwar shekara kuma dai.

    Umar Mikail ne zai kawo rahotonni na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya bisa kulawar Haruna Ibrahim Kakangi.

    Ku biyo mu.