Arsenal za ta ci gaba da cefane kan a rufe kasuwar
cinikayyar yan kwallo ranar 1 ga watan gobe, harma tana son sayen dan wasan Bayer
Leverkusen mai tsaron baya, Piero Hincapie.
Arsenal ta daɗe tana neman mai tsaron baya daga gefen
hagu, yanzu tana fatan sayen ɗan kwallon tawagar Ecuador.
Hincapie wanda yake da kunshin yarjejeniyar fam miliyan
52 ga duk mai son sayensa, daidai da sama da naira biliyan 315, yana kumas son barin
kungiyar Jamus a bana, .
Ya buga wasa 166 a dukkan karawa a Leverkusen tun bayan
da ya koma kungiyar a 2021 – yana kuma cikin yan wasan da suka lashe Bundesliga
a 2023/24.
Kawo yanzu Arsenal ta kashe sama da fam miliyan 200 wajen
sayen sabbin yan wasa a bana, kwatankwacin sama da naira biliyan 412 kenan
Gunners tana fatan sayar da Fabio Vieira da Reiss Nelson da
Oleksandr Zinchenko da sauransu kafin kasuwar cinikin yan kwallo ta ci ta watse.
Haka kuma Gunners tana son zawarcin Jakub Kiwior, wanda
Porto ke son saya da sauran manyan kungiyoyin Turai.