Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 07/11/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 07/11/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza da Umar Mikail

  1. Kamfanin rarraba wutar lantarki na AEDC ya kori ma'aikata 800

    Kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja ya kori ma'aikatansa 800, a daidai lokacin da ƙasar ke ci gaba da fuskantar da matsalar wutar lantarki da tsadar rayuwa.

    Jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito cewa AEDC ya ɗauki matakin ne a wani ɓangare na sake fasalin kamfanin, da ke bai wa birnin Abuja da jihohin Nasarawa da Neja da Kogi wutar lantarki.

    Bayanai sun ce tun da farko kamfanin ya sanar da korar ma'aitaka 1,800 ne kafin daga bisani ya rage su zuwa 800, bayan jerin tattaunawa da ƙungiyoyin ma'aikatan lantarki da sauran masu ruwa da tsaki a ƙasar.

    Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar tsadar wutar lantarki da rashin wutar a wasu wurare a faɗin ƙasar.

  2. Tesla ya amince da biyan Elon Musk dala tiriliyan ɗaya

    Masu hannun jari a kamfanin ƙera motoci na Tesla sun amince da biyan shugaban kamfanin Elon Musk dala tiriliyan ɗaya

    Bayan sanarwar, Mista Musk, wanda dama tuni ya shiga jerin attajiran duniya, ya hau kan dandamali inda ya yi rawa yana ambaton sunansa.

    Domin samun wannan kuɗi, dole ne Mista Musk ya ɗaga darajar kamfanin Tesla a tsawon shekara 10.

    Sabon albashin ya janyo suka, amma kamfanin Tesla ya haƙiƙance cewa Mista Musk zai iya barin su idan ba a amince da biyan sa kuɗin ba.

  3. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannna lokaci domin kawo muku halin a duniya ke ciki.

    Kada ku manta da shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa