Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman labarai na wasanni a faɗin duniya daga 15 zuwa 21 ga watan Yunin 2025.

Taƙaitattu

  • Real Madrid ta fara da canjaras a Club World Cup
  • Barcelona ta ɗauki golan Espanyol Joan Garcia
  • An fitar da jadawalin sabuwar kakar Premier League
  • An sake buɗe kasuwar saye da musayar 'yanwasa
  • Real Madrid ta sayi matashi Mastantuono daga Argentina
  • Italiya ta naɗa Gattuso sabon kocinta
  • Sabbin dokokin da Fifa ta ɓullo da su a gasar Club World Cup
  • Inter Miami ta Messi ta fara Club World Cup da canjaras
  • Abin da ya kamata ku sani kan Fifa Club Wold Cup 2025

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Chelsea ta fara Club World Cup da nasara

    Chelsea ta buɗe wasannin gasar kofin duniya ta Club World Cup da nasarar doke Los Angeles FC 2-0 a gaban tsirarun 'yankallo da ba su kai rabin filin wasa na Mercedes-Benz ba da ke birnin Atlanta na Amurka.

    Pedro Neto ne ya fara cin ƙwallo tun kafin a tafi hutun rabin lokaci, sai kuma Enzo Fernandez da ya ci ta biyu a minti na 79.

    Chelsea na Rukunin D tare da Flamengo ta Brazil, da Esperance ta Tunisia. Flamingo ce ta ɗaya a rukunin bayan doke Esperance 2-0.

  2. Bournemouth ta sayi Truffert daga Rennes

    Ƙungiyar Bournemouth ta Ingila ta sayi ɗanwasan baya Adrien Truffert daga Rennes kan fan miliyan 14.4.

    Ɗan Faransan mai shekara 23 da ke buga baya a gefen hagu ya saka hannu kan yarjeejniyar shekara biyar.

    Yarjejeniyar ta ƙunshi fan miliyan 11.4 da za a biya da kuma yiwuwar miliyan uku na tsarabe-tsarabe, yayin da ita kuma Rennes ta nemi a biya ta kashi 10 cikin 100 na kuɗin idan wani kulob ɗin ya sayi ɗanƙwallon.

    Shi ma ɗanwasan baya na Bournemouth Milos Kerkez na tattaunawa da Liverpool don komawa ƙungiyar.

  3. Barkanmu

    Mun sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye na duniyar wasanni na ranar Talata.

    Umar Mikail ne zai ci gaba da kawo muku rahotonnin.

  4. An sake buɗe kasuwar saye da musayar 'yanwasa

    Kasuwar saye da musayar 'yanwasa ta bazara ta sake buɗewa 'yan kwanaki bayan zangon farko.

    Ƙungiyoyin Premier League ta Ingila za su iya yin sayayya ko sayarwa har zuwa ƙarfe 7:00 agogon Najeriya da Nijar na ranar Litinin, 1 ga watan Satumban 2025.

    An buɗe zangon farkon daga ranar 1 zuwa 15 ga watan Yuni domin bai wa ƙungiyoyin da ke fafatawa a gasar kofin duniya ta Club World Cup damar yin cefane.

    A zangon farkon, Manchester City ce kan gaba wajen kashe kuɗi, inda ta kashe fan miliyan 116.2 wajen ɗaukar Tijjani Reijnders, da Rayan Cherki, da Rayan Ait-Nouri, da kuma Marcus Bettinelli.

    Real Madrid ma ta ɗauki 'yanwasa uku da suka haɗa Alexander-Arnold, da Dean Huijsen, da Franco Mastantuono.

  5. PSG ta zazzaga wa Atletico ƙwallaye huɗu

    Zakarun nahiyar Turai Paris St-Germain sun yi wa Atletico Madrid ta Sifaniya ruwan ƙwallaye 4-0 a wasan farko na cikin rukuni na gasar kofin duniya ta Club World Cup da Amurka ke karɓar baƙunci.

    PSG ta Faransa ce ta mamaye farko-farkon wasan da 'yankallo 80,619 suka halarta a filin wasa na Bowl da ke Pasadena.

    Fabian Ruiz ne ya fara jefa wa Atletico ƙwallo a raga, sai Vitinha da ya yi kwance-kwance a da'irar bayanta kuma ya ɗaɗa ƙwallo a raga kafin a tafi hutun rabin lokaci.

    Julian Alvarez ya zaci ya farke wa Atletico ƙwallo ɗaya amma sai alƙalin wasa ya ƙwace ta saboda ƙetar da Koke ya yi wa ɗanwasan PSG kafin ta shiga raga.

    A minti na 78 ne kuma aka kori ɗanwasan Atletico Clement Lenglet bayan ɗaga masa katin gargaɗi karo na biyu sakamakon nuna fushinsa kan yadda alƙalin wasa ya ƙi hura laifin da yake tunanin an yi wa golansu Oblak.

    Senny Mayulu da Lee Kang-in ne suka ci sauran ƙwallayen.

    Sakamakon ya sa PSG ta zama ta ɗaya da maki uku a Rukunin B. Botafago RJ ta Brazil ce ke biye da maki uku ita ma bayan doke Seatle Sounders ta Amurka 2-1.

  6. Bayern Munich ta antaya ƙwallaye 10 a ragar Auckland City

    Zakarun gasar Bundesliga ta Jamus Bayern Munich ta ɗura ƙwallaye har 10-0 a ragar Auckland City yayin wasanta na farko a zagayen rukuni na gasar kofin duniya ta Club World Cup da ke gudana a Amurka.

    Shi ne adadin ƙwallaye mafi yawa da aka taɓa ci a tarihin gasar.

    Tawagar ta Vincent Kompany ta lallasa Auckland ta ƙasar New Zealand ne da kwallaye uku da Jamal Musiala ya ci, Kinsley Coman ya ci biyu, Olise ma ya ci biyu, Muller ma ya ci biyu, sai Boey da ya ci ɗaya.

    Tun kafin a tafi hutun rabin lokaci Bayern ta antaya ƙwallo shida a raga, wanda ya ba ta damar ɗrewa saman teburin Rukuni na C da maki uku.

    Tana tare da Boca Juniors ta Brazil, da Benfica ta Portugal a rukunin, waɗanda ba su yi nasu wasan ba tukunna.

  7. Real Madrid ta sayi matashi Mastantuono daga Argentina

    Real Madrid ta sayi danwasan tsakiya Franco Mastantuono daga kungiyar River Plate ta Argentina kan kudi yuro miliyan 45.

    A makon da ya gabata ne matashin mai shekara 17 ya zama mafi kankantar shekaru da ya taka wa kasarsa Argentina leda a wasan neman shiga gasar Kofin Duniya ta 2026.

    Sai a ranar 18 ga watan Agusta kwantaragin shekara shida da ya saka wa hannu zai fara aiki idan ya cika shekara 18 da haihuwa.

    Shi ne na uku da Madrid ta ɗauka a wannan bazarar bayan Alexander-Arnold daga Liverpool, da Dean Huijsen daga Bournemouth.

  8. Maraba

    Barkammu da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye na duniyar wasanni na ranar Litinin.

    Ku biyo mu domin sanin yadda take kayawa a gasar kofin duniya ta Club World Cup.

  9. Italiya ta naɗa Gattuso sabon kocinta

    Italiya ta naɗa tsohon ɗanwasanta Gennaro Gattuso a matsayin sabon kocin da zai jagoranci tawagarta ta ƙwallon ƙafa.

    Tsohon tauraron AC Milan ɗin ya maye gurbin Luciano Spalletti, wanda ya bayyana korarsa da aka yi yayin taron manema labarai a makon da ya gabata.

    Gattuso mai shekara 47 ya buga wa ƙasar tasa wasa 73 a matsayin ɗanwasa kuma yana cikin tawagarta da ta lashe gasar Kofin Duniya ta 2006.

    Italiya ta lashe gasar Kofin Duniya biyu a tarihi, kuma ita ce ta cinye kofin gasar nahiyar Turai ta Euro 2020 amma kuma ta kasa samun gurbi a gasar da aka sake yi a shekarar da ta gabata.

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta Italiya ta ce za ta gabatar da Gattuso ga 'yanjarida a ranar Alhamis.

  10. Sabbin dokokin da Fifa ta ɓullo da su a gasar Club World Cup

    Albarkacin gasar kofin duniya ta kulob-kulob da aka fara a Amurka, hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya Fifa ta ƙaddamar da wasu sauye-sauye game da dokokin wasannin.

    A karon farko, gasar ta Club World Cup ta faɗaɗa zuwa ƙungiyoyi 32 maimakon bakwai da aka yi a 2023.

    Kyamara a jikin alƙalin wasa

    Daga wannan gasar, alƙalan wasa za su maƙala kyamara haɗe da abin maganar da ke rataye a jikin kunnensu, wadda za ta dinga ɗaukar abin da ke faruwa kai-tsaye kamar yadda suke gani a cikin fili.

    Za a dinga saka bidiyon cikin hotunan da masu kallo gani a talabijin, amma ba za a dinga nuna abu maras daɗin gani ba - kamar ƙeta ko kuma faɗa tsakanin 'yanwasa.

    "Hikimar ita ce kawai do a daɗaɗa wa masu kallo a talabijin," a cewar Pierluigi Collina, shugaban kwamatin alƙalan wasa lokacin da yake sanar da matakin.

    Amfani da Ƙirƙirarriyar Basira wajen gano satar gida (offside)

    Duk da cewa aiki da fasaha wajen gano satar gida ko kuma offside yayin wasa ba sabon abu ba ne, za a yi amfani da fasahar ta wani ɓangare daban da wanda aka saba gani ta hanyar amfani da Ƙirƙirarriyar Basira ko kuma Artificial Intelligence a Turance.

    Kyamarori 16 ne za su dinga bayar da hotunan abubuwan da ke faruwa zuwa ga na'urar ta AI, wadda ita kuma za ta dinga sanar da alƙalan wasa cikin gaggawa da zarar ɗanwasan da ke offside ya taɓa ƙwallo.

    Fifa na fatan wannan mataki zai taimaka wajen rage yawan lokacin da ake ɗauka kafin yanke hukunci kan satar gida.

    Akwai yiwuwar hakan zai sa a dinga ɗaga tuta da wuri, da rage yawan lokacin da ake ɗauka kafin busa offside ɗin kansa - ba kamar daɗewar da ake gani ba kafin yanzu da ake amfani da na'urar VAR kawai.

    Sannan kuma za a dinga nuna wa 'yankallo bidiyon da na'urar VAR ta ƙirƙira na offside ɗin.

    Sabbin dokoki kan masu tsaron raga

    Wani abin ba sabo ba ne, amma dai masu tsaron raga za su fuskanci cikin sauri ba kamar a baya ba idan suka riƙe ƙwallo saboda ɓata lokaci.

    Dokar ta ce masu tsaron raga kada su riƙe ƙwallo a hannu sama da daƙiƙa ko kuma sakan shida, amma kuma alƙalan wasa ba su fiya hukunta su da sauri ba idan suka aikata hakan.

    Yanzu alƙalin wasa zai yi wa gola gargaɗi daga daƙiƙa biyar - ta hanyar ƙirgawa da hannu - daga nan kuma dole ne golan ya saki ƙwallo daga hannunsa kafin daƙiƙa ta takwas.

    Idan mai tsaron raga ya ƙi sakin ƙwallon a daƙiƙa takwas, za a hukunta kulob ɗinsu ta hanyar bai wa abokan hamayyarsu bugun kwana, maimakon bugun tazara da ake bayarwa a baya.

  11. Mexico ta fara kare kofinta na Gold Cup da nasara kan Dominica

    Tawagar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Mexico ta fara kare kambinta na gasar Gold Cup bayan nasarar doke Dominican Republic 3-2 ranar Asabar a birnin Los Angeles na Amurka.

    Kafin wasan, sai da aka tilasta wa tawagar ta Mexico sauya masauki saboda fargabar tsaro sakamakon zanga-zangar da Amurkawan ke ta yi game da samamen da dakarun shige da fice ke yi kan 'yan cirani.

    Kofin na Gold Cup, shi ne mafi daraja tsakanin ƙasashen yankin nahiyar Amurka ta Arewa da Tsakiya da kuma Carribbean.

    Ɗanwasan West Ham na Mexico Edson Alvarez ne ya fara cin ƙwallo ana dab da tafiya hutun rabin lokaci. Sai kuma ɗanwasan Fulham Raul Jimenez da ya ƙara biyu ana dawowa daga hutun, kodayake Peter Gonzalez ya farke wa Dominica ɗaya babu daɗewa.

    Ɗanwasan baya na Dominica Cesar Montes ya ci gida bayan Alvarez ya saka wa ƙwallo kai, inda wasa ya zama 3-1. Amma ba a tashi ba sai da Edison Azcona ya farke wa Dominica ta biyu.

    Yanzu Mexico ce ta ɗaya da maki uku a Rukunin A. Nan gaba Costa Rica da Siriname za su fafata domin sanin wacce za ta yi ta biyu da ta uku.

  12. Tarihin Fifa Club World Cup

    An fara gudanar da gasar a 2000 a Brazil kuma Corinthians ce ta fara lashe kofin, bayan nasara a kan Vasco da Gama 4-3 a bugun fenariti a wasan ƙarshe.

    Necaxa ta Mexico ce ta uku, sakamakon doke Real Madrid 4-3 a bugun daga kai sai mai tsaron raga a gasar da ƙungiyoyi takwas suka kece raini.

    Sai dai ba a ci gaba da wasannin ba daga tsakanin 2001 zuwa 2004, bayan durku shewar kamfanin da Fifa ke haɗakar tallata gasar wato International Sport and Leisure (ISL).

    An ci gaba da wasannin a duk shekara tun daga 2005 har zuwa 2023 daga nan aka sauya fasalin gasar da cewar za rinƙa gudanar da ita duk shekara huɗu daga 2025.

    Lokacin da aka fara wasannin a 2000 a Brazil ana kiran gasar da sunan Intercontinental Cup da ake yi tsakanin ƙungiyoyin nahiyar Turai da waɗanda suka yi abin kirki a Copa Libertadores, wato daga nahiyar Kudancin Amurka.

    A shekarar 2005 aka haɗe wasannin Intercontinental Cup da Fifa Club World Cup Championship daga nan aka sauya sunan gasar zuwa Fifa Club World Cup a 2006.

    Daga lokacin duk ƙungiyar da ta zama gwarzuwa, sai a bata kofin Fifa Club World Cup da takardar shaidar Fifa World Champions.

    Real Madrid ce kan gaba a yawan lashe kofin inda ta ɗauka har sau biyar a tarihi a gasar da Corinthians ta fara lashewa a 2000 a Brazil.

    Ƙungiyoyin Sifaniya sun ɗauki kofin sau takwas, sai guda huɗu a Ingila da suka lashe Fifa Club World Cup da suka hada da Manchester United da Chelsea da Liverpool da kuma Manchester City.

    Manchester City ce ke riƙe da kofin, wadda ta doke Fluminense 4–0 a wasan ƙarshe a 2023.

  13. Inter Miami ta Messi ta fara Club World Cup da canjaras

    Ƙungiyar Inter Miami ta su Lionel Messi ta fara wasan kofin duniya na kulo-kulob da canjaras tsakaninta da Al Ahly ta ƙasar Masar a yau Lahadi.

    Miami wadda ke garin da ke karɓar baƙuncin gasar a Amurka, ta dogara kacokam kan mai tsaron ragarta Oscar Ustari kafin ta tsira da maki ɗayan saboda yadda hana ƙwallaye shiga ragarsa har ma ya lashe kyautar mafi hazaƙa a wasan.

    Shi ne wasa na farko a gasar ta Fifa Club World Cup da aka yi wa kwaskwarima, inda ƙungiyoyi 32 za su nemi lashe kofin a Amurka.

    Messi ya kusa cin ƙwallo bayan dawowa daga hutun rabin lokaci daga bugun tazara, da kuma wani shot da ya buga daga nesa amma sai golan Ahly Mohamed el Shenawy ya doke ƙwallon.

    Inter Miami na Rukunin A tare da Al Ahly, da FC Porto ta Portugal, da kuma Palmeiras ta Brazil.

  14. Maraba

    Barka da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye, wanda ke kawo rahotonni game da duniyar wasanni.

    Sunana Umar Mikail, kuma ni ne zan jagoranci shafin daga yanzu zuwa lokuta masu zuwa.

    Ku biyo mu.