Sabbin 'yansanda nawa Najeriya ke buƙatar ɗauka a kowace shekara?

Asalin hoton, NPF.GOV.NG
Yayin da rudunar ƴansandan Najeriya ta bayyana aniyarta na sake ɗaukar ƴan sanda dubu 30 a kowacce shekara, masu sharhi kan harkokin tsaro a ƙasar na ganin wannan adadi ba zai cike giɓin ƙarancin jami'an da ake da shi ba a ƙasar.
Masana tsaron na wannan tsokaci ne bayan da babban sufeton ya ce Najeriyar za ta ci gaba da ɗaukar ƴan sanda dubu 30 kowacce shekara.
Masanan na ganin cewa la'akari da irin ƙalubalen da ake fuskanta daga ɓangaren tsaro a Najeriya, adadin jami'an yan sandan da ake buƙata domin shawo kan matsalar, dole a ruɓanya yawan adadin.
SP Habibu Shehu Yakawada mai murabus ɗaya ne daga cikin masu wannan ra'ayi, ya ce kawo yanzu adadin 'yansandan Najeriya ba su kai 500,000 ba, kuma idan aka yi la'akari da jihohin da ake da su a Najeriya adadin ya gaza.

















