Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 17/02/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 17 ga watan Fabrairun 2026.

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed da Aisha Babangida

  1. Na yi amannar Iran za ta amince da yarjejeniyar nukiliya - Trump

    Shugaba Trump ya ce ya yi amanna Iran na son a cimma yarjejeniya akan shirinta na Nukiliya. Ya yi kalaman ne a yammacin ranar da za a fara zagaye na biyu na tattaunawar da ake tsakanin wakilan Amurka da na Iran a Geneva wanda Oman ke shiga tsakani.

    Wakilin BBC ya ce, Mr Trump ya ce ba ya tunanin Iran na son abin da zai biyo baya idan har ta ki yarda ta kulla yarjejeniyar sannan kuma ya yi amanna Iran din na son a cimma yarjejeniyar.

    A nata ɓangaren ma'aikatar harkokin wajen Iran ta bakin mai magana da yawunta, ya ce yanzu Amurka ta fi nuna da gaske take musamman kan batun matsayarta kan batun nukiliya .

  2. Farawa

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Talata daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.