Amurka ta fara aiwatar da ƙarin harajin kashi 25 kan karafa da aka shigar da su ƙasar
A yau ne Amurka ta fara aiwatar da shirinta na sanya harajin kashi 25 cikin 100 kan duk wasu ƙarafa da sanholo da ake shigar da su amurka daga duka ƙasashen duniya.
Ƙasar Australia na daga cikin ƙasashen da suka fara korafi kan wannan mataki inda Firaministanta Anthony Albanese ya ce wannan matakin da shugaba Trump ke ɗauka bai dace ba.
Ya ƙara da cewa matakin ya saba wa ginshikin abotar da ke tsakanin ƙasashen biyu ya kuma saɓa wa fa'idar da ƙawancen tattalin arzikinsu ya samar sama da shekaru 70.
Mista Trump dai ya kare manufofinsa a wani taro da ya yi da shugabannin manyan kamfanonin Amurka a fadar White House a jiya Talata