Sai da safe
Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafin.
Ku kasance tare da mu gobe da safe domin samun wasu sababbin rahotonnni da suka shafi rayuwarku.
Umar Mikail ke cewa sai da safenku.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 12/03/2025
Haruna Ibrahim Kakangi, Abdullahi Bello Diginza, da Umar Mikail
Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafin.
Ku kasance tare da mu gobe da safe domin samun wasu sababbin rahotonnni da suka shafi rayuwarku.
Umar Mikail ke cewa sai da safenku.
Majalisar Dattijon Najeriya ta nemi gwamnatin tarayyar ƙasar ta kafa sansain soja na dindindin a ƙaramar hukumar Gwer ta Yamma da ke jihar Binuwai.
Majalisar ta ce ya kamata a yi hakan ne saboda a inganta tsaron mazauna yankin sakamakon yawan hare-haren 'yanbindiga a jihar da ke tsakiyar Najeriya.
Sanata Tartenger-Zam daga Binuwai ne ya gabatar da ƙudirin gaggawa ga majalisar a zamanta na yau Laraba, inda baki ɗayan 'yanmajalisar suka amince da yin kiran.
Ɗanmajalisar ya soki yadda jami'an tsaro suke gaza kai ɗauki cikin gaggawa duk lokacin da aka fuskanci hari daga 'yanbindigar da ke iƙirarin makiyaya ne.
Kafofin yaɗa labarai a Najeriya na cewa a ranar Lahadi da Litinin ma sai da aka kashe mutum huɗu a yankin bayan wasu mahara sun auka yankin na Gwer.
Iran ta ce ta karɓi wata wasiƙa daga wajen Shugaban Amurka Donald Trump da ke bukatar sake ƙulla sabuwar yarjejeniya kan makamin nukiliyarta.
Ba a bayyana abin da wasiƙar ta ƙunsa ba a baianar jama'a
Sai dai a makon da ya gabata Mrista Trump ya ce Iran ɗin za ta fuskanci matakin soji matukar ta ƙi amincewa da yarjejeniyar shirinta na makamin nukiliya.
Jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya yi watsi da buƙatar tattaunawar.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Rasha "ba za ta ji da daɗi ba" idan ta ƙi amincewa da yarjejeniyar tsagaita a yaƙin Ukraine.
"Akwai abubuwa da za a iya da ba za su yi daɗi ba a fannin harkokin kuɗi. Zan iya yin abubuwa a fannin kasuwanci," in ji shi lokacin da yake magana da manema labarai a fadar White House.
"Lamarin zai yi wa Rasha muni. Ba ni son na yi hakan, saboda zaman lafiya nake nema.
"Na haɗu da mutumin da bai shirya karɓar zaman lafiya ba, amma yanzu ya amince da zaman lafiyar."
Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Katsina ta ce ta daƙile wani harin 'yanfashin daji tare da kuɓutar da mutum 30 da aka yi garkuwa da su.
Wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Abubakar Sadiq, ya fitar a yau Laraba ta ce lamarin ya faru ne a ƙaramar hukumar Faskari.
"Da misalin ƙarfe 1:00 na daren yau muka samu rahoto cewa wasu da ake zargin 'yanfashin daji ne ɗauke da manyan makamai sun kai hari ƙauyen Unguwar Sarkin Fulani tare da sace mutum 30," in ji sanarwar.
Bayan samun rahoton ne kuma dakaru suka kutsa "tare da yi wa maharan kwanton ɓauna, inda suka yi musu ɓarin wuta".
Ya ƙara da cewa babu wanda ya ji rauni cikin mutanen, sannan sun yi nasarar kuɓutar da dabbobi a hannun 'yanfashin.
Likitoci a Australia sun ce wani maras lafiya ya kafa tarihin zama mutum na farko a duniya da aka sallama daga asibiti da dasasshiyar zuciya, yayin da yake dakon samun zuciyar da za a yi masa dashe da ita.
Mutumin ɗan kimanin shekara 40, ya sake kafa wani tarihin inda ya rayu tsawon kwanaki 100 da wata na'urar ƙarfe kafin ya yi nasarar samun zuciyar mutum.
Likitocin sun ce suna fatan dashen na'urar ƙarfen wadda ke tunkuɗa jini zuwa sassan jiki da kuma huhu za ta maye gurbin buƙatar yi masa dashen zuciyar ma baki ɗaya.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya ce samun dawwamammen tsaro a Ukraine ya danganta ne da irin matakan da aka ɗauka na hana Rasha kai wa Ukraine hari a nan gaba.
Mista Rubio ya ce kamar kowacce ƙasa a duniya, Ukraine na son dawwamammen tsaro da zaman lafiya a ƙasarta, suna kuma son su tabbatar da cewa ba su ƙara fuskatar wata matsalar tsaro ba.
Sakataren harkokin wajen na Amurka, ya ce yarjejeniyar da za a kulla tsakanin Amurka da Ukraine kan ma'adinan ƙasa na Ukraine za ta sanya Amurka ta zamo tana da muradi a ɓangaren tattalin arziƙi da tsaron Ukraine.
Sai dai bai bayyana hakan a matsayin wani alwashi na tsaro ba.
Mista Rubio ya buƙaci Rasha ta yi tunanin dakatar da duk wasu hare-hare, in kuma ba ta yi hakan ba za ta sanya Amurka ta fara tababa kan takamaiman abin da Rashar ke son cimmawa.
Tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya ce babu abin da zai faru idan majalisar dokokin jihar ƙarƙashin jagorancin Amaewhule sun tsige gwamnan jihar, Siminalayi Fubara.
A wata hira da manema labarai da ya gabatar ranar Laraba a Abuja, Mista Wike ya ce ƴanmajalisar ba su yi laifi ba idan suka yanke shawarar tsige Fubara, saboda ya aikata laifukan da suka cancanci a tsige shi, ciki kuwa har da riƙe musu albashi na tsawon watanni.
''Idan har ka aikata laifin da ya kamata a tsigekan, mene ne laifi idan an tsigekan? ba laifi ba ne ,kundin tsarin mulki a tanadi hakan...'' a cewar Mista Wike - wanda shi ne minitan Abuja.
“Idan ka yi abin da ya saɓa kundin tsarin mulki, kuma majalisa ta ga dacewar tsigeka, dole a tsigeka, babu abin da zai faru,'' a cewarsa.
“Na ji mutane na cewa: ‘Idan aka tsige shi hakan zai kawo hargitsi da rashin zaman lafiya, wannan shirme ne babu abin da zai faru.”
Gwamnan Fubara ya samu matsala da tsohon gwamnan jihar, bayan soma gudanar da mulki, wani abu da ya saƴansiyasar biyu suka ja zare a fagen siyasar jihar, mai arzikin man fetur.
Rahotanni sun ce sabon faɗa ya ɓarke a yankin Tigray da ke arewacin ƙasar Habasha yayin da ƙungiyar ƴantawaye ta TPLF ke fama da rikicin karbe mulki.
Shugaban yankin Getachew Reda, ya zargi ɓangaren da shugaban ƙungiyar ta TPLF ke jagoranta da ƙaddamar hare-hare a babban birnin yankin Mekelle tare da ƙwace birni na biyu mafi girma a yankin abin ya ya cutar da farar hula da dama.
Ana fargabar cewa rikicin zai iya dawo da yaƙin basasa a yankin.
Rundunar ƴansandan birnin Tarayya Abuja ta sanar da kashe wani ƙasurgumin ɗanbindiga mai garkuwa da mutane, Dogo Saleh da ya birnin.
Kakakin rundunar ƴansandan birnin, SP Josephine Adeh ta shaida wa BBC cewa ɗanbindigar tare da yaransa sun addabi wasu sassan birnin Abuja, inda suke ayyukan garkuwa da mutane.
Ta ƙara da cewa sakamakon bayanan sirri da suka samu kan maɓoyar ɗanbindigar ya sa suka tura jami'ai maɓoyar domin kama shi.
''Sai dai sakamakon gumurzun harbe-harbe da jami'anmu, mun samu nasarar kashe ɗanbindigar da wasu yaransa '', in ji kakakin ƴansandan birnin.
Ta kara da cewa ɗanbindigar - wanda shi ne babban mataimakin shugaban ƴanbidigar - ya yi ƙaurin suna wajen ayyukan ta'addanci a kan titin Abuja zuwa Kaduna.
SP Adeh ta ce a lokacin gumurzun jami'an ƴansanda sun kuɓutar da wasu mutane da ɗanbindigar ke garkuwa da su.
Rasha ta ce dakarunta na ci gaba da sake kwace wasu sassan yankin Kursk da ke kudu maso yammacin Ukraine daga hannun dakarun ƙasar, waɗanda suka ƙwace da yankin a watan Agustan da ya gabata.
Wata cibiyar nazarin yaƙi da ke Amurka ta tabbatar da hare-haren dakarun Moscow a yankin a baya-bayan nan da nufin ƙwace garin Sudzha.
Wani jami'i a wurin ya ce an kashe wata mata tare da raunata 14 a harin makami mai linzami kan Kryvyi Rih.
Jami'an sun kuma ce an kashe ƴan ƙasar Syria huɗu a birnin Odesa lokacin da Rasha ta kai hari kan wani jirgin ruwa.
Jami'an tsaron da ke gadin harabar majalisar dokokin jihar Rivers sun ƙulle ƙofar majalisar tare da hana gwamnan jihar Siminalayi Fubara shiga zauren majalisar.
Cikin wani bidiyo da sakataren yaɗa labaran gwamnan ya wallafa shafinsa na Facebook ya ce Fubara ya je majalisar ne domin gabatar da kasafin kuɗin jihar na 2025.
Rahotonni daga birnin Fatakwal sun ce tarin jami'an tsaron da aka jibge a harabar sun rufe ƙofar shiga majalisar a lokacin da gwamnan ya hallara tare da tawagarsa domin gabatar da kasafin.
Bayanai sun ambato jami'an tsaron na cewa sun yi hakan ne saboda ba a sanar da su labarin zuwan gwamnan a hukumance ba.
To sai dai Gwamna Fubara ya ce tuni ya aike wa kakakin majalisar, Martins Amaewhule wasikar sanar da shi zuwansa, kuma ya yi ƙoƙarin kiransa a waya tun ranar Talata.
A makonnin da suka gabata ne dai Kotun Ƙolin ƙasar ta yanke hukunci hana CBN bai wa jihar kason kuɗaɗenta daga tarayya saboda rashin gabatar da kasafin kuɗi a gaban halastacciyar majalisar dokokin jihar.
Haka kuma kotun ta yanke hukuncin maido da ƴanmajalisar jihar 27 da suka sauya sheƙa zuwa APC, tare da soke zaɓen ƙananan hukumomin jihar.
To sai dai a ranar 28 ga watan Fabrairu, Fubara ya sanar da yin aiki da hukuncin kotun tare da umartar hukumar zaɓen jihar ta shirya sabon zaɓen ƙananan hukumomin.
Tuni dai hukumar ta saka ranar 9 ga watan Agustan 2025 domin gudanar da sabon zaɓe.
Masu sana'ar haƙar kabari a jihar Kano, sun koka kan yadda mutane ke yi musu kallon masu mugun fata
Isah Garba Tudun Wada, mai sana'ar a unguwar Tudun Wada da ke birnin Kano ya ce duka da cewa suna yin sana'ar ne domin taimaka wa al'umma, amma mutane na tsangamarsu saboda sana'ar tasu.
''Wasu za su riƙa cewa mu masu mugun fata ne, masu mugun tanadi''.
Ya ƙara da cewa yawanci ko dubiyar marasa lafiya ba su zuwa saboda yadda mutane ke yi musu kallo.
''Idan muka je dubiyar marasa lafiya sai su ce mun zo ne mu ja su kabari, kwanan nan ma kanwar mahaifiyata ba ta da lafiya, da na je dubo ta, bayan kwana biyu sai ta rasu, daga nan ƴan'uwa suka fara cewa ai dama na je ne domin na janyota maƙabarta'', in ji shi
''Suka riƙa cewa ai dama tunda muka ga ka zo, mun san baba ta kusa tafiya (mutuwa)''.
Mai sana'ar haƙar kabarin ya ce yakan ɗauke shi minti 20 domin haƙa kabari guda.
''Wannan idan wuri mai laushi ne kena, amma idan wuri na da tauri yakan ɗauke mu sa'a guda ko minti 50,'' in ji shi.
Ƙungiyar Tarayya Afirka, AU ta yi gargaɗin cewa Sudan na cikin hatsarin ƙara rarrabuwa a yaƙin da ƙasar ke fama da shi na kusan shekara biyu.
Ƙungiyar ta yi Allah wadai da mayaƙan RSF da ƙawayenta saboda sanya hannu kan samar da gwamnatin ƴan hamayya a ƙasar.
Rikicin Sudan - da ya fara tun watan Afrilun 2023 ya kashe dubban mutane tare da jefa ƙasar cikin tsananin ƙangin yunwa da yanayin buƙatar tallafi.
Tun bayan ɓarkewar rikicin, sojojin Sudan ke iko da arewaci da gabashin ƙasar, yayin da RSF ke riƙe da mafi yawan birnin Darfur a yammaci da kuma wasu yankuna masu yawa a kudanci.
Kotun Ƙolin Najeriya ta bai wa hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa damar binciken gwamnatin tsohon gwamnan jihar River Peter Odili.
A shekarar 2018 ne dai kakakin majalisar dokokin jihar Rivers na wancan lokaci da babban mai shari'a na jihar suka garzaya kotun da nufin hana EFCC binciken gwamnatin Mista Odili.
A farkon makon nan ne kotun mai alƙalai biyar, ƙarƙashin jagorancin mai shari'a John Okoro suka yi watsi da ƙarar, wani abu da ya buɗe wa hukumar kofar damar binciken gwamnatin tsohon gwamnan na jihar Rivers.
Peter Odili - wanda ya mulki jihar Rivers daga 1999 zuwa 2007 - ya samu umarnin babbar kotun tarayya da ke birnin fatakwal - wanda ya haramta wa EFCC bincikar gwamnatinsa, ko kama shi ko ma gabatar da shi a gaban kotu.
Kotun tarayyar ta kuma hana EFCC binciken kuɗaɗen da jihar River ta samu a zamanin mulkin Peter Odili.
Duk da cewa a 2008 hukumar ta yi yunƙurin ɗaukaka ƙara kan hukuncin, haƙarta bai cimma ruwa ba, lamarin da ya sa umarnin farkon ya ci gaba da kange Mista Odili daga tuhumar EFCC har na tsawo shekara 18.
Kodayake a 2018 kotun ɗaukaka ƙara ta bai wa EFCC damar binciken tsohon gwamnan, amma sai babban mai shari'a da kakakin majalisar dokokin jihar sun garzaya kotun ƙoli domin neman a soke hukuncin kotun ɗaukakar ƙarar.
Ƙungiyar Likitocin Sri Lanka ta ayyana fara yajin aikin kwana guda domin nuna rashin jin daɗinsu kan cin zarafin lalata da aka yi wa wata likita a wani asibitin ƙasar.
Sai dai yajin aikin - wanda zai ƙare a safiyar gobe Alhamis - bai shafi sashen buƙatar kulawar gaggawa da muhimman ɓangarori ba.
Ƴansanda sun ce sun kama wani mutum bisa zargin cin zarafin likitar a asibitin da abin ya faru, da ke birnin Anuradhapura a tsakiyar ƙasar.
Hukumomi sun bayyana mutumin da ake zargin a matsayin wani soja da ya gudu daga aiki.
Zargin cin zarafin likitar - wadda ke bakin aiki - ya haifar da fushi da damuwa a faɗin ƙasar.
Rundunar sojin Pakistan na ci gaba da ƙoƙarin kuɓutar da ɗaruruwan fasinjojin jirgin ƙasa da mayaƙan ƴan'aware suka yi garkuwa da su a lardin Bolachistan ranar Talata.
Majiyar sojin ƙasar ta ce fiye da fasinjoji 150 aka sako, sai dai kawo yanzu ba a san adadin waɗanda ke hannun masu garkuwar ba.
Jirgin ƙasar - na kamfanin Jaffar Express - na ɗauke da fasinjoji 400 a lokacin da mayaƙan ɗauke da makamai suka dasa abin fashewa kan titin jirgin tare da buɗe masa wuta a kusa da wani tsauni a lardin.
Tuni mayaƙan ƙungiyar 'Baloch Liberation Army' suka ɗauki alhakin kai harin.
Ƙungiyar ta kuma buƙaci a saki fursunonin siyasa da ta ce sojojin Pakistan na tsare da su.
Ma'aikatar Ilimi ta Amurka ta ce za ta rage ma'aikatanta da kusan kashi 50 cikin 100 yayin da gwamnatin Trump ke ci gaba da aiwatar da shirinta na rage ma'aikatan tarayya.
Sakatariyar Ilimi, Linda McMahon, ta ce babu wani ɓangaren ma'aikatar da lamarin ba zai shafa ba, kuma wasu ɓangarorin za su fuskanci sauye-sauye da dama.
Tuni dai aka riga aka aika wa ma’aikatan saƙon Imel cewa su yi aiki daga gida a yau Laraba domin za a rufe duka ofisoshin ma’aikatar.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya buƙaci jagororin yankin Naija Delta su shawarci gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara ya yi biyayya ga hukuncin Kotun Ƙolin ƙasar kan rikicin siyasar jihar.
Yayin da yake jawabi da masu ruwa da tsaki na yankin kudu maso kudancin ƙasar, ƙarƙashin ƙungiyar ci gaban yankin Naija Delta a fadarsa da ke Villa ranar Talata, shugaba Tinubu ya ce ya ɗora alhakin samar da zaman lafiyar jihar River a wuyan jagororin ƙungiyar.
Shugaba Tinubu ya buƙaci sadaukarwar jagororin yankin wajen ganin jihar ta yi aiki da kundin tarin mulkin ƙasar, ta hanyar yin biyayya ga dokokin ƙasar don samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.
''Mutunta ɓangaren shari'a muhimmin ɓangare ne a tsarin dimokraɗiyya,'' kamar yadda shugaban ƙasar ya ya bayyana, cikin sanarwar da kakakinsa, Bayo Onanuga ya fitar.
Ya ƙara da cewa ''Wannan ƙasa ce da ake amfani da dokokin na shari'a, inda babu waɗannan dokoki, da ban zama shugaban ƙasa ba, na yi imani da tsarin dimokraɗiyyarmu, muna da fata mai kyau. Ɗan'adam kan yi kuskure, amma idan kotu ta yanke hukunci to zance ya ƙare'', a cewar shugaban ƙasar.
“Don haka ina roƙonku, ku koma gida ku taimaka a yi amfani da hukunci kotu cikin ƙanƙanin lokaci, na ɗora alhakin a kanku, ku taimaka ku shiga tsakani a sirrance da kuma zahiri ku shawarci gwamna, a rungumi hanyar zaman lafiya da kwanciyar hankali'', a cewar Shugaba Tinubu.
A kwanakin baya ne dai kotun ƙolin Najeriya ta yanke hukuncin soke zaɓen ƙananan hukumomin jihar tare da mayar da ƴanmajalisar jihar 27 da suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC ma hamayya a jihar, wani abu da bai yi wa gwamnan jihar daɗi ba.
Kodayake cikin wani jawabi da ya yi wa al'ummar jihar bayan yanke hukuncin gwamnan ya ce gwamnatin jihar za ta bai wa hukumar zaɓen jihar goyon bayan sake shirya wani zaɓen ƙananan hukumomin.
Shugaban Ukraine Vlodymyr Zelensky ya ce yanzu ya rage ga Amurka ne ta shawo kan Rasha ta amince da shirin tsagaita wuta na kwana 30 da Amurka da Ukraine suka tsara a Jeddah.
Da yake magana a fadar White House, shugaba Trump ya ce a yanzu za a fara ƙoƙarin tattaunawa da Rasha.
Mista Trump ya ce cikakken tsagaita wuta ne, Ukraine ta amince da hakan, kuma muna fatan Rasha ma za ta amince.
Za mu gana da su nan gaba yau da gobe, muna da fatan za mu iya cimma yarjejeniya.
Ya zuwa yanzu dai Rasha ba ta ce komai kan yarjejniyar a hukumance ba.