Gasar Firimiya ta Ingila da kuma English Football League za su ci gaba da aiwatar da tsarinsu na watan Ramadan, inda za a rika dakatar da wasa na ɗan lokaci, domin bai wa ƴan wasa Musulmi damar buɗa baki.
Ramadan zai fara a wannan mako kuma zai ɗauki tsawon wata guda. A wannan lokaci, Musulmai na kaurace wa abinci da abin sha daga fitowar alfijir har zuwa faɗuwar rana.
Da yake faduwar rana a Birtaniya tana tsakanin karfe 17:00 zuwa 19:00 agogon GMT a wannan lokaci, wasannin da za a iya dakatarwa zai fi shafar na ranar Asabar da karfe 17:30 da kuma na ranar Lahadi da karfe 16:30.
Kamar yadda aka saba a shekarun baya, shugabannin ƙungiyoyi tare da alkalai za su cimma matasaya kan lokacin da ya kamata a tsayar da wasan domin bai wa ƴan wasa ko jami’ai Musulmi damar buɗa baki.
Ƙungiyoyi da alkalai za su tattauna tun kafin taka leda, domin cimma matsaya kan lokacin da ya kamata a dakatar da wasa domin buɗe bakin.
Kuma ba za a tsayar da wasa ba a lokacin da ake gara ƙwallo, sai idan an samu damar bugun tazara ko jifa da dai sauransu.
A shekarar 2021 ne aka cimma yarjejeniya da ta bai wa ƴan wasa Musulmi damar buɗa baki yayin wasan Firimiya.
An kuma fara ne a wasa tsakanin Leicester City da Crystal Palace a watan Afrilu 2021. An dakatar da wasan a lokacin bugun falan ɗaya a minti na 30 da take leda, domin bai wa Wesley Fofana na Leicester da Cheikhou Kouyate na Palace damar buɗe baki.
Daga cikin sunayen ƴan wasa Musulmi a gasar Firimiya akwai Mohamed Salah da William Saliba da Rayan Ait-Nouri da Amad Diallo da sauransu.
A wata hira da BBC Sport a 2023, tsohon dan wasan Everton Abdoulaye Doucoure ya ce: “A gasar Firimiya kana da ƴancin yin abin da ya dace. Ba za su taɓa yin wani abu da ya saɓa wa addininka ba, kuma wannan abu ne mai kyau.
“Ina azumi kullum, ban taba ƙin yi ko da rana guda ba. Yanzu ya zama al’ada a gare ni, kuma abu ne mai sauki. Horarwa tana tafiya kamar yadda aka saba a Ramadan, amma idan mun je wasannin waje, muna iya cin abinci daga baya fiye da sauran ƴan wasa, don haka mai girki yana shirya mana abinci yadda ya kamata, kamar yadda muke samu a gida. Muna samun abinci halal, don haka babu wata matsala.”
Haka kuma a 2022, tsohon dan wasan Liverpool Sadio Mane ya bayyana cewa ƙungiyarsa tana sauya jadawalin atisaye domin tallafa wa ƴan wasa Musulmi a watan Ramadan.