Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 27/01/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 27 ga watan Janairun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed, Aisha Babangida da Ahmad Bawage

  1. Tsananin sanyi ya yi ajalin aƙalla mutum 20 a Amurka

    Akalla mutane 20 sun mutu sakamakon tsananin sanyi da zubar dusar kankarar da ake fama da su a jihohin kudanci da kuma gabashin Amurka.

    Tsananin Sanyin ya sa wutar lantarki ta dauke inda mutane da dama ke zama ba tare da hasken lantarki ba.

    Kazalika tsananin sanyin ya janyo soke tashi da saukar jiragen sama a kasar.

    Jihohi 20 sun ayyana dokar ta baci yayin da a wasu yankunan Canada ciki har da Toronto kuma ake fama da zubar dusar kankara.

  2. Aƙalla mutum dubu 37 aka tilasta wa barin gidajensu a gaɓar yamma da kogin Jordan - MDD

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce Falasdinawa da dama sun rasa muhallansu a gabar yamma da kogin Jordan a shekarar 2025.

    Hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira a Majalisar ta ce an tursasawa mutane fiye da dubu 37 barin gidajensu a shakerar da ta gabata kuma yawanci saboda ayyukan da rundunar sojin Isra'ila ke yi ne a sansanonin 'yan gudun hijira da ke arewacin yankin.

    Hukumar ta kuma rawaito hare-hare da dama da aka kai wa Falasdinawa wanda Yahudawa 'yan kama wuri zauna a yankin Gabar Yamma da kogin Jordan din suka kai a bara. break

  3. Buɗewa

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Talata daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu ɗaura daga inda muka tsaya a jiya wajen kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Ku kasance tare da mu.