Sai da safe
Nan za mu rufe shafin da ya kawo rahotonni kai-tsaye daga sassan duniya a ranar Lahadi.
Mu hadu gobe da safe domin samun wasu labaran.
Umar Mikail ne ke fatan mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 03/08/2025
Isiyaku Muhammed da Umar Mikail
Nan za mu rufe shafin da ya kawo rahotonni kai-tsaye daga sassan duniya a ranar Lahadi.
Mu hadu gobe da safe domin samun wasu labaran.
Umar Mikail ne ke fatan mu kwana lafiya.

Asalin hoton, Niger State Government
Ƙungiyar neman shugabanci na gari ta Serap ta bai wa gwamnan jihar Neja da ke arewacin Najeriya wa'adin awa 48 domin ya janye umarnin rufe gidan rediyon Badeggi FM ko kuma ya fuskanci matakin shari'a.
Cikin wata wasiƙa da ƙungiyar ta aika wa Gwamna Umaru Bago, shugaban Serap Kolawole Oluwadare ya ce rufe gidan rediyon da ke birnin Minna "saɓa wa doka" ne, kuma ya nemi gwamnan ya mayar musu da lasisinsu.
"Toshe bakin masu suka da sunan tsaron ƙasa keta rantsuwar kama aiki da ka yi ne da kuma ɓata sunan Najeriya a idon duniya game da haƙƙin ɗan'adam," a cewar wasiƙar.
A ranar Juma'a ne Gwamna Bago ya bayar da umarnin rufe gidan rediyon na Badeggi FM nan take tare da ƙwace lasisinsa saboda zargin "tayar da fitina".

Asalin hoton, Getty Images
Ƙasashen Larabawa sun yi Allah wadai da ziyarar da ministan tsaron Isra'ila mai tsattsauran ra'ayi ya kai harabar Masallacin Ƙudus da ke birnin Ƙudus.
Jordan ta kira ibadar da Itamar Ben-Gvir ya yi a wurin abin da ba za a lamunta ba. Saudiyya, a nata ɓangaren, ta ce hakan zai kawo cikas ga ƙoƙarin samar da zaman lafiya a yankin.
Hukumar Falasɗinawa ta ce ziyarar ta ƙetare iyaka.
A cewar wakilin BBC, Birtaniya ta ƙaƙaba wa Itamar Ben Gvir takunkumi saboda yawan tayar da fitina a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.

Asalin hoton, Reuters
Ƙasashen Pakistan da Iran sun amince da ƙarfafa hulɗar kasuwanci tsakaninsu zuwa dala biliyan 10 da kuma aii tare wajen daƙile "ta'addanci".
Yarjejeniyoyin da suka ƙulla a yau Lahadi sun ƙunshi ɓangarori da dama, ciki har da makamashi, da kasuwanci, yayin ziyarar kwana biyu da Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya kai Pakistan.
"Mun saka ƙudirin dala biliyan 10 na kasuwanci muna fatan za mu iya cimma hakan nan da iyakar lokacin da za mu iya," a cewar Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif.
Sharif ya jaddada goyon bayan 'yancin Iran kan shrin nukiliyarta na zaman lafiya, kuma ya caccaki Isra'ila kan hare-haren da ta kai mata a watan Yuni.

Asalin hoton, EPA
Dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Australia, inda suka rufe babbar gadar Sydney Harbour ta ƙasar.
Sun gudanar da zanga-zangar ce kwana ɗaya bayan kotun ƙolin ƙasar ta amince a gudanar da gangamin a ranar Lahadi, duk da mamakon ruwan sama da aka tashi da shi.
Sun ɗaga kwalaye da ke ɗauke da rubuce-rubuce, suna kira ga ƴansiyasa da su sa baki domin kawo ƙarshen yaƙin a Gaza.

Asalin hoton, EPA

Asalin hoton, EPA
Wani dutse a gabashin Rasha ya kama da wuta karon farko cikin sama da shekara 500.
Ƙwararru na cewa akwai yiwuwar yana da alaƙa da gagarumar girgizar ƙasar da aka yi a makon da ya gabata.
Wutar dutsen na Krasheninnikov da ke Kamchatka ya haifar da tashin hayaƙi mai tsawon kilomita shida da tsakar dare. Amma babu wata barazana ga gidajen mutane, in ji hukumar ba da agaji ta Rasha.
'Yan awanni bayan haka, wata babbar girgizar ƙasa ta jawo hukumomi sun fara bayar da gargaɗin tsunami a yankuna uku na lardin.

Asalin hoton, Nema
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa a Najeriya ta ce wani gini mai hawa uku da ya rushe ya rutsa da mutum biyu a Abuja babban birnin ƙasar.
National Emergency Management Agency (Nema) ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:00 na yammacin Asabar a kasuwar kifi da ke unguwar Kado.
"Ginin wanda ake kan ginawa ya rufto ne a daidai lokacin da masu gadi biyu ke cikinsa, inda ɗaya ya tsira ba tare da rauni ba, ɗayan kuma ya ji munanan raunuka," a cewar wata sanarwa a yau Lahadi.
Ta ƙara da cewa tuni aka kai mutumin Asibitin Ƙasa domin kula da lafiyarsa, kuma ta kammala aikin ceto na hadin gwiwa da misalin ƙarfe 4:35 na asubahin Lahadi.

Asalin hoton, Peter Obi
Tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar Labour, Peter Obi ya ce idan ya samu nasarar zama shugaban ƙasar, wa'adi ɗaya na shekara huɗu kawai zai yi kamar yadda ya yi alƙawari.
Obi ya bayyana haka ne a shafinsa na X, inda ya ce ko tsohon shugaban Amurka, Abraham Lincoln wa'adi ɗaya ya yi na shekara huɗu, "sannan John F. Kennedy bai ma ƙarasa wa'adi ɗaya ba, amma ana cigaba da tunawa da su a matsayin shugabanni masu adalci."
Ya ce ko a Afirka, Nelson Mandela ya zama abin koyi a duniya wajen shugabanci na adalci, "amma wa'adi ɗaya kawai ya yi."
"Ba daɗewa a ofis ba ne ke alamta nasara, irin ayyukan da shugaba ya yi ne za a riƙa tunawa. Saboda haka ne nake sake nanata alƙawarin da na yi cewa wa'adi ɗaya na shekara huɗu kawai zan yi idan na zama shugaban Najeriya," in ji shi.
Ya ƙara da cewa ya san ƴan Najeriya ba su cika yarda da maganar ƴan siyasa ba, "amma duk da haka akwai masu cika alƙawari."
"Na ga wani yana rubuta cewa ko da me zan rantse ba zai yarda cewa wa'adi ɗaya zan yi ba, wani kuma ya ce duk wanda ya ce wa'adi ɗaya zai yi ya je asibitin ƙwaƙwalwa."
Obi ya ce ya fahimci abin da suke nufi, amma a cewarsa, yana da tarihi mai kyau wajen cika alƙawari tun daga lokacin da ya fara siyasa a Anambra, inda ya ce wata 48 sun isa duk wani shugaba da ya shirya mulki ya yi abin da ya dace.
"Idan na zama shugaban Najeriya a wa'adi ɗaya zan magance matsalar tsaro, zan yaƙi da talauci in inganta aikin gwamnati, sannan zan fifita ɓangaren ilimi da kiwon lafiya, sannan in yaƙi cin hanci da rashawa. Sannan uwa-uba zan inganta ɓangaren noma ta hanyar amfani da kimiyya da fasaha domin Najeriya ta zama ƙasa mai ciyar da kanta da wasu ƙasashen."

Asalin hoton, EPA
Dubban matasa 'yan darikar Katholika sun kwana a kan tittuna a birnin Rome a lokacin da suke dakon taron addu'a da Fafaroma Leo zai gabatar.
Ana gudanar da irin wannan taro ne musamman ga matasa a duk bayan shekara 25. Kusan mako guda aka shafe matasa na tuɗaɗa Rome daga sassa daban-daban na duniya domin halartar wannan biki, wanda kuma shi ne na farko da Vatican za ta tara fitattun matasa 'yan katholika da suka yi fice a shafukan sada zumunta.
A jiya Asabar, Fafaroma Leo ya halarci taron addua'a da bukukuwan share- fagge kafin babban taron na yau, wanda ake saran ya gabatar da jawabi da harsuna daban-daban.
Ya ce idan har dagaske kunason kusantar Ubangiji to ya zama dole ku kiyayye da kauracewa abubuwa saɓa masa, ku tsarkake zuciyarku ku aikata ayyuka masu kyau.

Asalin hoton, Getty Images
Jami'ai a Amurka sun ce sun ƙaddamar da bincike kan tsohon mai shigar da ƙara na musamman, Jack Smith, wanda ya jagoranci shari'o'i biyu na manyan laifuka kan shugaba Donald Trump kafin zaɓen shugaban ƙasa a shekarar da ta gabata.
Ofishin shigar da ƙara na musamman - wanda ke zaman kansa - an ba da rahoton cewa yana nazartar zarge-zargen da ake yi wa Mista Smith na saɓa dokoki ta hanyar sa kan sa cikin harkar siyasa.
Wakiliyar BBC ta ce dama gwamnatin nan ta nuna sai ta ƙalubalance waɗanda suka zame mata tarnaki da ƙoƙarin ganin-bayanta a lokacin neman mulki.
Mista Smith ne ya jagoranci bincike kan zargin da ake yi wa Mista Trump kan abubuwan da ya gudanar bayan zaɓen 2020 da kuma wani shari'ar kan wasu bayanan sirri.
Nasarar Trump a karo na biyu ne ya sa aka janye kararrakin da ake masa.

Asalin hoton, Dean Lewins/EPA
Dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Australia, inda suka rufe babbar gadar Sydney Harbour ta ƙasar.
Sun gudanar da zanga-zangar ce kwana ɗaya bayan kotun ƙolin ƙasar ta amince a gudanar da gangamin a ranar Lahadi, duk da mamakon ruwan sama da aka tashi da shi.
Sun ɗaga kwalaye da ke ɗauke da rubuce-rubuce, suna kira ga ƴansiyasa da su sa baki domin kawo ƙarshen yaƙin a Gaza.
Shugaban WikiLeaks, Julian Assange na cikin waɗanda suka shiga zanga-zangar, tare da ɗanmajalisar ƙasar, Ed Husic.
A shekarar 2023 ne aka taɓa rufe gadar Sydney Harbour na ƙarshe, lokacin da kusan mutum 5,000 suka gudanar da zanga-zanga.
"Mutanen sun riƙa cewa "Isra'ila kin ji kunya, Amurka kin ji kunya. Muna so a kawo ƙarshen yaƙin."
"An kasa ƙaƙaba wa Isra'ila takunkumi duk da abin da take yi," in ji wata mai suna Zara Williams da ta halarci zanga-zangar ɗauke da yarinyarta.

Asalin hoton, Borno State
Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya ce gwamnatinsa ta fara yunƙurin gyara tsarin birnin jihar domin kiyaye jihar daga ambaliya.
Zulum ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan ziyarar gani da ido da ya yi wajen gyara da ake yi a dam ɗin Alau, inda ya ce har yanzu akwai wasu da suke gini a magudanan ruwa da kuma masu zuba shara suna toshe magudunan ruwa.
"Za mu duba tare da gyara tsarin birnin Maiduguri domin mu tabbatar dukkan magudanan ruwanmu a buɗe suke kuma suna aiki," in ji shi kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Ya yi gargaɗin cewa duk wani gini da aka yi a magudunan ruwa za a rushe su.
Ya ce za su ɗauki matakin rusau ɗin ne domin kare sake aukuwar irin ambaliya da ta auku a ranar 10 ga watan Satumban 2024 a Jere da ke Maiduguri.
A game da fargabar da ake yi a Maiduguri na sake aukuwar ambaliyar, Zulum ya buƙaci ƴan jihar su kwantar da hankalinsu, inda ya ce akwai babbar ma'adana ta dam ɗin Alau ɗin, da ya ce za ta janye ruwan idan ya cika.

Asalin hoton, DSNS Ukraine
An samu tashin gobara a wani defon dakon mai da ke yankin Sochi na Rasha a tekun Bahar Aswad.
Gwamnan yankin, Veniamin Kondratyev, ya ce jirgin Ukraine mara matuki shi ya kai hari kan tankar mai, kuma sama da masu kashe gobara 120 ne suka kai agajin gaggawa zuwa yankin, domin kawo ƙarsehen gobarar.
Shaidu a shafukan sada zumunta sun rinka bada labarin karar fashe-fashe.
Kafin wannan lokaci, Jami'ai a Ukraine sun ce Rasha ta kai hari da makami mai linzami kan gidajen mutane da gine-ginen farar-hula a birnin Mykolaiv da ke kudancin ƙasar.
A Kherson ma, an lalata wata gada da butuntun tura iskar gas.

Asalin hoton, Reuters
Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce ya yi dogon tattaunawa da iyalan 'yan Isra'ila biyu da ake garkuwa da su a Gaza, bayan sakin wani bidiyo da ke nuna mutanen su biyu cikin yanayi na galabaita.
Mista Netanyahu ya ce ya nuna wa iyalan, Evyatar David da Rom Braslavski yanayi na kaɗuwa da ya shiga - da alkawarta cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba, har sai an sake dukkanin sauran mutanen da ke hannun Hamas.
Sannan ya bukaci dukkanin 'yan ƙasar su yi Allah-wadai da Hamas.
A jiya Asabar dubban mutane sun fito zanga-zangar mako mako da aka saba yi a TelAviv domin neman ceto sauran mutanen da ake riƙe da su a Gaza.
Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Lahadi daga nan sashen Hausa na BBC.
Ku kasance tare da mu a wannan shafin da za mu kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.