Iran ta kashe mutumin da aka kama yana yi wa Isra'ila leƙen asiri
Iran ta ce ta aiwatar da hukuncin kisa ga mutumin da aka kama yana yi wa Isra'ila leƙen asiri.
Hukuma ta ce an kama Esmail Fekri a shekarar 2023, kuma yana ƙoƙarin miƙa wa Isra'ila bayanan sirri ne don samun kuɗi.
Wannan ne karo na uku a baya-baya nan da Iran ke aiwatar da hukuncin kisa saboda zargin leƙen asiri ga Isra’ila.
A ranar Lahadi, Isra’ila ta ce ta kama wasu ‘yan ƙasa biyu da ake zargin suna aiki da hukumar leƙen asirin Iran.
Babban alƙalin Iran, Gholamhossein Mohseni Ejei, ya bayyana a ranar Litinin cewa, la'akari da yanayin “yaƙi” da suke ciki, dole ne a gudanar da shari’o’i ga waɗanda ake zargin suna aiki da Isra’ila cikin hanzari.