Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 16/06/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 16/06/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi da Aisha Babangida

  1. Ana tuhumar wanda ya kashe ƴar majalisa a Amurka

    Masu gabatar da ƙara a jihar Minnesota na Amurka sun gabatar da tuhuma kan wanda ake zargi da kashe wata 'yar majalisar democratic da mijinta.

    Sun ce Vance Boulter zai fuskanci hukuncin kisa idan aka same shi da laifi.

    Ana kuma zarginsa da barazana da amfani da bindiga.

    Jami'ai sun bayyana kisan Melissa Hortman da mijinta Mark da kulle-kullen siyasa.

  2. A ina cibiyoyin nukiliyar Iran suke kuma waɗanne ne aka kai wa hari?

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai hare-hare a cibiyoyin nukiliya na Iran a ranar Juma'a 13 ga watan Yuni. Wasu faye-fayen bidiyo da BBC ta gani sun nuna yadda hare-haren suka wakana a cibiyoyi guda biyar.

    Yawancin cibiyoyin a babban birnin ƙasar, Tehran suke - inda wasu faya-fayen suka nuna yadda hare-haren suka ɓarnata wasu gidajen mutane.

    Wata babbar cibiya ita ce Natanz - kimanin kilomita 225 (mil 140) daga kudancin babban birnin ƙasar - inda cibiyar haɓaka ma'adinin uraniun yake.

    Rahotanni daga Iran sun nuna cewa cibiyoyin Natanz da Arak suna cikin cibiyoyin da Isra'ila ke hari.

  3. Bayanan da kuke son sani kan yaƙin Isra'ila da Iran

  4. Kashe Ayatollah Ali Khamenei zai kawo karshen rikici - Netanyahu

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce duk wani shiri na hallaka jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei ba zai rura wutar rikicin da ake yi yanzu ba, hasali zai ma kawo karshen rikicin ne.

    A wata tattaunawa da tashar talabijin ta ABC ta Amurka ta yi da shi ne Netanyahu ya bayyana haka.

    A yayin hirar duk wata tambaya da aka yi masa game da ko Isra'ila na shirin kashe babban jagoran addinin, Netanyahu ya ki kawar da yuwuwar hakan.

    Da aka matsa shi a kan ko za su hari jagoran, sai ya ce : ''Muna yin abin da muke da bukatar yi.''

    "Mun hari manyan masana nukiliyarsu," ya kara da cewa. "Har yanzu muna da sauran aikin da za mu yi a daya bangaren."

    Haka kuma jagoran na Isra'ila ya nuna cewa sun kai wa Iran hari ne domin kare al'umma, domin kare duk wata barazanar nukiliya daga Iran.

    "Yau birnin Tel Aviv, ne gobe kuma New York, ne " in ji shi.

  5. Ko Isra'ila tana da makaman nukiliya?

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya dade yana cewa Iran na kusan da kera makamin nukiliya.

    Amma kuma abin da ya ki fitowa ya tabbatar wanda da yawa aka yi amanna da shi, shi ne cewa, Isra'ila tana da makamana nukiliya na kanta tun daga shekarun 1960.

    Yawancin abin da kiyasin cibiyar hana bazuwar makamai ta duniya ta ce shi ne Isra'ila tana da makaman nukiliya kusan 90.

    Sannan kuma kasar ba ta cikin mambobin da suke cikin yarjejeniyar duniya ta hana bazuwar makaman nukiliya.

    Masu sharhi sun yi amanna Isra'ila na tafiyar da shirinta na nukiliya ne a tashar nukliya ta Dimona, wani birni da ya ke hamadar Negev.

    Isra'ila tana da wata manufa ta boye magana - kuma har kullum ta ki ta tabbatar cewa tana da makaman nukiliya sannan kuma ba ta ce ba ta da su ba.

  6. Babu matakin soji da zai iya kawo karshen nukiliyar Iran - Birtaniya

    Sakataren harkokin wajen Birtaniya, David Lammy, ya ce babu wani matakin soji da zai iya kawo karshen shirin nukiliyar Iran.

    Mista Lamy ya bayyana hakan ne a yayin jawabin da ya gabatar a majalisar dokokin Birtaniya a yau Litinin.

    Ya kuma ce babu hannun Birtaniya a hare-haren da Isra'ila ke kai wa Iran din, yana mai karin bayani da cewa, ''wannan aiki ne na soja kawai da Isra'ila ke yi.''

    Dangane da hare-haren Sakataren ya ce, Isra'ila tana da 'yancin kare kanta da kuma 'yan kasar, amma abin da muka fi son gani shi ne a dakatar da hare-haren da suke kaiwa juna.

    ''Sakonmu ga Isra'ila da Iran karara shi ne - a ja baya - a kai zuciya nesa - kada a yi nisa a shiga rikicin da ba wanda zai iay dakatar da shi,'' in ji shi.

    Sakataren ya ce gwamnatin Birtaniya ta yi kira ga duk 'yan kasarsa da ke Isra'ila da su je su yi rijistar inda suke a ofishin ma'aikatar harkokin waje, don samun bayanai a kai-a kai a kan lamarin da kuma shirin barin kasar.

  7. Shugaban ƴansandan Najeriya ya isa jihar Benue

    Babban Sufeton 'yansandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya isa jihar Benue, da ke yankin arewa maso tsakiyar Najeriya, inda wasu mahara suka hallaka mutane da dama tare da tilasta wasu daruruwa barin gidajensu.

    Jihar ta Benue ta dade tana fama da hare-hare da ake zargin makiyaya da kaiwa.

    Tsawon shekaru ana wannan kashe-kashe na jama'a a jihar ta Benue, inda wasu ke danganta matsalar da rikici tsakanin kabilu ko al'ummomin garuruwa da rikicin filaye tsakanin manoma da makiyaya.

    To sai dai kashe-kashen na wannan makon sun yi yawa kusan ba kakkautawa, inda aka tabbatar da hallaka wajen mutum 160 a hare-haren da ake zargin makiyaya da kaiwa.

    A jiya Lahadi Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci shugabannin hukumomin tsaron kasar da su kawo karshen kashe-kashen a jihar ta Benue.

    A wata sanarwa da fadar shugaban ta fitar, shugaban ya ce abin ya isa haka, kuma a jibi Laraba ne Shugaban zai je jihar da kansa.

  8. Isra'ila ta kai hari gidan talabijin na Iran

    Ministan tsaron Isra'ila, Israel Katz, ya tabbatar da cewa kasarsa ta kai hari gidan talabijin din gwamnatin Iran

    A wata sanarwa da ya fitar, Mista Katz ya ce an kai harin ne bayan mutane da yawa da ke zaune a yankin da tashar take sun tashi.

    Ministan ya kara da cewa Isra'ila za ta kai hari kan wanda ya kira jagoran mulkin-mulka'u na kasar a duk inda yake.

    An ga wani hoton bidiyo na tashar inda wata ma'aikaciya da ke bayar da bayanai kai tsaye ta fice daga dakin watsa labaran lokacin da aka kai harin inda ake iya ganin burbushin ginin na ta sauka a dakin.

    Wani wakilin gidan talabijin din na Iran ya sanya hoton wani sashe na gidan yana cin wuta, a sakamakon harin na Isra'ila.

    A hoton, Younes Shadlou ya ce ba shi da tabbacin ko nawa daga cikin abokan aikinsa aka kashe a harin.

  9. Tinubu zai ziyarci Benue bayan mutuwar mutum 100 a hare-haren jihar

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya soke ziyarar aiki da ya shirya zuwa Kaduna, a maimakon haka zai ziyarci jihar Benue domin jajanta wa al'ummar jihar sakamakon kashe-kashen da aka samua jihar a baya-bayan nan.

    Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce Shugaba Tinubu zai ziyarci jihar a ranar Laraba domin duba halin da jihar ke ciki bayan kashe-kashen da aka samu a ƴan kwanakin nan a jihar.

    Sanarwar ta ce a lokacin ziyarar, shugaba Tinubu zai gana da masu ruwa da tsaki na jihar, da suka haɗa da sarakuan gargajiya da ƴansiyasa da jagororin addini da shugabannin al'umma da kungiyoyin matasa, da nufin lalubo hanyoyin magance rikicin jihar.

    Tuni dai shugaban ya aike da tawagar wakilan gwamnatin tarayya a yau da ta ƙunshi sakataren gwamnatin tarayya da babban sifeton ƴansanda da shugabannin hukumomin tattara bayanan sirri ta ƙasa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro da shugabannin kwamitsocin tsaro a majalisun dokokin ƙasar.

    A ƙarshen mako ne dai aka samu munanan hare-hare a jihar Beneu da suka yi sanadin kashe fiye da mutum 100 a jihar.

  10. Gwamnatin Najeriya ta aika tawagar manyan jami'an tsaro zuwa Benue

    Fadar Shugaban Najeriya ta ce wata babbar tawagar manyan jami’an tsaron Najeriya ta isa jihar Benue domin bayar umarnin yadda za a tunkari matsalar rashin tsaron da jihar ke fuskanta da kuma mai do da kwanciyar hankali.

    Cikin wata sanarwa da ya fitar kakakin shugaba Bola Tinubu, Bayo Onanuga ya ce hakan na zuwa ne bayan umarnin da shugaban ya bai wa shugabannin hukumomin tsaron ƙasar na maido da kwanciyar hankali da tsaro mai ɗorewa a jihar.

    Hakan na zuwa ne bayan hare-haren da ƴanbindiga suka kai a baya-bayan nan kan al’umomi a jihar da rahotanni ke cewa sun kashe mutum 100.

    Baya ga bai wa jami’an tsaron umarnin dakatar da hare-haren, shugaban ƙasar ya umarci gwamnan jihar da ya kira zaman sulhu da kuma tattaunawa tsakanin al’ummomin jihar da ba su ga maciji da juna domin kawo ƙarshen abin da ya kira zubar da jini maras iyaka da kuma samar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin manoma da makiyya da ma sauran jama’a.

    Yayin da ya bayyana kashe-kashen a zaman na rashin imani da kuma mayar da hannun agogo baya, Shugaba Tinubu ya yi kira ga shugabannin siyasa da na al’umma a yankunan da ake rikicin da su daina ingiza wutarsa ta hanyar yin kalamai marasa kan gado da ka iya ƙara tayar da hankula.

    Rahotanni daga babban birnin jihar na Makurdi sun ce yanzu haka jiragen saman soji na ta shawagi samaniyar garin da kewayensa bayan kashe-kashen baya-bayan nan da aka yi a garuruwan Yelwata da Daudu wanda aka ce sun yi sanadin mutuwar kimanin mutum 100.

    Tuni dai babban sufetan ‘yansadan kasar Kayode Ebgetokun ya ziyarci jihar tare da karbe ragamar shugabancin aikin tabbatar tsaro a jihar.

  11. Yayin da hankali ya koma kan Iran, an kashe mutum 20 a Gaza

    Rahotanni daga Gaza sun bayyana cewa fiye da mutum 20 sun mutu a kusa da wuraren raba agaji da Gidauniyar Agaji ta Gaza (GHF) ke gudanarwa – wanda Isra’ila da Amurka ke marawa baya.

    Babban Kwamishinan kare haƙƙin ɗan Adam na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk, ya ce hanyoyin da Isra’ila ke bi wajen yaƙi a Gaza suna haddasa mummunar azaba da ba za a yarda da ita ba.

    Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a kusa da Al-Alam roundabout, kusan kilomita ɗaya daga cibiyar agaji da ke Rafah.

    Wurin ya kasance wajen da ake samun irin waɗannan hare-hare tun bayan fara sabon tsarin raba abinci da Isra’ila ke marawa baya makonni da suka gabata.

    Ma’aikatan bayar da agajin gaggawa sun zargi sojojin Isra’ila da buɗe wuta, yayin da Isra'la ke cewa tana duba lamarin.

    Volker Turk ya zargi Isra’ila da amfani da abinci a matsayin makami tare da neman gudanar da bincike cikakke kan waɗannan hare-haren kusa da wuraren raba agaji.

  12. Ghana ta fara kwashe ƴan ƙasarta daga Iran

    Ghana ta sanar da rufe ofishin jakadancinta a Iran tare da fara gaggawar fitar da ‘yan kasar daga ƙasar, sakamakon rikicin da ke ci gaba da tsanani tsakanin Iran da Isra’ila.

    Ba a san adadin ƴan Ghana da ke zaune a Iran ba, amma ministan harkokin wajen Ghana, Samuel Okudzeto Ablakwa, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa ma’aikatan ofishin jakadancin da dalibai da sauran ƴan ƙasar da ke zaune a Iran za a fitar da su ta kan iyaka ta ƙasa.

    A lokaci guda kuma, gwamnatin Ghana ta yi kira ga ƙasashen Isra’ila da Iran da su nemi mafita ta diflomasiyya kuma su kawo ƙarshen wannan rikici.

    Tun daga ranar Juma’a ne Isra’ila da Iran kai ta kai hare-hare masu kashe rayuka, lamarin da ya haddasa asarar rayukan fararen hula da dama.

  13. Bai kamata a yi shiru kan kashe-kashen Benue ba - Atiku

    Tsohon ɗan takarar shuagaban ƙasa na jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, ya nuna damuwa matuka kan ci gaba da zubar da jini a jihar Benue, yana mai kira ga gwamnatin tarayya da ta ɗauki matakin gaggawa domin kawo karshen matsalar tsaro da ke addabar yankin.

    A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya bayyana halin da ake ciki a matsayin “mummunar masifa” da gwamnatin ta kasa ɗaukar matakin da ya dace a kai.

    Atiku ya ce al’ummar Benue na fama da hare-hare na tsawon shekaru, inda rayuka ke salwanta, kauyuka ke lalacewa, iyalai ke rasa muhallansu.

    "Buƙatarmu ita ce samun zaman lafiya da noma ba tare da fargabar mutuwa ba, da kuma tarbiyyar 'ya'yansu cikin kwanciyar hankali." in ji Atiku.

    Ya jaddada cewa wadannan hakkoki ne da ƙundin tsarin mulki na kasa ya tanada, kuma wajibi ne gwamnati ta kare su.

    Ya kuma yi Allah-wadai da yadda jami’an tsaro ke amfani da karfi da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar lumana a Benue da ke neman kariya daga gwamnati.

    "Hakan ba salon mulki ba ne, illa zalunci ne da cin amanar shugabanci." Ya ce hakan yana nuna yadda gwamnati ta yi biris da kukan jama’a.

    Atiku ya ƙara da cewa matsalar tsaro ba a Benue kaɗai take ba, har da jihohin Plateau da Zamfara da Kaduna da kuma Taraba, inda jama’a ke fuskantar irin wannan hali.

    Ya bukaci shuwagabanni da gwamnatocin jihohi da su mayar da hankali kan kare rayukan ‘yan ƙasa fiye da yin fito na fito da siyasa, ta hanyar aiki da hukumomin tsaro da samar da kayan aiki masu inganci ga yankunan da abin ya shafa.

    Hakazalika, Atiku ya yi kira ga ƴan Najeriya da kada su yi shiru a gaban zalunci. Ya bukace su da su ɗaga murya su nemi adalci da aukar mataki.

  14. Ba a ƙara yi wa cibiyoyin nukiliyar Iran biyu ɓarna ba - MDD

    Shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya (IAEA), Rafael Grossi, ya bayyana cewa ba a ƙara yi wa cibiyoyin nukiliyar Iran da ke Natanz da Fordow ɓarna ba bayan harin da Isra’ila ta kai a ranar Juma’a.

    Grossi ya yi kira ga ɓangarori masu ruwa da tsaki da su nuna hakuri da kauce wa tayar da hankali.

    A cewarsa, yayin da yake jawabi ga kwamitin gudanarwa na IAEA, ya ce an rusa wani sashen gwaji da ke sama a Natanz, amma babu wani alamar hari a sassan karkashin kasa na wurin.

    Sai dai ya ce an lalata wutar lantarki a wurin, lamarin da zai iya haddasa lalacewar injinan tace sinadarin uranium.

    Grossi ya ƙara da cewa an lalata gine-gine guda huɗu a wani wurin nukiliya da ke Isfahan, amma babu rahoton wani lahani a wurin Fordow, wanda aka gina cikin dutse.

  15. Iyalan tsohon shugaban Zambiya da gwamnati sun cimma matsaya kan jana'izarsa

    Bayan kwanaki na rashin jituwa, iyalan tsohon shugaban ƙasar Zambiya, Edgar Lungu wanda ya mutu yana da shekara 68 sun cimma matsaya da gwamnati kan shirye-shiryen jana’izarsa.

    Lungu, wanda ya shugabanci ƙasar daga shekarar 2015 zuwa 2021, ya rasu kwana 11 da suka gabata a Afirka ta Kudu yayin da ake kula da lafiyarsa kan wata cuta da ba a bayyana ba.

    Rahotanni dai sun ce Lungu kafin ya rasu ya bayar da umarnin cewa shugaban ƙasa mai ci, Hakainde Hichilema, kada ya kusanci gawarsa amma iyalinsa yanzu sun amince da shugaban ya jagoranci jana’izar ƙasa da za a yi a ranar Lahadi, 22 ga Yuni.

    A cewar jadawalin, za a kawo gawar Lungu Lusaka a ranar Laraba ta jirgin haya, inda za a tarbe ta da girmamawa ta soja kafin a kai ta gidansa domin kwana.

    Daga ranar Alhamis, za a kai gawar babban ɗakin taro domin jama'a su yi gn shi kuma suyi masa adu'a na tsawon kwana uku.

    Za a kuma gudanar da jana’izar ƙasa a ranar Lahadi, yayin da za a kawoƙkarshen lokacin makoki a washegari.

    Za a binne shi a ranar Litinin a Embassy Park, inda ake binne shugabannin kasar Zambiya.

  16. Poland za ta kwashe ƴan ƙasarta daga Isra’ila

    Poland na shirin kwashe kusan ‘yan kasarta 200 daga Isra’ila a cikin kwanaki masu zuwa sakamakon hare-haren da ke faruwa tsakanin Iran da Isra'ila.

    Yayin da take jawabi a wani taron manema labarai, Mataimakiyar ministar harkokin wajen ƙasar, Henryka Moscicka-Dendys ta ce galibi wadanda za a kwashen masu yawon buɗe-idanu ne.

    "Mutanen da za mu kwashe sun haɗa da waɗanda suka maƙale a Isra’ila ne a matsayin yawon bude ido ko kuma na ɗan gajeren zama kawai," in ji ta.

    Ta ƙara da cewa za a fara jigilar mutanen zuwa birnin Amman na ƙasar Jordan a titi, sannan daga nan su tashi zuwa Warsaw, babban birnin Poland, saboda rufe sararin samaniyar Isra’ila.

  17. Iran ta tsawaita dakatar da jiragen sama wajen shige da fice daga ƙasar

    Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Iran ta bayyana cewa an tsawaita dakatar da duk wasu tashi da saukar jiragen sama har zuwa ƙarfe 02:00 na safe agogon ƙasar a ranar Talata wato ƙarfe 11:30 na dare agogon BST na Litinin, kamar yadda kafafen yaɗa labaran gwamnati suka ruwaito.

    Tun makon da ya gabata ne Iran ta rufe sararin samaniyarta ga dukkan jiragen kasuwanci saboda tashe-tashen hankula da ake fama da su.

    Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta kankane sararin samaniyar birnin Tehran na Iran, inda jiragen yaƙin Isra’ila ke amfani da shi wajen kai farmaki kan wasu muhimman wurare a cikin ƙasar.

  18. Wasu jagororin ƴanbindiga a Katsina sun ajiye makamansu

    Wasu fitattun jagororin ƴanbindiga da suka addabi yankunan ƙaramar hukumar Dan Musa ta jihar Katsina sun ajiye makamansu tare da sakin mutum 16 da suka yi garkuwa da su.

    Cikin wata sanarwa da rundunar sojin Najeriya ta wallafa a shafinta na X, ta ce matakin na cikin wani shiri na ci gaba da karɓar makamai da ficewa daga harkar aikata laifuka wanda rundunar Operation Fasan Yamma ke jagoranta tare da hadin gwiwar hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki.

    Jagororin ‘yan bindigar da suka miƙa wuya sun haɗa da Kamulu Buzaru da Manore da Nagwaggo da Lalbi da Alhaji Sani da Dogo Baidu da Dogo Nahalle da Abdulkadir Black.

    A cewar jami’an tsaron, fitattun ƴanbindigar sun miƙa makamansu ne a ranar 14 ga Yuni, 2025, tare da yin alƙawarin barin aikata laifi da zama lafiya da sauran al’ummomi.

    An karɓi makamansu kuma an adana su a karkashin kulawar hukumomi, kamar yadda jami'an tsaron suka tabbatar.

    Domin tabbatar da zaman lafiyar, tsoffin ‘yan bindigar sun saki mutum 16 da suka haɗa da mata bakwai da yara tara da suke tsare da su, tare da alƙawarta sakin wasu da dama.

    Hukumomin soja sun bayyana cewa bayan wannan mataki, lamarin tsaro a yankin Dan Musa ya daidaita, tare da ci gaba da sanya ido daga dakarun soji don hana sake faruwar rikice-rikice.

  19. Ambaliya ta hallaka mutane da dama a Kongo

    Aƙalla mutum 22 ne suka rasa rayukansu yayin da dubban gidaje suka ruguje a cikin ambaliyar ruwa sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a Kinshasa, babban birnin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, da Brazzaville a ranar 14 ga Yuni.

    A Kinshasa, hukumomi sun tabbatar da mutuwar mutum 19, inda mafi yawansu suka faru ne a ƙaramar hukumar Ngaliema.

    Birnin ya kuma samu mummunan lalacewar manyan gine-gine sakamakon ambaliyar.

    A gefe guda kuma, Brazzaville ta ba da rahoton mutuwar mutum uku sakamakon ruwan saman kamar da bakin ƙwarya.