Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump ya kamnala haɗa majalisar zartarwarsa bayan sanar da naɗin sakatariyar harkokin noma.
Brooke Rollins tana cikin masu biyayya ga Trump da suka yi aiki a fadar White House a wa’adin mulkinsa na farko.
Majalisar zartarwar ta ƙunshi mutane masu ra'ayin gangaminsa na sake farfaɗo da martabar Amurka, watau ''Make America Great Again''.
Akwai kuma 'yan tsiraru da za a iya cewa ba su cikin gangamin amma sun samu shiga, daga cikin su har da Marco Rubio da Trump ke son naɗawa sakataren harkokin waje.
Akwai kuma irin su Robert F Kennedy Jnr, wanda zai jagoranci ma'aikatar lafiya, duk da tarihinsa na yin togaciya ga shirin riga-kafi.
Dole ne majalisar dattawa ta amince da naɗin nasu kafin ya tabbata, kuma akwai hasashen cewa za a kai ruwa-rana kafin amincewa da wasu daga cikin maƙarraban na Trump.
Wani da naɗin nasa ya janyo ce-ce-ku-ce, Matt Gaetz - da aka so naɗawa muƙamn babban lauyan gwamnati - ya janye bayan fuskantar tangarɗa.
Wani kuma da ake ganin naɗin nasa a matsayin wata hanyar ɗauke hankali da janyo dambarwa shi ne hamshaƙin attajirin duniyar nan, Elon Musk, mamallakin shafin X.