Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 24/11/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 24/11/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza da Annur Muhammad Annur

  1. Rufewa

    Masu bibiyarmu a wannan shafin na BBC Hausa, da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye, yau Lahadi a nan za mu rufe shafin na.

    A madadin kowa da kowa, Muhammad Annur Muhammad ke fatan za ku kasance da mu gobe Litinin, 25 ga watan Nuwamba, 2024, idan Allah Ya yarda.

    Mu rufe da wannan karin maganar da ke cewa - Sanin asali ya sa kare cin alli

  2. Wasu mabiya Sunnah da Shi'a da ke rikici a Pakistan sun cimma yarjejeniya

    Gawarwaki

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙabilun al'ummar Musulmi mabiya aƙidar Sunnah da 'yan Shi'a sun cimma yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta a tsakaninsu bayan wani rikici da ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutum 60 a makon da ya gabata a yankin arewa maso gabashin Pakistan.

    Mai magana da yawun lardin da lamarin ya faru, Khyber Pakhtunkhwa, ya ce, a tsawon lokacin sasancin na kwana bakwai, ɓangarorin biyu sun yarda su yi musayar fursunoni da kuma gawarwakin waɗanda suka mutu.

    Haka kuma ana sa ran hukumomi za su shiga lamarin domin magance abin da ya haddasa rikici a tsakanin mabiyan.

    Daman yankin a tarihi ya yi ƙaurin suna da rkikicin ƙungiyoyin addini, to amma wannan rikicin yana da nasaba ne da maganar mallakar fili.

    A ranar Alhamis 'yanbindiga suka yi wa tawaga biyu daban-daban ta 'yan Shi'a kwanton-ɓauna, inda suka hallaka aƙalla mutum arba'in.

  3. Ƙiris ya rage da na zama mai jarabar shan taba - Obasajo

    Cif Olusegun Obasanjo

    Asalin hoton, PASCAL PAVANI

    Tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya ce ƙiris ya rage da ya zama mai jarabar shan taɓa da bai yi watsi da ita ba.

    Shugaban na magana ne a wajen wani gangami na yaƙi da ta'ammali da miyagun ƙwayoyi a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, wanda wata ƙungiya Recovery Advocacy Network ta shirya, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito yau Lahadi.

    Obasanjo ya ce ya tuna lokacin da ya yunƙurin fara shan taba yana matashi inda abin da kai shi ga kamuwa da tari mai tsanani, saboda haka ya yi watsi da tabar.

    Tsohon shugaban ya shawarci matasa da ɗalibai, da su guji amfani da miyagun ƙwayoyi da cewa ba abin da suke ƙarawa ga rayuwa sai dai ɓata ta.

    Obasanjo ya nuna damuwa kan ƙaruwar ta'adar amfani da miyagun ƙwayoyi a Najeriya da Afirka ta Yamma.

  4. Gwamnatin Senegal na shan suka kan kama jagoran hamayya da ya yi suɓul da baka

    Shugaba Bassirou Diomaye Faye

    Asalin hoton, OTHERS

    Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'Adam a Senegal sun yi suka game da tsare wani jagoran hamayya saboda ya ce la'ana ce ta faɗa wa al'ummar ƙasar saboda zaɓen Bassirou Diomaye Faye da suka yi a matsayin shugaban ƙasa.

    A ranar Juma'a aka kama Moustapha Diakhaté wanda ya furta kalaman a wani gidan talabijin mai zaman kansa.

    Ƙungiyar kare haƙƙin bil'Adama ta Amnesty international ta ce kama shi wata alama ce ƙarara ta neman danne 'yancin faɗin albarkacin baki..

    Amnesty ta ce ko da kalaman da ya yi laifi ne, hakan bai kai a sa shi a gidan yari ba.

    Ana zargin Shugaba Faye da Firaminista Sonko da koyi da ɗabi'ar tsohon shugaban ƙasar Macky Sall ta hanyar harin 'yan hamayya na siyasa da dokoki na ɓata suna.

  5. An kashe aƙalla mutum uku a rikicin 'yansanda da masu zanga-zanga kan masallaci a India

    Hoton yankin masallaci a ƙone

    Aƙalla mutum uku ne suka mutu a rikici da 'yansanda da masu zanga-zanga kan safiyon inda aka gina wani masallaci tun na ƙarni 16 da ake taƙaddama a kanshi a arewacin India.

    Wata kotu ce ta bayar da umarnin gudanar da bincike kan inda aka gina masallacin a jihar Uttar Pradesh tun a zamanin da, bayan da aka shigar da ƙorafi cewa an yi ginin ne a kan wani kufai na wajen ibadar 'yan Hindu, wanda masu mulki na tsohuwar Daular Mughal suka rushe ɗaruruwan shekaru a zamanin suna mulki a India.

    Shugabannin al'ummar Musulmi sun nuna ƙin amincewa da bincike.

    'Yansanda sun ce sun yi amfani da kulake da hayaƙi maisa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar, waɗanda ke jifa da duwatsu da kuma ƙona motoci.

    Ƙungiyoyin mabiya addinin Hindu masu ra'ayin riƙau na zargin cewa an rushe dubban wuraren bauta na 'yan Hindu aka gina masallatai a kansu a zamanin Daular Mughal a India, to amma wasu masana tarihi sun musanta alƙaluman.

  6. 'Yansanda a Thailand na binciken wajen bauta na Buddha da aka gano gomman gawarwaki

    Mabiya Buddha da 'yansanda

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yansanda a arewacin Thailand na binciken wani wajen bauta na addinin Buddha, inda aka gano gomman gawarwaki a jiya Asabar.

    Ba a san inda gawarwakin suka fito ba, amma wani jami'in 'yansanda ya ce, gawarwakin na haɗe da takardun shedar rasuwa da kuma tallafi.

    Ya ƙara da cewa an tuntuɓi iyalansu domin sanin ko an bayar da su ne tallafi da sanin iyalan.

    A ranar Laraba ma an samu wasu gawarwakin 12 a wani wajen bautar a wani lardi da ke maƙwabtaka.

    Babban limamin wurin bautar ya gaya wa kafafen yaɗa labaran yankin cewa suna amfani da gawarwaki wajen gwajin wani nau'in ibada da ya ƙirƙiro.

    Jami'ai na ƙoƙarin tabbatar da iƙirarin nasa da kuma sanin yawan yadda ake wannan bauta.

  7. 'Yansandan Pakistan na ɗauki-ba-daɗi da magoya bayan tsohon firaministan ƙasar

    Rikici da 'yansandan Pakistan

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni na nuna cewa ana ɗauki-ba-daɗi a wajen babban birnin Pakistan, Islamabad, yayin da cincirondon magoya bayan jam'iyyar tsohon firaministan ƙasar Iman Khan, PTI, ke shiga birnin.

    Masu zanga-zangar na kiran da a saki tsohon firaministan daga kurkuku.

    Jam'iyyar ta PTI ta ce 'yansanda sun harba hayaƙi mai sa hawaye tare da amfani da kulake domin tarwatsa magoya bayan nata.

    Su kuwa 'yansandan sun ce masu zanga-zangar na jifansu na duwatsu ne.

    Rahotanni sun ce an tsare ɗaruruwan 'yan jam'iyyar ta PTI .

    Daman jami'an tsaro sun rufe birnin kafin zanga-zangar, wadda babbar kotun birnin ta haramta.

  8. Iran za ta gana da ƙasashen Yamma kan shirin nukiliyarta

    Makamin nukuliyar Iran

    Asalin hoton, AFP

    Hukumomin Iran sun ce ƙasar za ta tattauna da ƙasashen Faransa da Jamus da Birtaniya kan batun nukiliyarta da sauran batutuwar da suka shafi yankin Gabas ta Tsakiya.

    Kakakin ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ne ya bayyana haka, inda ya ce za a yi tattaunawar a ranar Juma'a mai zuwa, sai dai bai bayyana inda za a yi ganawar ba.

    Tun da farko kamfanin dillancin labaran Japan, Kyodo ya bayyana cewa za a yi tattaunawar ne a birnin Geneva.

    A ranar Juma'a hukumar kula da nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da Iran kan kasa bai wa hukumar haɗin kai.

    Hukumar kula da munanan makamai na duniya ta ce Iran ta ƙara yawan amfani da makamashin uranium da take sarrafawa zuwa makamai.

  9. Dangote ya rage farashin man fetur a Najeriya

    Kamfanin Dangote

    Asalin hoton, NNPCL/X

    Kamfanin mai na Dangote ya bayyana yi wa 'yan kasuwa da ke saro man fetur a matatarsa ragin kuɗin man.

    Cikin wata sanarwa da babban jami'in sadarwar kamfanin, Anthony Chiejina ya fitar ranar Lahadi ta ce an rage wa 'yan kasuwar farashin da suke saro man daga naira 990 zuwa naira 970, domin ''nuna godiyarsa ga 'yan Najeriya''.

    ''A yayin da shekarar nan ke zuwa ƙarshe, wannan ita ce hanyar da za mu gode wa mutanen Najeriya kan irin goyon bayan da suka riƙa nuna mana har matatarmu ta tabbata. Wannan ƙari ne kan godiyar da muke yi wa gwamnati bisa goyon bayan da ta ba mu wajen ɗaukar matakan da suƙa ƙarfafa wa kamfanonin cikin gida gwiwa''.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Sanarwar ta ƙara da cewa matatar ba za ta yi wani abu da zai rage ingancin man da take tacewa ba, wanda ta ce ingantacce ne da ba ya gurɓata muhalli.

    Hakan na zuwa ne 'yan kwanaki da matatar ta fara fitar da man fetur zuwa ƙasashen waje somin sayarwa

  10. Rundunar sojin Isra'ila ta nemi afuwar sojojin Lebanon kan harin da ta kai musu bisa kure

    Sojojin Isra'ila

    Asalin hoton, IDF

    Rundunar sojin Isra'ila ta nemi afuwar sojojin Lebanon bayan da wani hari ta sama da Isra'ilar ta kai ya faɗa kan wani ƙaramin sansanin sojin Lebanon inda ya kashe soja guda tare da raunata wasu 18.

    Kakakin sojin Isra'ila ya ce tuni suka ƙaddamar da bincike kan lbatun.

    Lamarin ya faru ne a yankin da ake fafatawa tsakanin sojojin Isra'la da mayaƙan Hezbollah.

    Sojojin Isra'ilar sun ce an harba kusan makaman roka 160 zuwa ƙasar daga Lebanon a yau Lahadi, yayin da aka kakkaɓo wasu daga ciki, sai dai babu rahoton jikkata.

    Tun da farko Hezbollah ta ce ta ƙaddamar da hare-hare kan sansanin sojin ruwan Isra'ila a Ashdod da ke kudancin Isra'ila da wani sansanin sojin a Tel Aviv.

  11. Al'ummar Uruguay na zaɓen shugaban ƙasa zagaye na biyu

    Masu zaɓe

    Asalin hoton, Getty Images

    An fara kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasa zagaye na biyu a Uruguay. Ɗan takarar adawa mai matsakaicin ra'ayin kawo sauyi, Yamandú Orsi ne ya zo na ɗaya a zaɓen zagaye na farko da aka gudanar a watan da ya gabata, amma bai samu rinjayen da zai ba shi nasarar lashe zaɓen ba.

    A zagaye na biyun yana fafatawa da ɗan takarar jam'iyyar gwamnati, Álvaro Delgado.

    Ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna cewa 'yan takarar na kankankan, yayin dubban ƙuri'un da za a kaɗa za su raba gardama.

    Akwai manyan abubuwa da dama da suka mamaye yaƙin neman zaɓen, da suka haɗa da tsadar rayuwa da rashin daidaito da tsaron ƙasa.

  12. Jam'iyyar Imran Khan a Pakistan ta fara babban gangami a Islamabad

    Gangami

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Hoton wani gangami da jam'iyyar ta taɓa gudanarwa a 2022

    Jam'iyyar PTI ta tsohon firaministan Pakistan, Imran Khan ta fara shirya wani gangami a babban birnin ƙasar Islamabad.

    Tuni babbar kotun binrin ta ce gangamin haramtacce ne, inda ta uamrci gwamnatin ƙasar ta yi duk mai yiwuwa domin ɗaukar matakan tabbatar da doka da oda.

    Tuni aka tsarara tsaro a birnin, tare da toshe titunan shiga birnin. An dakatar da sadarwar waya da na intanet a wasu yankunan. Imran Khan ya buƙaci magoya bayansa su haɗa kansu.

    Ya yi tir da abin da ya kira da maguɗi a babban zaben watan Fabrairu, da kuma kamen ɗaruruwan 'yan PTI da ya kira da 'rashin adakci'.

  13. 'Yan ciranin Somaliya 30 sun mutu a kifewar jiragen ruwa a Madagascar

    jirgin ruwa

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'an Somaliya sun tabbatar da mutuwar 'yan cirani kusan 30 bayan da jiragen ruwa biyu da suke tafiya a ciki suka nutse a kife Madagascar.

    Jakadan Somaliya a Ethiopia ya ce mutum 70 ne a cikin jragen, waɗanda dukkansu 'yan ƙasar Somaliya ne.

    Daga baya an gano jiragen biyu na shawagi a saman ruwa a gaɓar tekun arewacin Madagascar.

    Waɗanda suka tsira daga hatsarin sun ce suna ƙoƙarin kai wa tsibirin Mayotte na Faransa ne, wata fitacciyar hanya mai cike da hatsari ga 'yan ciranin Somaliya masu neman mafaka.

  14. Sojojin Sudan sun ƙwace birnin Sinja daga hannun RSF

    Al Burhan

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Shugaban mulkin sojin Sudan Janar Al- Burhan

    Rundunar sojin Sudan ta ce ta ƙwace babban birnin jihar Sennar daga hannun dakarun RSF.

    A watan Yulin da ya gabata ne dakarun na RSF suka ƙwace iko da Sinja, babban birnin jihar Sennar, lamarin da ya tilasta wa dubban mazauna birnin ficewa daga cikinsa.

    Wasu bidiyoyi da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda mazauna Sinja ke ta murna a kan titunan ƙasar bayan da sojojin ƙasar suka dawo cikin birnin.

    Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil-adama sun ce a lokacin da birnin ke hannun mayaƙan RSF sun riƙa fuskantar nau'ikan cin zarafi.

    A yayin da sojoji ke murnar ƙwace birnin da ke kudu maso gabashin birnin Khartoum, an samu rahotonnin da ke nuna cewa mayaƙan RSF sun kai hare-hare a wasu garuruwa a jihar Blue Nile mai maƙwabtaka.

    Har yanzu mayaƙan RSF na riƙe da wasu yankunan babban birnin jihar Al Jazeera da na jihar Darfur.

  15. Akwai yiwuwar a kama Netanyahu idan ya shiga Birtaniya

    Netanyahu

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, A ranar Alhamis ne Kotun ICC ta bayar da sammacin kama Netanyahu

    Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ka iya fuskantar kamu idan ya shiga Birtaniya, bayan hukuncin Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta ICC na bayar da sammacin kama shi, kamar yadda fadar gwamnatin Birtaniyar ta nuna.

    Mai magana da yawun firaministan Birtaniya, ya ƙi yin magana game da shari'ar, amma ya ce gwamnati za ta sauke ''nauyin da shari'a'' ta ɗora mata.

    A ranar Alhamis ne Kotun ICC ta bayar da sammacin kama Netanyahu tare da tsohon ministan tsaron ƙasar, Yoav Gallant, kan zargin aikata laifukan yaƙi a Gaza.

    Duka ƙasashe mambobin kotun, ciki har da Birtaniya, sun sanya hannun kan yarjejeniyar da ta ɗora musu alhakin aiwatar da sammacin kamu da kotun ta bayar kan ko wane ne.

    Da aka tambaye shi ko za a tsare Netanyahu idan ya shiga Birtaniya, kakakin firaministan na Birtaniya bai ce komai ba kan batun.

    To amma ya ce ''gwamnati za ta sauke nauyin shari'a da ke kanta ƙarƙashin dokokin da shari'a ta gindaya''.

  16. Saudiyya ta kama mutum 19,696 da ke zaune a ƙasar ba bisa ƙa'ida ba

    Mazauna

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar cikin gidan Saudiyya ta ce jami'anta sun kama mutum 19,696 da ke zaune a ƙasar ba bisa ƙa'ida ba.

    Jaridar Saudi Gazzet ta ce an kama mutanen ne cikin mako guda bayan da jami'an ma'aikatar cikin gidan ƙasar tare da haɗin gwiwwar wasu hukumomin tsaro suka ƙaddamar da farautar 'yan ƙasashen waje da ke zaune a ƙasar ba bisa ƙa'ida ba.

    Mutanen da aka kama sun ƙunshi waɗanda suka shiga Saudiyya ba tare da biza ba, ko bizarsu ta ƙare da waɗanda suka saɓa dokokin kan iya wajen shiga ƙasa, da waɗanda suka saɓa wa dokokin bizar aiki.

    Ma'aikatar ta kuma ce jami'anta sun kama wasu mutum 1,547 da ke ƙoƙarin shiga ƙasar ta kan iyakokinta ba bisa ƙa'ida ba, waɗanda ta ce kashi 65 cikin 100 'yan ƙasar Ethiopia ne sai kuma kashi 32 cikin 100 'yan ƙasar Yemen.

  17. Tinubu ya koma Najeriya bayan taron G20

    Shugaba Tinubu

    Asalin hoton, Fadar shugaban Najeriya

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya koma ƙasar bayan halartar taron ƙungiyar G20, ta manyan ƙasashe mafiya ƙarfin tattalin arziki.

    Taron - wanda aka gudanar a ƙasar Brazil - ya tattauna batutuwa da dama na ci gaban ƙasashen duniya.

    A ranar Asabar da daddare ne shugaba Tinubu da mai ɗakinsa, Sanata Remi Tinubu- wadda ta raka shi taron - sauka sauka a filin jirgin sama na Abuja.

    Shugaban ya samu tarba daga manyan jiga-jigan gwamnatinsa da 'yan siyasa, ciki har da Ministan Abuja, Nyesom Wike da shugaban ma'aikatan fadarsa, Femi Gbajabiamila da shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribado da sauran muƙarraban gwamnati

  18. An tsinci gawar jagoran addinin Yahudawa a UAE - Isra'ila

    ..

    Asalin hoton, Chabad

    Gwamnatin Isra'ila ta ce an tsinci gawar jagoran addinin Yahudawan ƙasar da ya ɓace a ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa

    A ranar alhamis ne ofishin firaministan Isra'ila ya sanar da ɓacewar Zvi Kogan, jakadan ƙungiyar Chabad ta addinin Yahudawa mabiya ɗariƙar Orthodox, lamarin da ya haifar da zuzzurfan bincike daga hukumar leƙen asirin Isra'ila, Mossad da hukumomin UAE.

    “Kisan Zvi Kogan babban laifi ne na ta'adincin ƙyamar Yahudawa. Don haka ƙasar Isra'ila za ta ɗauki mataki da iya ƙarfin da take da shi, domin gurfanar da mutanen da suka kashe shi'', kamar yadda ofishin firaministan Isra'ila ya bayyana cikin sanarwar kisan.

    Sanarwar ta ci gaba da cewa jami'an Isra'ila sun riƙa magana da iyalan Mista Kogan, ɗan Isra'ila asalin Moldovan, tun bayan sanar da ɓacewarsa.

    Kamfanin dillancin labaran Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ya ce ma'aikatar cikin gidan ƙasar na nema tare da bincike game da ɓatan jagoran addinin Yahudawan

    Ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa Abu na da ƙawance mai ƙarfi da ƙasar Isra'ila, ƙarƙashin wata yarjejeniya da Amurka da shiga tsakaninsu, da aka fi sani da 'yarjejeniyar Abraham'.

    Yarjejeniyar da ƙasashen biyu suka martaba a lokacin yaƙin Isra'ila da Hamas a Gaza.

  19. Trump ya kammala haɗa majalisar zartaswarsa da naɗin sakatariyar noma

    Brooke Rollins sabuwar sakatariyar noma ta Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Brooke Rollins ta taɓa yin aiki a fadar White House a wa’adin mulkin Trump na farko

    Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump ya kamnala haɗa majalisar zartarwarsa bayan sanar da naɗin sakatariyar harkokin noma.

    Brooke Rollins tana cikin masu biyayya ga Trump da suka yi aiki a fadar White House a wa’adin mulkinsa na farko.

    Majalisar zartarwar ta ƙunshi mutane masu ra'ayin gangaminsa na sake farfaɗo da martabar Amurka, watau ''Make America Great Again''.

    Akwai kuma 'yan tsiraru da za a iya cewa ba su cikin gangamin amma sun samu shiga, daga cikin su har da Marco Rubio da Trump ke son naɗawa sakataren harkokin waje.

    Akwai kuma irin su Robert F Kennedy Jnr, wanda zai jagoranci ma'aikatar lafiya, duk da tarihinsa na yin togaciya ga shirin riga-kafi.

    Dole ne majalisar dattawa ta amince da naɗin nasu kafin ya tabbata, kuma akwai hasashen cewa za a kai ruwa-rana kafin amincewa da wasu daga cikin maƙarraban na Trump.

    Wani da naɗin nasa ya janyo ce-ce-ku-ce, Matt Gaetz - da aka so naɗawa muƙamn babban lauyan gwamnati - ya janye bayan fuskantar tangarɗa.

    Wani kuma da ake ganin naɗin nasa a matsayin wata hanyar ɗauke hankali da janyo dambarwa shi ne hamshaƙin attajirin duniyar nan, Elon Musk, mamallakin shafin X.

  20. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa barkanmu da hutun ƙarshen mako.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kun wayi gari lafiya, tare da fatan kasancewa a daidai wannan lokaci.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin bayar tofa albarkacin bakinku kan labaran da muke wallafawa.