Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 04/07/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Ahmad Bawage

  1. Wike ya gargaɗi masu haɗaka su daina amfani da ƴan Najeriya don cimma manufofinsu

    Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike ya gargaɗi masu shiga sabuwar haɗaka da aka kafa, da su daina amfani da ƴan Najeriya don cimma manufofinsu.

    Wike ya bayyana haka ne ranar Alhamis lokacin da yake tattaunawa da ƴan jarida a gidansa da ke Abuja.

    A cewarsa, sabuwar haɗaka da wasu fitattun ƴan siyasa suka shiga ta hanyar amfani da jam'iyyar ADC, sun yi ta ba don buƙatun ƴan Najeriya ba, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

    "Saboda kana fushi da wani, sai ka ce ƴan Najeriya sun fusata sannan ka ja-gaba wajen shiga haɗaka. Ya kamata mu ɗauki batutuwan Najeriya da muhimmanci.

    "Ina kalubalantar dukkan waɗanda suka shiga haɗakar da su nuna irin ci gaba da suka kawo lokacin da suke kan mulki. Me suka yi wa ƙasar," in ji Wike.

  2. Rasha ta zama ƙasa ta farko da ta amince da gwamnatin Taliban a Afghanistan

    Rasha ta amince da gwamnatin Taliban a Afghanistan a hukumance.

    Ana tunanin ita ce ƙasa ta farko da ta yi hakan.

    Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta ce amincewa da gwamnatin Taliban ɗin zai taimaka wajen inganta haɗin kan ƙasashen biyu a ɓangarori da dama.

    Ministan harkokin wajen Taliban ya yaba wa Moscow inda ya ce matakinta na jarumtaka zai zama abin koyi ga wasu.

    A shekarar 2021 ne Taliban ta koma kan karagar mulki bayan da ta ƙwace iko da birnin Kabul.

  3. Me ya sa wasu manyan muƙarraban Buhari suka shiga haɗakar ADC?, Abdullahi Bello, BBC News Abuja

    Zargin da wasu ke yi cewa muƙarraban tsohuwar gwamnatin Buhari ba sa jin daɗin gwamnatin Tinubu na ƙara fitowa fili, bayan da aka ga fuskokin wasu jiga-jigan tsohuwar gwamnatin kane-kane cikin sabuwar haɗakar ADC.

    A ranar Laraba ne wasu jiga-jigan yan siyasar ƙasar daga jam'iyyun hamayya da ma wasu a APC suka sanar da yin haɗaka ƙarƙashin inuwar jam'iyyar ADC da nufin kawar da gwamnatin APC ta Bola Tinubu.

    A watannin da suka gabata ne dai wasu daga cikin tsagin tsohuwar jam'iyyar CPC da Buhari ya jagoranta a baya - da ta narke cikin haɗakar APC a 2014 - suka nuna damuwarsu kan rashin damawa da su a gwamnatin Tinubu.

  4. 'Na ga yadda aka buɗe wa Falasɗinawa wuta a Gaza'

    Wani tsohon jami'in tsaro a cibiyoyin rarraba kayayyakin jin-ƙai a Gaza ya shaida wa BBC cewa ya ga yadda abokan aikinsa suka buɗe wa Falasɗinawan da ba su haifar da wata barazana ba wuta.

    Mai kwarmata bayanan wanda ya yi magana da kuma ya buƙaci a sakaya sunansa ya bayyana al'adar rashin hukunta mai laifi inda jagororin shirin ke kwatanta al'ummar Gaza a matsayin aljanu tare da faɗa wa jami'an tsaron da ke aikin kwangila su buɗe wuta a duk lokacin da suka fuskanci wata barazana.

    Wakiliyar BBC ta ce gidauniyar agajin ta ƙaryata zarge-zargen, inda ta ce babu wani lokaci guda da aka buɗe wa farar hula wuta a cibiyoyinta na rarraba kayayyakin jin ƙai.

  5. Assalamu Alaikum

    Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Juma'a - Hajj Babbar Rana.

    Ku kasance da mu a wannan shafi domin kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.