Wata hadakar malamai a Arewacin Najeriya ta amince Tinubu ya zarce
Wata hadakar malaman Musulunci daga jihohi 19 na Arewacin Najeriya ta bayyana goyon bayanta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tare da amincewa da ya sake tsayawa takara a zaben 2027.
Hadakar ta bayyana matsayarta ne yayin taronta na Muslim Intellectuals Forum, wanda aka gudanar a dakin taro na Sir Ahmadu Bello, Sabuwar Sakatariya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Hadimin Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, Isah Muhammad Yusuf, ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
A cewarsa, taron ya hada malaman Musulunci da masana daga jihohin Arewacin Najeriya 19, inda suka bayyana amincewarsu da jagorancin Shugaba Tinubu da kokarinsa na magance matsalolin da ke addabar yankin, musamman matsalar rashin tsaro.
Kungiyar ta kuma kada kuri'ar amincewa da Shugaba Tinubu, tare da kira ga 'yan Najeriya, musamman al'ummar Arewa, da su mara wa shugaban baya da jam'iyyar APC a zaben 2027.
Goyon bayan na zuwa ne a daidai lokacin da jam'iyyu da kungiyoyin siyasa ke kara shirye-shiryen tunkarar babban zaben 2027.
A nata bangaren, kungiyar ta ce ta yi imanin cewa jagorancin Tinubu da matakan da gwamnatinsa ke dauka za su taimaka wajen magance kalubalen da Arewacin Najeriya ke fuskanta.